Editor

9513 Posts
El-Rufai ga Hukumar JAMB: Ku daina bai wa ɗaliban Arewa maki na musamman

El-Rufai ga Hukumar JAMB: Ku daina bai wa ɗaliban Arewa maki na musamman

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya yi kira ga Hukumar Shirya Jarabawar Sahare Fagen Shiga Manyan Makarantu (JAMB) a kan ta daina bai wa ɗaliban Arewacin Nijeriya da suka rubuta jarabawarta maki na musamman. El-Rufai ya yi wannan kira ne a lokacin da ake hira da shi a wani shirin tashar ChannelsTV a safiyar Litinin da ta gabata. Ya ce ba yana nufin a bai wa ɗaliban ƙasa da makin da aka ƙayyade ba ne, amma dai a ba su makin daidai da yadda ake bai wa takwarorinsu a sauran sassan ƙasa domin su iya gogayya a duk inda suka…
Read More
Minista Sadiya ta sa Buhari ya kori Sanata Lado daga muƙaminsa

Minista Sadiya ta sa Buhari ya kori Sanata Lado daga muƙaminsa

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige shugaban Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP), Sanata Basheer Mohammed. Mohammed ya rasa kujerarsa ne watanni huɗu kacal da soma shugabancin hukumar. Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu, ya ce Buhari ya aminta da naɗin Fatima Waziri-Azi a matsayin wadda za ta maye gurbin Mohammed. Shehu ya ce naɗin Fatima ya taso ne sakamakon shawarar da Ministar Jinƙai da Agaji da Bunƙasa Zamantakewa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayar ne. Ya ce ministar ce ta nuna buƙatar gaggawar da ke akwai na…
Read More
Zaɓen Anambra: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

Zaɓen Anambra: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta yi amfani da hedikwatar ta ta yanki da ke Owerri wajen rarraba kayan aiki marasa hatsari na zaɓen gwamnan Jihar Anambra da za a yi. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron bayan wata huɗu da ya kan yi da manyan 'yan jarida, wanda aka yi a Abuja a ranar Laraba ta wannan makon. Farfesa Yakubu ya ce an yanke shawarar yin haka ne sakamakon hare-haren da aka kai tare da lalata kayan hukuma a Anambra kwanan nan. Ya ce kayan aikin zaɓen waɗanda ba…
Read More
Gyara bayan haihuwa

Gyara bayan haihuwa

Daga BILKISU YUSUF ALI Tambaya: Salam Malama barka da war haka. Ina da tambaya; shin akwai wani tanadi na musamman da mace ya kamata ta yi bayan ta haihu, saboda bayan na yi haihuwar fari sai maigidana ya ke ƙorafi kan na buɗe da yawa kuma Ina bushewa? Amsa: Akwai abubuwa da dama da mace ya kamata ta mayar da hankali a kansu tun lokacin da take da ciki kama daga abinci da motsa jiki da kulawa da kai da sauransu wanda tun daga lokacin ya kamata a fara tattalin al’amuran da za su biyo baya bayan an haihu. Amma…
Read More
Zargin satar fasaha ta kunno kai a Kannywood kan shirin ‘Wuf’

Zargin satar fasaha ta kunno kai a Kannywood kan shirin ‘Wuf’

Daga SHAFIU ALI MAILANTARKI A 'yan kwanakin nan mun fuskanci wani abin da ya ɗaure mana kai game da masana'antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. Mun shaidi cewa ita ce masana'anta da a yanayi da zubin gudanarwarta take fama da suka ta fuskoki masu yawan gaske. Kasantuwar fim abu ne da ake nunawa, wato labari ake bayarwa, wannan ya sa malaman Hausa da Adabin Hausar suke ƙorafin ana ɓatanci ga al'adu da addini a inda aka ce madubi ake yi gare su ana yaɗa su ga al'ummar duniya, duk da cewar iyo ake yi a taƙaitaccen jigo…
Read More
Allah ya ƙara ba mu shugaba irin Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi

Allah ya ƙara ba mu shugaba irin Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi

Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya yi addu’ar Allah ya sake azurta Nijeriya da shugaba mai farar zuciya irin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023. Gwamna Umahi ya bayyana wannan fata nasa ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala ganawa da Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Umahi ya ce ba yanzu ne ya dace a kaɗa gangar siyasar 2023 ba, yana mai cewa yin hakan ka iya karkatar da hankalin shugaban ƙasa da na gwamnoni. Ya ce ya zuwa yanzu ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban a…
Read More