Editor

9513 Posts
Kadaɗe ya daɗe a taron PDP

Kadaɗe ya daɗe a taron PDP

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ba wani baƙon labari ba ne kasancewar a makon jiya yadda sunan wani matashi, Muhammad Suleiman Kadaɗe, ya shiga kafafen yaɗa labarai, saboda yadda linzamin sunansa na addu'ar daɗewa ya bayyana da zaɓarsa a matsayin sabon shugaban matasan babbar jam'iyyar adawa ta PDP. Tun kafin zaɓen na ga hotunan matashin mai shekaru 25 da manyan 'yan jam'iyyar ciki kuwa har da wanda ya ma ta takarar shugaban ƙasa a 2019 wato Atiku Abubakar. Duk da dai taro ne na zaɓen shugabanni na ƙasa na PDP da ta mulki Nijeriya daga 1999-2015, amma maganar matashin nan ta…
Read More
Ranar hana cin zarafin ’yan Jarida ta duniya

Ranar hana cin zarafin ’yan Jarida ta duniya

Al'ummar duniya baki ɗaya na bikin wannan rana a matsayin ranar kawo ƙarshen cin zarafin ’yan jarida da ma'aikatan yaɗa labarai na duk duniya. Majalisar Ɗinkin Duniya a shekara ta 2013 ne ta zartar da wani ƙuduri a zamanta na 68 tare da ayyana ranar 2 ga watan Nuwamba na kowace shekara a matsayin ranar bikin, inda ta buƙaci ƙasashe mambobin ƙungiyar da su aiwatar da kwararan matakai na daƙile aukuwar lamarin na cin zarafinsu. An zaɓi ranar ne domin tunawa da kisan gillar da aka yi wa wasu ’yan jaridar Faransa biyu, Ghislaine Dupont da Claude Verlon a Mali…
Read More
Da Ɗumi-ɗuminsa: An ceto ma’aikatan Jami’ar Abuja

Da Ɗumi-ɗuminsa: An ceto ma’aikatan Jami’ar Abuja

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja, ta tabbatar da cewa rundunar tsaron haɗin gwiwa sun ceto dukkan ma'aikatan Jami'ar Abuja da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Litinin da ta gabata. Mai magana da yawun 'yan sandan yankin, Josephine Adeh, ita ce ta bada wannan tabbaci cikin sanarwar da ta fitar a yau Juma'a. Haka nan, Adeh ta ce tuni an sadar da waɗanda lamarin ya shafa da iyalansu.
Read More
Daga Oxford Zuwa Maiduguri: Labarin Farfesa William Richards

Daga Oxford Zuwa Maiduguri: Labarin Farfesa William Richards

Daga PORTIA ROELOFS Marubuciyar wannan ƙasida wata Baturiya ce mai suna Portia Roelofs, wacce ɗaliba ce a Kwalejin St. Annes College da ke Jamiar Oxford, mai gudanar da bincike kan harkokin siyasa da mulki a Afrika. Ta rubuta ƙasidar ne kan wani shehin malamin jamia a Jamiar Maiduguri, Farfesa William Richards, wanda ya rasu shekaru biyu zuwa uku da suka gabata. Ga yadda ƙasidar ta kasance: Danshin ɗumin iskar bazara na shekara ta 2019 ya daki fuskata. A tsaye na ke ƙiƙam a ɗakin saman benen gidanmu. A lokacin, ba abunda ƙwayoyin idanuwana suke yi illa ba wa cikinsu abinci…
Read More
‘Yan bindiga sun sace tsohon babban Manajan NPA a Kano

‘Yan bindiga sun sace tsohon babban Manajan NPA a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Wasu gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun sace tsohon Janar manajan hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA Bashir M. Abdullahi. Rahotanni sun ce, ɓata garin sun sace shi ne a wata gonarsa da ke garin Sitti da ke yankin ƙaramar hukumar Sumaila da yammacin ranar Laraba da ta gabata, To sai dai kuma rahotanni sun ruwaito cewa, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ba ta samu rahoton sace shi ba, Wasu mazauna garin da lamarin ya faru ne dai suka shaida wa manema labarai faruwar…
Read More
Ɗan Senegal ne ya lashe kyautar adabin Faransanci

Ɗan Senegal ne ya lashe kyautar adabin Faransanci

Daga AISHA ASAS Mohamed Mbougar Sarr matashi daga Ƙasar Senegal ne ya yi nasarar lashe gasar rubuce-rubuce na adabin harshen Faransanci mafi girma wanda ake kira da 'Concourt'. Matashin ya yi nasarar cin wannan gasar ne ta sanadiyyar littafinsa mai suna 'La plus secrète mémoire des hommes'. Kwamitin alƙalanci na gasar sun jinjina wa namijin ƙoƙarin da Muhammad ya yi a littafin, tare da nuna muhimmancin rubutu irin na littafin ga adabin na Faransanci. Ɗaya daga alƙalan ya yi bita dangane da abubuwan da ke kunshe a wannan littafin na 'La plus secrète mémoire des hommes', don ƙara tabbatar da…
Read More
Matsalar warin baki da hanyoyin magance ta

Matsalar warin baki da hanyoyin magance ta

Daga BILKISU YUSUF ALI Babbar matsalar da takan haifar da rashin jituwa da tsana da damuwa ga ma’aurata wadda wannan matsalar wata babbar damuwa ce in ta ta’azzara tana iya raba aure ko kai tsaye ko a kaikaice an sani ko ba a sani ba. Wannan za mu tattauna a yau wadda matsala ce da take ci wa ma’aurata tuwo a kwarya wannan matsala kuwa ita ce matsalar warin baki. Baki a zamantakewar aure yana da muhimmanci kwarai da gaske don yana cikin ‘yan aike da ke fara isa don nuna ƙauna da tayar da sha’awa da ɗaukar hankali. Duk…
Read More
Yadda bajekolin littafai da al’adun Hausa na duniya ya gudana a Kaduna

Yadda bajekolin littafai da al’adun Hausa na duniya ya gudana a Kaduna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kaduna A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne aka gudanar da babban taro mai suna 'Hausa Internation Book and Arts Festival' wato bikin bajekolin Littafai da al'adun Hausa na duniya. Bikin bajekolin littafai da al'adun Hausawa na duniya da ya gudana a Arewa Hausa da ke birnin Kaduna, taken taron dai shi ne Sarari wato (spaces). Taron wanda aka yi kwana uku ana gabatar da shi, an kuma fara ne a Ranar Alhamis inda aka fara da Hausa da Hausawa a doron ƙasa wanda Farfesa Abdullah Uba Adamu da Farfesa Ibrahim Malumfashi suka gabatar, wanda suka…
Read More
INEC ta shirya wa zaɓen gwamnan Anambra na ranar Asabar – Yakubu

INEC ta shirya wa zaɓen gwamnan Anambra na ranar Asabar – Yakubu

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Anambra cikin lumana wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa, 6 ga Nuwamba. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Talata a ofishin hukumar da ke garin Awka, babban birnin jihar. Ya ce: “Lokacin da hukumar ta saki jadawalin ranakun da za a gudanar da zaɓen, watanni bakwai da su ka gabata, tunanin da wasu su ka yi shi ne lokacin ba zai zo ba.…
Read More
Ni ce mace ta farko da aka fara ba wa shugabar jam’iya a Katsina – Mariya Abdullahi

Ni ce mace ta farko da aka fara ba wa shugabar jam’iya a Katsina – Mariya Abdullahi

“Na yi tafiye-tafiya da Obasanjo don neman a yafe wa Nijeriya bashin da ake bin ta” Daga UMAR GARBA, a Katsina Hajiya Mariya Abdullahi gogaggiyar ma'aikaciyar gwamnati ce wadda ta yi aiki a ma'aikatu daban-daban kama daga Jihar Katsina, sauran jihohin ƙasar nan da ma ƙasashen ƙetare, ta kuma kasance shahararriyar 'yar siyasa da ta yi takara kuma ta samu nasarar zama shugabar ƙaramar hukuma, mai bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar'adua shawara ta musamman, kwamishiniyar yaɗa Labarai, ta kuma taɓa kasancewa mamba a majalisar wakilan Tarayyar Nijeriya. Manhaja ta tattauna da Hajiya Mariya Abdullahi akan batutuwan da…
Read More