Editor

9513 Posts
Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya don kinkimo bashin biliyan $4 da miliyan €710

Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya don kinkimo bashin biliyan $4 da miliyan €710

Duk da ƙorafe-ƙorafen da 'yan ƙasa ke yi game da yawan bashin da gwamnati ma ci ta ciyo, Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa da ta amince masa kan sake kinkimo bashin Dala biliyan 4 da Euro miliyan 710 daga ƙetare Buƙatar Buhari na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattatawa, wanda shugaban majalisar ya karanta ta a zauren majalisar a ranar Talata. A cewar Buhari, za a biya bashin da ake shirin karɓowa ne ta hanyar samo wasu basussukan daga Bankin Duniya da Cibiyar French Development da Bankin EXIM da kuma IFAD. Ya…
Read More
Bankin CBN: Jagorancin Emiefele ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasa – Kakakin Majalisar Matasan Arewa

Bankin CBN: Jagorancin Emiefele ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasa – Kakakin Majalisar Matasan Arewa

An bayyana cewa muddin ba a yi abin da ya kamata ba a kan lokaci, Nijeriya za ta faɗa cikin wani mawuyacin hali ta dalilin shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emiefele. Kakakin Majalisar Matasan Nijeriya, Mohammed Salihu Danlami shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin. Ɗanlami ya ce, Godwin Emiefele shi ne mafi munin abin da ya taɓa faruwa ga Nijeriya da tattalin arzikin ta, duba da yadda sha'anin tattalin arzikin Nijeriya ke fuskantar koma-baya, musamman yadda darajar kuɗin ƙasar ke ta ja baya. Ya ce Emiefele mutum ne mai…
Read More
Ya kamata malamai su riƙa yi wa bakinsu linzami

Ya kamata malamai su riƙa yi wa bakinsu linzami

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ba da jimawa ba ne, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Muhammad Abubakar na lll ya yi wani kira ga malaman addini da masu wa'azi su yi hattara da irin wa'azozin da suke yi a kan minbarori a masallatai da coci coci, sakamakon yadda wasu malaman ke amfani da matsayin su na masu faɗa a ji suna tunzura jama'a da yaɗa kalamai na ɓatanci da ƙiyayya a tsakanin ‘yan Nijeriya. Ba wannan ne karon farko da Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi irin wannan kiran ba ga malaman addini da sauran ‘yan Nijeriya dangane da yadda ake…
Read More
Hukumar Alhazai ta Abuja ta maida miliyan N432 ga maniyyata 334

Hukumar Alhazai ta Abuja ta maida miliyan N432 ga maniyyata 334

Hukumar Alhazai ta Birnin Tarayya, Abuja ta bayyana cewa, ta biya miliyan N432 ga maniyyata 334 a matsayin maida musu kuɗaɗen da suka biya don zuwa Hajjin 2021 wanda bai yiwu ba saboda matsalar annobar korona. Shugaban hukumar, Muhammadu Nasiru Ɗanmallam ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja yayin taron manema labarai da hukumar ta shirya ran Litinin. Ɗanmallam ya ce, Nijeriya ba ta samu yin Hajji ba na shekaru biyu a jere, wato 2020 da 2021, sakamakon rufe hanya da ƙasar Saudiyya ta yi ga maniyyatan ƙetare don kauce wa barazanar annobar korona. Ya ce a nasu…
Read More
Harin ‘yan bindiga: Fursunoni 240 sun tsere daga gidan yarin Kogi

Harin ‘yan bindiga: Fursunoni 240 sun tsere daga gidan yarin Kogi

Bayanai daga Jihar Kogi na nuni da cewa, aƙalla fursunoni 240 ne suka tsere sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai a matsakaicin gidan yarin da ke Kabba a jihar. Mai magana da yawun hukumar kula da gidajen yari na ƙasa, Mr Francis Enobore, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ran Litinin, inda ya ce an kai harin ne da tsakar daren Lahadin da ta gabata. A cewar jami'in, 'yan bindigar waɗanda ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari gidan yarin ne ɗauke da manyan makamai wanda ya…
Read More
Illar rashin ɗaukar nauyin ’ya’ya

Illar rashin ɗaukar nauyin ’ya’ya

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Yau ma ga mu a filinku mai albarka na Tarbiyya a shafin jaridarku ta Manhaja, inda kamar yadda mu ka saba, za mu ɗora daga inda muka tsaya. Da fatan ku na biye da mu kamar kullum. Mun ɗan samu ƙorafin mata a kan maza masu fita ba tare da sun wadata gidansu da abubuwan buƙata na rayuwa ba. Amma su suna fita su biya wa kansu buƙatarsu ba tare da sun tuna iyalinsu na buƙatar kulawarsu ba. A ce maza ba za su ba da kuɗin cefane yadda ya kamata ba, sai su fita su…
Read More
Jiki da jini…

Jiki da jini…

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, kuma ku san yadda jikinku ke aiki. Malam bahaushe na cewa jiki da jini sai da Hutu. To amma jikin ɗan Adam kusan koyaushe colin aiki yake. Duk ranar da ya tsaya cak, to tabbas rayuwa ta ƙare. Sai dai kuma hakan ba ya nufin jikin ɗan Adam ba ya buƙatar hutu. Zanfi mayar da hankali wajen bayyana ayyukan…
Read More
An kuɓutar da ɗaliban Zamfara daga hannun ‘yan fashin daji

An kuɓutar da ɗaliban Zamfara daga hannun ‘yan fashin daji

Kimanin ɗalibai 70 na Makarantar Sakandare da ke Ƙaya cikin yankin Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara aka ceto daga hannun 'yan bindiga a ranar Lahadi. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 1 ga Satumba rundunar 'yan sandan Zamfara ta tabbatar da an yi garkuwa da ɗalibai 73 a jihar. Sai dai, a ranar da aka kwashi ɗaliban ba da jimawa ba biyar daga cikinsu suka kuɓuta. Lamarin da ya sanya gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya ɗauki matakin rufe dukkan makarantun firamaren da sakandaren jihar. Tare kuma da kafa dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 6 na yamma zuwa…
Read More
Amfanin kanumfari ga lafiyar iyali

Amfanin kanumfari ga lafiyar iyali

Daga BIKISU YUSUF ALI Tambaya: Salam ina da tambaya kan muhimmancin kanumfari ga lafiya, musamman lafiyar ma’aurata. Amsa: Kanumfari abu ne mai muhimmancin gaske ga lafiyar al’umma. Asalin sunansa Bahaushe ya aro shi ne daga harshen Larabci 'ƙaranful' amma da Turanci ana kiransa da Cloves. Kanumfari yana cikin tsiro da ake amfani da shi a duk duniya ko dai don kayan ƙamshi a abinci ko kuma sinadari ko ma magani. Kanumfari yana ɗauke da sinadarai masu inganci da ƙara lafiyar jiki. Yana da matuƙar amfani a jiki amma in an sha shi dai-dai gwargwado saboda in ya yi yawa yana…
Read More