Bayan shafe kwanaki 88 a hannun ‘yan bindiga, an sako ɗaliban Islamiyyar Neja

Rahotanni daga jihar Neja, sun tabbatar da ‘yan bindiga sun sako ɗaliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko su 70 da aka yi garkuwa da su a garin Tegina.

Sakin nasu na zuwa ne bayan da suka shafe kwanaki 88 a hannun ‘yan bindigar.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan labari, an ce ɗaliban suna hanyarsu ta zuwa Minna daga Kagara.

Tun farko sai da aka biya ‘yan bindigar Naira miliyan N50 a matsayin kuɗin fansa don dai a samu su sako yaran amma suka ƙi amincewa.

An yi garkuwa da ɗaliban ne su 156 daga Islamiyyar a ranar Litinin, 30 ga Mayun da ya gabata, bayan da ɗaruruwan ‘yan bindiga suka yi wa garin dirar mikiya lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda a wancan lokaci.

A watan Yuni ne ɓarayin suka buƙaci a biya su fansar milyan N200 kafin su sako ɗaliban.

Daga baya ne da iyayen yara suka ga wankin hula na neman ya kai gwamnati dare, suka yanke shawarar neman taimako a masallatai da mujami’u don tara kuɗin da za su yi amfani da shi wajen ceto yaransu.