Editor

9513 Posts
HOTUNA: An yi fidda’un kwanaki uku da rasuwar Sarkin Kontagora, Alhaji Sa’idu Namaska

HOTUNA: An yi fidda’un kwanaki uku da rasuwar Sarkin Kontagora, Alhaji Sa’idu Namaska

A wannan Lahadin aka gudanar da addu'ar fidda'u na kwanaki uku da rasuwar marigayi Sarkin Kontagora, Alhaji Sa'idu Namaska a fadar masarautar. Taron ya samu halarcin jama'a da dama, na kusa da nesa, ciki har da Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, tsohon gwamnan jihar, Dr Mu'azu Babangida Aliyu, Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar da manyan 'yan siyasa da jami'an gwamanti a matakin ƙasa da jihohi. Yayin taron, Gwamna Sani Bello ya yi kira ga al'ummar Masarautar Kontagora da su ci gaba da yi wa marigayin da iyalansa da ma masarautar baki ɗaya addu'a, Kazalika, Bello ya buƙaci al'ummar masrautar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta raba tallafin kayayyaki ga waɗanda ambaliya ta shafa a Keffi

Gwamnatin Tarayya ta raba tallafin kayayyaki ga waɗanda ambaliya ta shafa a Keffi

Gwamnatin Tarayya ta raba tallafin kayayyakin abinci ga ahali 450 waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Keffi, Jihar Nasarawa. Gwamnati ta yi rabon kayan ne ta hannun Ma'aikatar Jinƙai, Agaji da Bunƙasa Zamantakewa ƙarƙashin jagorancin Minista Sadiya Umar Farouq wadda kuma Kwamishinar Tarayya, Imam Sulaiman Ibrahim ta wakilta. Yayin rabon tallafin Kayan tallafin da aka raba wa waɗanda lamarin ya shafa a ranar Lahadi, sun haɗa da buhuhunan shinkafa, katan-katan na tumatiri, man girki haɗa da tufafi da sauransu. Waɗanda aka gani a wajen rabon tallafin wanda ya gudana a yankin GRA, har da nakasassu da marasa galihu.…
Read More
Hukumar Alhazai ta Jigawa ta maida wa maniyyata 609 da kuɗaɗensu

Hukumar Alhazai ta Jigawa ta maida wa maniyyata 609 da kuɗaɗensu

Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta maida wa maniyyata 609 waɗanda suka biya kuɗaɗe don Hajjin 2020/2921 da kuɗaɗensu har Naira miliyan 752. Sakataren hukumar, Alhaji Muhammad Sani Alhassan, shi ne ya bayyana haka a Asabar da ta gabata yayin zantawarsu da manema labarai a garin Dutse, babban birnin jihar. Alhassan ya ce, Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ita ce ta ba da umarnin da a gaggauta maida wa maniyyatan da kuɗaɗensu bayan da ƙasar Saudiyya ta bayar da sanarwar hana maniyyatan wasu ƙasashen duniya zuwa aikin Hajji a matsayin wani mataki na yaƙi da yaɗuwar cutar korona. Alhassan ya…
Read More
Dangin ‘yan siyasa na wawashe asusun Nijeriya – Hukumar FIRS

Dangin ‘yan siyasa na wawashe asusun Nijeriya – Hukumar FIRS

Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS) ta bayyana cewa, dangin 'yan siyasar ƙasar nan ke wawushe kuɗaɗen harajin da ake tara wa ƙasa. Bayanin haka ya fito fili ne a lokacin da wasu ma'aikatan hukumar suka bayyana tsoron makomarsu idan ya zamana cewa ikon karɓar haraji ya fita daga hannun hukumar ya koma hannun jihohin ƙasar nan. Da alama dai 'yar tsamar da ke tsakanin hukumar tara haraji ta FRIS da wasu jihohin ƙasar nan kan batun ikon karɓar haraji na ci gaba da zafafa ganin cewa ana samun ƙarin jihohin da ke ra'ayin su ma a ƙyale su su…
Read More
Martanin Labarina: Naziru Sarkin Waƙa da Aminu Saira ba su da laifi ko kaɗan

Martanin Labarina: Naziru Sarkin Waƙa da Aminu Saira ba su da laifi ko kaɗan

Daga Al-AMIN CIROMA Na karanta wani labari mai taken 'Naziru Sarkin Waƙa Ya Hayaƙa 'Yan Jarida' wanda da dama mutane suka mayar da martani a kafafen sadarwa, inda suka bayyana abin da fitaccen mawaƙin ya yi a matsayin tozarci da 'yan jarida. Babu shakka masu wannan ra'ayi suna da nasu hujjojin, bai kamata a ga laifinsu ba, sai dai ni na bambanta da mafi yawan ra'ayoyin nasu. Amma na fi karkata kan ra'ayin Malam Nazifi Dawud, wanda ya nuna yadda 'yan jaridar da kansu suke wulaƙanta kansu. A iya sanina dai, aikin jarida aiki ne mai ɗimbin ƙa'idoji da 'Farillai,'…
Read More
Rikici tsakanin ‘yan fim da ‘yan jarida a fim ɗin Labarina

Rikici tsakanin ‘yan fim da ‘yan jarida a fim ɗin Labarina

Daga ABDUSSALAM BARISTA HOTORO Wasu ‘yan jaridu sun koka kan yadda suka yi tunnain an ci zarfin ɗan jarida a cikin fim mai dogon zango mai suna Labarina. A cikin kashi na 11 a zango na uku an nuna ɗan jarida na neman ba’asi a wajen fitaccen mawaƙi Nazir M. Ahmad (Sarkin Waƙa) dangane da rayuwar Sumayya (Nafisa Abdullahi) wanda ya jaddada ita ya kamata a tuntuɓa kasancewar rayuwar ce. A yayin da ɗan jarida ya dage wajen bibiyar labari sai Naziru ya nemi a ba wa ɗan jarida kuɗin mota don yayi na mota alamun ba zai iya samun…
Read More
Malami Bukkuyum: Mutumin da ya shafe shekaru 35 yana facin hanyoyin Najeriya

Malami Bukkuyum: Mutumin da ya shafe shekaru 35 yana facin hanyoyin Najeriya

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMAMAD a Nasarawa Malami Bukkuyum, ɗan Jihar Zamfara ne, wanda ya shaida wa Manhaja cewa, ya kwashe shekaru 35 yana facin hanya bayan ya haƙo ƙasa ya cike ramummuka da ke manyan titina Najeriya. Ba sabon labari ba ne mutum ya ce, ya bi titi a cikin biranen ƙasar nan da ya ke da ramummukan da sai direba ya zaɓi mai ƙarancin zurfi ya faɗa sannan ya wuce. Wannan ya sa matasa ko majiya ƙarfi suke gogoriyon saro ƙasa suna cike hanyoyi, domin neman na sa wa a bakin-salati a manyan da ƙananan hanyoyin ƙasar da ke cikin…
Read More
Tasirin kwalliyar mata a gidan aure

Tasirin kwalliyar mata a gidan aure

Daga AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon zan yi bayani a kan irin tasirin da kwalliyar 'ya mace da gyaranta suke da shi wajen janyo mata daraja a gidan aurenta ko kuma akasin haka. Da farko dai mu duba me ake nufi da kwalliya? Kwalliya dai tana nufin duk wani nau'i na gyara da mace za ta yi tun daga wanke can, gyaro can, shafa wannan, goge wancan da sauransu. Dukkansu suna cikin kwalliya ba sai ta fuska ba kaɗai. Nau'ikan kwalliya:Akwai irin su gyaran gashi a taje shi, ko a…
Read More
Hatsarin kasa kaya a gefen titi

Hatsarin kasa kaya a gefen titi

Kwanan nan, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta yi gargaɗi mai tsanani ga ‘yan kasuwa da ke da ɗabi’ar mayar da kafaɗun manyan tituna wajen baje kolin tallata kayansu da su guji irin waɗannan ayyukan da ba su dace ba, wanda hakan kuma ke ƙara haddasa cunkoson zirga-zirgar ababen hawa. Rundunar haɗin gwiwa na Minista kan Kula da zirg-zirgar ababen hawa (MTTM), ƙarƙashin jagorancin Ikharo Attah, ta yi wannan gargaɗin a madadin FCT yayin da take kan bincike a Kasuwar Nyanya, kafaɗun hanya da hanyoyin da ke yankin. Ikharo ya ce, tawagarsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba…
Read More
Na haramta saka kiɗan fiyano a wajen taron Hausa, matuƙar ni ne uban ƙungiya – Farfesa Abdallah

Na haramta saka kiɗan fiyano a wajen taron Hausa, matuƙar ni ne uban ƙungiya – Farfesa Abdallah

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Tsohon Shugaban Buɗaɗɗiyar Jami'a NOUN kuma mai ɗauke da matsayin Farfesa biyu a kan sa wato Farfesan Sadarwa da kuma Farfesan Kimiyyar Ilimi wato Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce daga yanzu indai an zo taron Hausa, kuma in dai an ce shi ne uban ƙungiya to ya haramta a saka kiɗan fiyano, amma ya ce idan ba za a yi haka ba sai a nemo wani uban amma ba shi ba, ya  ce hakan shi ne abinda zai burge shi. Farfesa Abdallah ya yi wannan jawabi ne a taron ranar Hausa ta duniya da…
Read More