Editor

9513 Posts
Uwargidan Ganduje za ta fito takara a Jigawa

Uwargidan Ganduje za ta fito takara a Jigawa

Daga ABUBAKAR M. TAHEER a Haɗejia Cikin ’yan kwanakin nan labarin takarar Uwargidan Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, wato Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje, yana daɗa jan hankulan al’ummar jihohin Kano da Jigawa. Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje, wacce ta ke ’yar asalin garin Malam Madori da ke Jihar Jigawa ce, ta kasance macen da masu sharshi kan al'amuran yau da kullum kan kalli lamarinta a matsayin akwai lauje cikin naɗi. Cikin kwanakin baya an jiyo amon zugar wasu ’yan jam'iyyar APC na cewa, sun bar jam'iyyar ta APC sakamakon kallon tafiyar hawainiya da jam'iyyar ta ke yi. Al’ummar yankin na…
Read More
Kotu ta yi fatali da buƙatar Malami ta neman janye dokar haramcin kama Igboho

Kotu ta yi fatali da buƙatar Malami ta neman janye dokar haramcin kama Igboho

Alƙali Ladiran Akintola na Babbar Kotun Jihar Oyo, ya ƙi amincewa da buƙatar Babban Lauyan Nijeriya (AGF) Abubakar Malami, ta neman kotu ta janye dokar haramta kama Chief Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho da ta shata, wadda ta haramta wa Malami da sauran hukumomin tsaro damƙe Igboho. Kotun ta ƙi amincewa da buƙatar Malami ne yayin zamanta a jiya Litinin bayan da Lauyoyin Malami suka ɗaga batun a gabanta. Lauyoyin sun buƙaci kotun da ta janye dokar haramcin kama Igboho saboda a cewarsu, wannan abu ne da bai kamata ya zarce kwanaki bakwai ba. Idan dai…
Read More
Ba mu da wani shirin soma yajin aiki yau Talata, cewar ASUU

Ba mu da wani shirin soma yajin aiki yau Talata, cewar ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ta ce, ba ta da wani shiri na soma yajin aiki aiki a yau Talata, kamar yadda ɗaya daga cikin shugabannin ASUU na ƙasa ya shaida wa manema labarai. Dr. Dele Ashiru, wanda kuma shi ne shugaban ASUU reshen Jami'ar Legas, ya shaida wa manema labarai a jiya Litinin cewa, ba haka kawai ASUU ke shiga yajin aiki ba face sai da cika wasu sharuɗɗanta. Ashiru ya ce lallai ne ƙungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin zuwa Talata, 31 ga Agustan 2021, a kan ta biya mata wasu buƙatunta. Yana mai cewa, "Da a ce…
Read More
Da Ɗumi-ɗuminsa: Gwamna Sule ya sauke kwamishinoninsa

Da Ɗumi-ɗuminsa: Gwamna Sule ya sauke kwamishinoninsa

Labarin da ya shigo wa MANHAJA yanzu-yanzu daga jihar Nasarawa, ya nuna Gwamnan Jihar, Engr. Abdullahi A.Sule, ya rushe 'yan majalisarsa. Gwamnan da kansa ya ba da sanarwar sauke 'yan majalisar a yau Litinin bayan wani taro na masu ruwa da tsaki a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Lafia. Wannan mataki ya shafi har da masu bai wa Gwamna shawara da sauransu. Gwamna Sule ya yaba wa kwamishinonin da hadiman da ya sauke bisa gudunmawarsu da suka bayar wajen cigaban gwamnatinsa da ma jihar baki ɗaya.
Read More
Baje sirrin gidanmu a yanar gizo ba birgewa ba ne

Baje sirrin gidanmu a yanar gizo ba birgewa ba ne

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Wata sabuwa in ji 'yan caca haka masu magana suka ce. Yau ma ga mu kamar kullum Cikin filinmu mai albarka. Za mu yi magana a kan sabuwar al'adar da ta shigo mana a shafukan yanar gizo, ta kwance sirrin gidajenmu. Yanzu wannan ɗabi'a ta zama kamar ba duniya ce za ta gani ba, idanunmu sun rufe. Ba ga mata ba, ba ga maza ba, wajen baje abunda ya kamata a ce a gida aka yi ko a cikin dangi, a'a, yanzu ɗebowa ake a baje kowa na gani. Ikon Allah! Kuma yawancin wannan rayuwar mata…
Read More
Tsufa (2)

Tsufa (2)

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan'uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. A satin da ya gabata, mona tara magana ne a kan tsufa. Na yi bayanin cewa tsufa wani mataki ne na rayuwar ɗan Adam. Yau zan ɗora daga inda na tsaya. A satin da ya wuce ɗin dai,  nayi bayanin tasirin wasu abubuwa game da saukowar tsufa, irinsu cima, muhallin da mutum ya taso a ciki, tsarin rayuwa,…
Read More
Duk mai son cin kujerar Gwamnan Kano a 2023 ya ba ni takarar mataimakiya, inji Rashida Maisa’a

Duk mai son cin kujerar Gwamnan Kano a 2023 ya ba ni takarar mataimakiya, inji Rashida Maisa’a

Rashida Abdullahi, wadda mutane suka fi sani da ‘Mai Sa’a’, fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood ce da ta daɗe tana jan zarenta; bayan nan kuma ‘yar siyasa ce a Jihar Kano, wanda yanzu haka tana ɗaya daga cikin masu taimaka wa Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje a ayyuka na musamman.A wannan hirar da Manhaja ta yi da ita, ta bayyana aniyarta na tsayawa takarar mataimakiyar gwamna a jihar idan Allah ya nufe mu da ganin zaɓen 2023. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance: Daga AISHA ASAS, a Abuja Za mu so ki fara da gabatar da kan ki.Assalamu alaikum…
Read More
Matawalle ya kafa sabbin dokokin tsaro 7 don yaƙi da matsalolin tsaron Zamfara

Matawalle ya kafa sabbin dokokin tsaro 7 don yaƙi da matsalolin tsaron Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau A matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro a Jihar Zamfara, Gwamnan Jihar, Dr. Mohammed Bello Matawalle, ya kafa wasu sabbin dokoki har guda bawkai waɗanda kuma aka buƙaci al'ummar Zamfara su kiyaye su don taimaka wa gwamnatin jihar wajen cimma ƙudurinta na neman ganin bayan matsalolin tsaro a jihar. Cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ayuba N. Elkanah, ya fitar a ranar Lahadi ta zayyano waɗannan dokoki da suka haɗa da: Haramta cin kasuwannin mako-mako a faɗin jihar, haramta sayar da man fetur…
Read More
Da Ɗumi-ɗuminsa: ‘Yan bindiga sun kashe ɗan gidan Sanata Ibn Na Allah, Captain Abdulkarim Na Allah a Kaduna

Da Ɗumi-ɗuminsa: ‘Yan bindiga sun kashe ɗan gidan Sanata Ibn Na Allah, Captain Abdulkarim Na Allah a Kaduna

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a Kaduna, sun kashe Captain Abdulkarim Bala Na Allah, wanda shi ne babban ɗan Sanata Bala Ibn Na Allah, a gidansa da ke umar Gwandu a Malali, Kaduna. Za a yi jana'izar marigayin a maƙabartar Unguwar Sarki Kaduna. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda inda wasu 'yan bindiga suka halaka Major Christopher Dator bayan sun yi garkuwa da shi sakamakon harin da suka kai makarantar horas da manyan jami'an sojoji (NDA) a Kaduna. Cikakken rahoton na nan tafe.
Read More
Harin NDA ya tayar da hazo

Harin NDA ya tayar da hazo

*'Yan bindiga sun kashe da sace jami’an soja a Kaduna*Za a farauto 'yan ta'addar – Makarantar NDA*Ina zargin ’yan cikin gida – Babban Hafsan Tsaro*Ya kamata wannan ya zama silar gamawa da 'yan bindiga – Janar Kuka-sheka*An tsara harin ne don a kunyata Buhari – Garba Shehu*Tsaron Nijeriya ya rikice – ACF*Buhari ya mayar da martani mai zafi*Masu lura da CCTV ba bacci suke ba – Hedikwatar Tsaro Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Abin mamaki da baƙin ciki mai kamar almara ya afku a ranar Talatar da ta gabata a wani harin da 'yan bindiga suka kai a Makarantar…
Read More