01
Nov
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba haka kawai gabagaɗi ake fitowa a ayyana cewa 'yan bindiga su ma 'yan ta’adda ne ba. Ministan Harkokin Tsaro, Bashir Magashi ne ya bayyana haka, tare da cewa, akwai matakan da ake bi, kuma ko an bi su ɗin, to sai an tabbatar da kammaluwarsu sannan za a ayyana cewa 'yan bindiga ma 'yan ta’adda ne. Magashi ya yi wannan maganar ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido don ganin irin ci gaban da ake samu a filin dagar yaƙi da Boko Haram a Maiduguri da ke…
