Editor

9513 Posts
An wulaƙanta min littafi na wai don ni yaro ne – Aliyu Idris Author

An wulaƙanta min littafi na wai don ni yaro ne – Aliyu Idris Author

*Marubuci kan sauya gurɓatattun tunanin mutane zuwa nagartattu - Aliyu Idris Author A lokacin da a ka ga littafi, hankali da tunanin mai karantawa zai tsaya akan babban mutum ne ya rubuta shi, wato mai yawan shekaru. Har ta kai idan a ka ga marubuci da ƙarancin shekaru sai a rena rubutun sa tun kan a karanta. Hakan ce ta sa yara ma su sha'awar rubutu jikin su kan yi sanyi idan sun tuna yanda a ke wa marubuta tsaran su. Dalilin ke nan da yasa ba kasafai ake samun marubuta masu ƙananen shekaru ba, duk da cewa akwai masu…
Read More
Haushin kaza: Kishin matar uba ga ‘ya’yan miji

Haushin kaza: Kishin matar uba ga ‘ya’yan miji

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanku da jimirin karatun jaridarku ta Manhaja, mai farin jini. A wannan mako za mu tattauna ne a kan yadda kishin mata yake zarcewa daga kan kishin miji zuwa kishi a kan yaran da suka haifa. Zan yi matashiya a kan wannan karin magana: "haushin kaza huce kan dami". Wato yadda idon kishiyoyi yake rufewa ruf a kan kishi har ma su dinga ramuwa da fanshe haushin kishinsu a kan 'ya'yan miji. Haka ma wasu 'yan mijin sukan ɗauki matar uba a matsayin kishiya wadda suke kishi da gasa da ita a kan duk wasu abubuwa…
Read More
Abubuwan lura a bayanin Sarkin Musulmi kan manyan matsalolin Nijeriya

Abubuwan lura a bayanin Sarkin Musulmi kan manyan matsalolin Nijeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bayyana takaicinsa ga irin yadda rashin fahimtar juna tsakanin 'yan Nijeriya ke ƙara ta’azzara, inda ya ce, wannan shi ne babban barazanar da ƙasar ke fuskanta, ya na mai cewa, don Nijeriya ta samu zaman lafiya, dole ne 'yan ƙasa su so juna. Bayanin ya na tabbatar da furucin Shugaba Muhammadu Buhari kan babbar matsalar ƙasar, sarkin yana nuni da cewa tare da fahimtar cewa, 'yan Nijeriya za su yi haƙuri da juna, domin zaman lafiya ya samu wajen zama a ƙasar. Sarkin, wanda ya yi magana a lokacin taron ƙungiyar…
Read More
Kotu ta buƙaci a yi wa Abduljabbar gwajin ƙwaƙwalwa

Kotu ta buƙaci a yi wa Abduljabbar gwajin ƙwaƙwalwa

Kotun Shari'a a jihar Kano, ta ba da umarnin s ɗauki Sheikh Abduljabbar Nasiru-Kabara zuwa asibitin mahaukata ta Dawanau don gwajin ƙwaƙwalwarsa. Gwamnatin Kano na tuhumar Abduljabbar ne da laifuka guda huɗu da suka shafi yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW). Sa'ilin zaman shari'a a ranar Alhamis, Alƙalin kotun, Malam Ibrahim Sarki-Yola, ya ba da umarnin a tafi da wanda ake zargin ya zuwa asibitin mahaukata ta Dawanau don binciken lafiyar ƙwaƙwalwarsa. Kazalika, Alƙali Sarki-Yola a sake gudanar gwaji kan Abduljabbar a Asibitin Ƙwararru ta Murtala da ke Kano. Daga bisani, Alƙali Sarki-Yola ya ɗage shari'ar zuwa ranar 16…
Read More
Da kyakkyawar manufa muka horar da sojoji mata – Rundunar Sojin Saudiyya

Da kyakkyawar manufa muka horar da sojoji mata – Rundunar Sojin Saudiyya

Rundunar sojoji ta Ƙasar Saudiyya ta ce, da kyakkyawar manufa ta bai wa sojoji mata horo don ci gaba da yi ƙasar hidima yadda ya kamata. Babban jami'i na rundunar, Maj. Gen. Adel Al-Balawi, shi ne ya bayyana haka a wajen bikin yaye sojoji mata karon farko a Saudiyya a Larabar da ta gabata. Al-Balawi ya ce cibiyar bai wa mata horon an tsara ta daidai da na ƙasa-ƙasa wadda ake sa ran za ta taimaka wa rundunar sojojin ƙasa cimma buƙatunta a gaba. Wannan shi ne karo na faro da Ƙasar Saudiyya ta bai wa mata damar shiga aikin…
Read More
Ƙalubalen da ke gaban Hausawa a ƙarni na 21

Ƙalubalen da ke gaban Hausawa a ƙarni na 21

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ranar Alhamis da ta gabata ne 26 ga watan Agusta, wasu ƙungiyoyi da kafafen sadawar zamani daban-daban suka gudanar bikin ranar Hausa ta duniya, wanda ya kasance karo na biyu da aka shirya irin sa a bainar jama'a, saɓanin yadda aka faro shi kuma ya taqaita a shafukan sada zumunta, tun bayan da wani ɗan jarida ma'aikacin BBC Hausa mai suna Abdulbaki Jari ya ƙirƙiro da ita a shekarar 2015. A shekarun baya babu irin wannan rana da za a ce al'ummar Hausawa sun ware suna tunatar da juna kyawawan al'adun su, gudunmawar da harshen…
Read More
Waɗanda ke neman ruguza Shi’a ba su yi nasara ba, cewar El-Zakzaky

Waɗanda ke neman ruguza Shi’a ba su yi nasara ba, cewar El-Zakzaky

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, (IMN), Shaikh Ibraheem El-Zakzaky, a makon da ya gabata, ya bayyana cewa, waɗanda ke neman rusa ƙungiyar bayan kisan kiyashin Zariya a shekarar 2015 ba su samu nasara ba. El-Zakzaky ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa ta farko da wakilan ɓangarori daban-daban na dandalin addini a Abuja. Ya yi bayanin cewa zaluncin da aka yi wa Harkar Musulunci a Nijeriya, wanda ya cika da shekaru shida na zaman gidan yari, ya mara famtsama sanin ƙungiyar a dukka faɗin a duniya. El-Zakzaky ya ce, “yayin da aka ƙaddamar da…
Read More
Matsalar Tsaro: Gwamna Bello ya haramta cin kasuwanni kara, sayen fetur a jarka a faɗin Neja

Matsalar Tsaro: Gwamna Bello ya haramta cin kasuwanni kara, sayen fetur a jarka a faɗin Neja

A matsayin wani mataki na yaƙi da matsalolin tsaro a jihar Neja, Gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya kafa wasu sabbin dokoki da za su taimaka wajen kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro da jihar ke fama da su. Sabbin matakan tsaron da Gwamna Bello ya sanar a ranar Laraba, ya ce za su soma aiki ne daga ranar 1 ga Satumban 2021. Waɗannan matakai sun hada da haramnta cin kasuwanni dabbobi na mako-mako a faɗin jihar, dole duk motar da za ta shigar da dabbobi cikin jihar ta nuna shaidar inda dabbobin suka fito da inda aka sayo su da…
Read More
MOPPAN ta yi haɗin gwiwa da NDLEA don yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

MOPPAN ta yi haɗin gwiwa da NDLEA don yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirin Fim (MOPPAN) ta bayyana cewar ta samu damar haɗin gwiwa da hukumar Hukumar Yaƙi da Sha da Kuma Yaƙi da Fataucin Miyagu Ƙwayoyi (NDLEA) domin bayar da tata gudunmawa wajen yaƙi da shan ƙwayoyi. Cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami'inta na hulɗa da jama'a na ƙasa, Al-Amin Ciroma, MOPPAN ta ce ta cimma wannan nasara ne sakamakon takardar da ta rubuta wa hukumar ta neman yin haɗin gwiwa wajen cigaba da yaƙi da miyagun ƙwayoyi a faɗin Nijeriya. Sanarwar ta nuna biyo bayan wannan haɗakar, Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari,…
Read More
An yi wa Hukumar Alhazai tunin maido da kuɗin adashin gata

An yi wa Hukumar Alhazai tunin maido da kuɗin adashin gata

Daga AMINA YUSUF ALI A ƙoƙarinsu na ganin sun cikasa wannan damar da kundin mulki ya ba wa al'umma na   'yancin samun bayani, mawallafan jaridar Hajj Reporters sun aike wa da hukumar alhazai takardar tuni ga hukumar jin daɗin alhazai domin su ba da ƙarin bayani a kan batun maido kuɗaɗen aikin hajji ga alhazan da suka biya kuma ba su samu damar tafiya ba a shekarun 2020/2021. Da ma ba wannan ne karo na farko da kamfanin jaridar yake aike wa da hukumar makamanciyar irin wannan wasiƙa ba, amma har yanzu shiru ba amsa. Waɗannan jawabai suna ƙunshe ne…
Read More