Allah ya ƙara ba mu shugaba irin Buhari a 2023, inji gwamnan Ebonyi

Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya yi addu’ar Allah ya sake azurta Nijeriya da shugaba mai farar zuciya irin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Gwamna Umahi ya bayyana wannan fata nasa ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala ganawa da Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Umahi ya ce ba yanzu ne ya dace a kaɗa gangar siyasar 2023 ba, yana mai cewa yin hakan ka iya karkatar da hankalin shugaban ƙasa da na gwamnoni.

Ya ce ya zuwa yanzu ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban a yankin Kudu-maso-gabas sun ba da himma wajen tabbatar da an miƙa wa yankin nasu tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamnan ya ci gaba da cewa shi dai a yanzu, ya maida hankalinsa ne wajen ƙoƙarin kammala ayyukan da ya sa gaba a jiharsa. Tare da cewa zai waiwayi harkar siyasa ne idan ya rage masa shekara guda ya kammala wa’adinsa, wato daga 29 ga Mayun 2022 ke nan.

Ya ƙara da cewa yana ganin wannan tsari shi ne irin tunanin da sauran gwamnonin Kudu-maso-gabas ke da shi haka ma gwamnonin APC baki ɗaya.