18
Sep
Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyyeti Allah Cattle Breeder (MACBAN), na reshen ƙaramar hukumar Lere a Jihar Kaduna, Abubakar Abdullahi Dambardi, saboda gazawa da ya yi wajen biyan fansar milyan N20 da aka buƙata ya biya kafin a sake shi. Sanarwar manema labarai da ta sami sa hannun shugaban ƙungiyar na jihar Kaduna, Haruna Usman Tugga, ta nuna ɓarayin sun halaka Dambardi ne da sanyin safiyar Juma'a a Lere. Tugga ya bayyana cewa, masu garkuwar sun buƙaci a biya su kuɗi har Naira miliyan 20 amma N250,000 ne marigayin ya iya samarwa ta hanyar rance,…
