05
Sep
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Jihar Filato da ke tsakiyar Nijeriya ta sake shiga kanun labarai a kafafen sadarwa daban-daban cikin watan da ya gabata, sakamakon wasu sabbin hare-hare da suka auku a babban birnin jihar, wato Jos. A dalilin wata rikita-rikita mai nasaba da ƙabilanci da addini, wacce aka jima ana yi tsawon shekaru fiye da 20, inda aka samu asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi da har yau ba a gama tantance adadinsu ba. Labari na baya bayan nan nan da ya fi ɗaukar hankali daga jihar shi ne, taron manema labarai na duniya da Majalisar Dokoki ta Jihar Filato…
