02
Nov
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ƙungiyar Mata Malaman Kwalejin Ilimi na gwamnatin Tarayya ta ‘National Association of Women in Colleges of Education’ (WICE) ta karrama Hajiya Dakta Amina Haruna Abdul, ƙwararriyar Malama a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya FCE da lambar yabo. Dakta Amina ita ce Wakiliyar Tula, ta farko ƙungiyar WICE ta karrama ta bisa da lambar Yabo bisa ayyukan jinƙai da taimakon al’umma da ta ke yi ako yaushe wajen ganin ta inganta ilimin 'ya'ya mata. An karrama ta a wani taron da ƙungiyar ta na ƙasa da suka gudanar a Kwalejin Ilimi na gwamnatin Tarayya ta…
