29
Aug
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Rikicin cikin gida ya kunno kai, wanda ya ke neman raba kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a Jihar Gombe, inda aka fara takun saƙa tsakanin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya da magoya bayansa da kuma tsohon ubangindansu a siyasa kuma tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Muhammad Danjuma Goje, wanda shine sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya a halin yanzu. Rikicin ya fara kunno kai ne a lokacin da jam’iyyar ta shirya zaɓen shugabanni na matakin gunduma a dukkan faɗin ƙasa, inda shi Sanata Goje ake ganin ya so yin abin da ya so a yankinsa ta hanyar…
