Hukumar Alhazai ta Abuja ta maida miliyan N432 ga maniyyata 334

Hukumar Alhazai ta Birnin Tarayya, Abuja ta bayyana cewa, ta biya miliyan N432 ga maniyyata 334 a matsayin maida musu kuɗaɗen da suka biya don zuwa Hajjin 2021 wanda bai yiwu ba saboda matsalar annobar korona.

Shugaban hukumar, Muhammadu Nasiru Ɗanmallam ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja yayin taron manema labarai da hukumar ta shirya ran Litinin.

Ɗanmallam ya ce, Nijeriya ba ta samu yin Hajji ba na shekaru biyu a jere, wato 2020 da 2021, sakamakon rufe hanya da ƙasar Saudiyya ta yi ga maniyyatan ƙetare don kauce wa barazanar annobar korona.

Ya ce a nasu ɓangaren, sun yi dukkan shirye-shirye don tafiya Hajji daidai da ƙa’idojin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da zummar komai zai kankama, amma a ƙarshe Saudiyya ta ba da sanarwar dakatar da ‘yan ƙetare daga aikin Hajjin wanda hakan ya shafi Nijeriya.

A cewar Ɗanmallam, kafin Saudiyya ta ba da sanarwar dakatar da baƙi daga aikin Hajjin, Hukumar Alhazai ta Abuja ta yi nasarar yi wa maniyyata 1,714 rajista don Hajjin 2021. Tare da cewa, wannan adadi na maniyyatan ya haɗa har da maniyyatan da suka nuna sha’awar zuwa Hajji a 2020.

Jami’in ya ci gaba da cewa, bayan da aka dakatar da zuwa Hajjin ne sai hukumar ta tuntuɓi maniyyatan a kan duk mai sha’awar ya karɓi kuɗinsa ya gabatar da kansa don a biya shi. Ya ce ya zuwa Juma’ar da ta gabata, sun maida kuɗi Naira miliyan 432 ga maniyyata 334.

Ya ƙara da cewa, hukumar ta maida wa maniyyatan kuɗaden nasu ne ba tare da zabtare ko taro ba daga ciki, kuma har yanzu shirin maida wa maniyyatan kuɗaɗensu na ci gaba da gudana.

Sai dai ya ce ragowar maniyyata 1,380 ba kowannensu ne ya samu zarafin biyan mafi ƙarancin kason da aka buƙace su da biya ba na miliyan N1,500,000.00 kamar yadda hukumar NAHCON ta buƙata.

Don haka ya ce maniyyatan da suka biya ƙasa da miliyan 1, ba a samu saka bayanansu ba a matattarar bayanan da NAHCON ta samar. Ya ce ana shawartar waɗannan maniyyata da su koma amfani da tsarin adashin gata na Hajj Savings Scheme (HSS) wanda NAHCON ta ƙirƙiro don ba su damar cika burinsu cikin sukuni ba tare da wata takura ba.

Daga bisani, Ɗanmallam ya ce maniyyatan da suka iya biyan mafi ƙarancin ajiya na miliyan N1,500,000 sannan suna da buƙatar ci gaba da ajiyar kuɗaɗensu don Hajji mai zuwa, suna iya yin haka, tare da cewa su za a fi bai wa muhimmancin ya zuwa lokacin shirye-shiryen Hajji na gaba.

Da wannan, shugaban hukumar ya ce ba za su karɓi kuɗain sabbin maniyyata don Hajjin 2022 ba har sai hukumar ta tabbatar da samun kason kujerun Hajji daga NAHCON, kuma bayan ta kammala da maniyyatan baya waɗanda ba su karɓi kuɗaɗensu ba.

A ƙarshe, Ɗanmallam ya yaba da irin goyon bayan da ‘yan jarida kan bai wa hukumarsu wajen gudanar da harkokinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *