26
Aug
Hukumar Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC) ta aika wa tashar Channels TV ta takardar aikata ba daidai ba kan “kalaman harzuƙawa, rarrabuwan kai da rashin adalci” da Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi, a shirin karin kumallo na tashar a ranar Talatar da ta gabata. NBC ta bayyana haka ne a cikin wata wasiƙa da ta aike wa gidan talabijin ɗin, mai ɗauke da kwanan wata 24 ga Agusta, 2021, wadda ta samu sa hannun Babban Daraktanta, Balarabe Ilelah. Wasiƙar ta ce, “Shirin wanda ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Binuwai, Governor Samuel Ortom, an fahimci ya ƙunshi kalaman da…
