Mutum 964 sun kamu da cutar korona cikin yini guda a Nijeriya – NCDC

Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta bada sanarwar an samu ƙarin mutum 964 da suka harbu da cutar korona a ranar 4 Satumban da muke ciki.

Cibiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet da sauran kafofinta na soshiyal midiya, tana mai cewa ƙarin da aka samu ya shafi wasu jihohi ne su 19.

Alƙaluman waɗanda suka kamu da cutar da NCDC ta wallafa a shafin nata sun nuna Lagos na da mutum 456, Ondo-180, Edo-66, Rivers-62, Neja-26, Akwa Ibom-25, Ekiti-22, Kwara-22, Oyo-22, Kaduna-17, sannan Delta na da mutum 14.

Sauran jihohin sun haɗa da Binuwai-12, Gombe-9, Filato-9, Birnin Taraya-8, Jigawa-5, Ogun-4, Bayelsa-2, Nasarawa-2, sai jihar Bauchi da ke da mutum 1.

Kawo yanzu, NCDC ta ce jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ta kai 195,052, yayin da mutum 182,463 sun warke an kuma sallame su, sannan mutum 2,544 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar.