Editor

9513 Posts
Buhari ya naɗa Adetifa a matsayin sabon shugaban Hukumar NCDC

Buhari ya naɗa Adetifa a matsayin sabon shugaban Hukumar NCDC

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Dr Ifedayo Morayo Adetifa a matsayin sabon shugaban Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC). Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, shi ne ya bayyana naɗin Adetifa a jiya Litinin. Da wannan, ya tabbata Adetifa ya zama magajin Chikwe Ihekweazu wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta naɗa shi a muƙamin Mataimakin Darakta-Janar na hukumar. Cikin wata wasiƙa da ya aika wa Ihekweazu, Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus, ya bayyana Ihekweazu a matsayin mataimakin shugaban sashen tattara bayanan gaggawa na hukumar. Kazalika, wasiƙar ta nuna Ihekweazu sai  soma aiki a WHO daga…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yar tsohon daraktan NBC, Abdulkadir a Katsina

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yar tsohon daraktan NBC, Abdulkadir a Katsina

A daren Litinin da ta gabata 'yan bindiga suka kai hari a rukunin gidaje na Bakori a jihar Katsina inda suka sace yarinyar tsohon darakta a hukumar NBC, Alhaji Ahmed Abdulkadir, mai suna Laila. Haka nan, 'yan bindigar sun haɗa da wasu mutum uku yayin harin, wato Alhaji Bello Aminu Bakori da Shamsuddeen Aminu da kuma Habibu Rabe suka yi gaba da su. 'Yan fashin sun kai harin ne da misalin ƙarfe 9 na dare a wannan rana ɗauke da bindigogi ƙirar AK 47. An ce kimanin ƙasa da awa guda bayan harin, sai aka haɗa kan 'yan banga don…
Read More
Sojoji sun tarwatsa maɓuyar ‘yan fashin daji a Kaduna

Sojoji sun tarwatsa maɓuyar ‘yan fashin daji a Kaduna

Sakamakon ruwan bamabamai da sojoji suka yi wa 'yan fashin daji a Zamfara wanda ya yi sanadiyar halaka da damansu a 'yan kwanakin nan, hakan ya rutsa da wata maɓuyar ɓarayin a jihar Kaduna. Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna maɓuyar da sojojin suka tarwatsa a dajin Kawara a yankin ƙaramar hukumar Igabi, nan ne 'yan bindigar kan ɓoye suna gudanar da harkokinsu na takura wa al'umma. Kamar yadda bayanai suka tabbatar, a ƙalla 'yan bindiga 50 ne aka kashe sakamakon ruwan bamabamai da sojoji suka yi wa maɓuyar tasu a ƙarshen makon da ya gabata. An bayyana cewa…
Read More
Dokar hana kiwo: Ƙungiyar Miyetti Allah ta nemi Majalisar Tarayya ta taka wa gwamnoni birki

Dokar hana kiwo: Ƙungiyar Miyetti Allah ta nemi Majalisar Tarayya ta taka wa gwamnoni birki

Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, ta yi kira ga Majalisar Ƙasa da ta sa baki wajen dakatar da yunƙurin da wasu gwamnonin Nijeriya suka yi na neman kafa dokar da za ta hana Fulani makiyaya kiwo a sake. Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Saleh Alhassan, shi ne ya yi wannan kira a wajen wani taro da suka gudanar a garin Uke da ke yankin Ƙaramar Hukumar Karu a jihar Nasarawa. Alhassan ya ce wannan doka za ta yi wa zaman lafiyar da ake samu yanzu tarnaƙi a ƙauyuka, da yi wa zamantakewa barazana da kuma tsananta matsalar satar shanu.…
Read More
Guinea: ECOWAS ta buƙaci a gaggauta sako Conde, maido da gwamnatin ƙasar kan tsarin da aka san ta

Guinea: ECOWAS ta buƙaci a gaggauta sako Conde, maido da gwamnatin ƙasar kan tsarin da aka san ta

Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta buƙaci sojojin Tarayyar Guinea da ke riƙe da Shugaban Ƙasar, Alpha Conde, da su gaggauta sako shugaban haɗa da dukkan jami'an da suke riƙe da su ba tare da gindaya wani sharaɗi ba. Cikin wata sanarwar bayan taro da ta fitar a ranar Lahadi wadda ta sami sa hannun Shugaban Ƙasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ECOWAS ta nuna takaicinta tare da yin Allah-wadai da wannan mummunan al'amari da sojojin Guinea suka aikata na yunƙurin kifar da gwamnatin Conde. ECOWAS ta kuma buƙaci ba tare da ɓata lokaci ba, a gaggauta…
Read More
Tsufa (3)

Tsufa (3)

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Har yanzu dai , mu na  magana ne a kan tsufa. Muna bayanin sauye sauyen da shi tsufa ya ke kawo a sassan jiki na ɗan Adam. Yau zan ɗora daga inda na tsaya. Shi tsufa ya na kawo raguwar fikira da azanci,  raguwar tsokar nama a jiki, ƙaruwar kitse a jiki, rauni a gaɓɓai, raguwar ƙarfin…
Read More
Dalilan da suke jawo matsalolin aure a yau

Dalilan da suke jawo matsalolin aure a yau

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Fatan kowa ya san wannan kalma ta 'aure'. Duk inda aka shiga aka fita, magana ce dai ƙwaya ɗaya da ake ta yin ta shekara da shekaru. Ba kalma ce ta wasa ba, kuma ba kalma ce ta riƙon je-ka-na-yi-ka ba. Kalma ce mai muhimmanci da amfani. Kalma ce da dukkan Musulmi yake daraja ta da girmamawa. Saɓanin yanzu da aka yi wa kalmar riƙo na sakainar ɗiban kashi ba. Da yawa yanzu an mai da auren abun wasa ko wani abu kawai na son rai. Ana ganin ma'aurata na cin karensu babu babbaka. Yara sun…
Read More
Nijeriya ta yi tir da juyin mulkin Guinea

Nijeriya ta yi tir da juyin mulkin Guinea

Gwamnatin Nijeriya ta yi tir da juyin mulkin da sojoji suka yi a Tarayyar Guinea ran Lahadi. Nijeriya ta nuna damuwanta kan juyin mulkin ne cikin wata sanarwar manema labarai da Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta fitar, inda ta bayyana juyin mulkin da lamari da ya saɓa wa dokar Ƙungiyar ECOWAS kan sha'anin dimukuraɗiyya da kuma shugabanci nagari. Nijeriya ta ce sam ba ta goyi bayan haka ba kuma ba za ta taɓa mara wa hakan baya ba. Cikin sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar, Esther Sunsuwa, ta sanya wa hannu, Nijeriya ta yi kira ga waɗanda ke da…
Read More
Guinea: Mun kama Shugaba Conde mun rushe gwamnatinsa – Sojoji

Guinea: Mun kama Shugaba Conde mun rushe gwamnatinsa – Sojoji

Sojojin ƙasar Guinea sun yi iƙirarin cewar sun gudanar da juyin mulki sun kuma kama Shugaba Ƙasa Alpha Conde, yayin da a hannu guda gwamnati ke cewa ta daƙile yunƙurin. Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce ya samu faifan bidiyo mai ɗauke da wani hafsan soji kewaye da wasu sojojin da ke ɗauke da bindigogi da yake sanar da kama shugaban ƙasa da kuma soke kundin tsarin mulkin ƙasar. Hafsan sojin ya kuma sanar da rufe iyakokin sama da ƙasa da kuma rusa gwamnatin ƙasar, amma kuma gwamnatin Conde ta sanar da gabatar da sanarwar da ke bayyana murƙushe yunƙurin…
Read More
Ƙasashen Larabawa sun soma tura agajin abinci da magunguna zuwa Afghanistan

Ƙasashen Larabawa sun soma tura agajin abinci da magunguna zuwa Afghanistan

Qatar ta ce ta soma gudanar da ayyukan bada agaji na 'yan kwanaki ya zuwa Afghanistan inda za ta riƙa tura kayayyakin buƙata na yau da kullum don amfanin 'yan ƙasar. Qatar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon jinkirin kai tallafi ƙasar da aka samu daga ɓangaren ƙasashen yammaci tun bayan da Taliban suka karɓe ikon ƙasar a watan jiya. Qatar ta yi wannan yunƙuri ne bayan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Baharain suka tura kayan agaji zuwa Afghanistan a ƙarshen mako da suka haɗa da kayan abinci da kuma magunguna. Bayanai sun nuna an ga jirgin Qatar…
Read More