03
Nov
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Aƙalla mutane 10 ne aka ruwaito sun mutu a ranar Litinin bayan da wani gini mai hawa 21 ya ruguje a hanyar Gerard a unguwar Ikoyi da ke Jihar Legas. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mutane da dama sun maƙale a cikin baraguzan ginin, ciki har da Manajan Darakta na Fourscore Heights Limited, Femi Osibona, wanda shi ne mai maginin, da wasu abokan aikinsa da injiniyoyi. Ɗaya daga cikin ma’aikatan da suka tsallake rijiya da baya, Gabriel Bassey, ya shaida wa manema labarai cewa, har yanzu kimanin mutane 50 ne ke maƙale a cikin ɓaraguzan…
