Editor

9513 Posts
Juma’a Buhari zai tafi Landon a bisa dalilin duba lafiyarsa

Juma’a Buhari zai tafi Landon a bisa dalilin duba lafiyarsa

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai koma Landon ranar Juma'a kan batun da ya shafi kula da lafiyarsa. Sanarwar da mai bai wa Buhari shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Femi Adesina, ya fitar ta nuna bayan tafiyar, Buhari zai dawo gida Nijeriya ne a mako na biyu na watan gobe. Adesina ya ce,  “Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landon ran Juma'a, 25 ga Yuni, 2021 bisa dalili na duba lafiyarsa. “Sannan ya dawo a mako na biyu na Yuli, 2021".
Read More
2023: Ƙungiyar matasa ta bai wa Bala wa’adin ya bayyana aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa

2023: Ƙungiyar matasa ta bai wa Bala wa’adin ya bayyana aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa

Daga UMAR M. GOMBE Ƙungiyar Shugabannin Matasan Arewa (NYLF) ta bai wa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, wa'adi a kan ya fito ya bayyana amincewarsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyyar da ya ji ya fi gamsuwa da ita ko kuma a manta da batunsa a harkokin siyasa a gaba. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Elliot Afiyo, ya bayyana cewa bincikensu ya gano Gwamna Bala shi ne ɗaya tilo da ya fi cancantar zama shugaban ƙasa na gaba. Sa'ilin da yake miƙa wa Bala wasiƙar neman ya fito ya bayyana sha'warsa ta tsayawa takarar a babban…
Read More
‘Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon ɗan majalisar Kogi a Abuja

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon ɗan majalisar Kogi a Abuja

Daga WAKILINMU Da sanyin safiyar Alhamis wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace tsohon ɗan Majalisar Dokoki na jihar Kogi, Friday Sani Makama, a wani otel da ke Abuja. Ɓarayin sun kai wa ɗan majalisar hari ne ɗauke da bindigogi a ƙauyen Tugun Mada da ke yankin Zuɓa a Abuja, inda suka yi harbe-harben bindiga a iska don razanar da jami'an tsaron da ke kusa. Makama ya taɓa wakiltar mazaɓar Igalamela Odolu a Majalisar Dokokin jihar ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Bayanai sun nuna iyalan Makama sun samu sanin halin da ya faɗa ciki ne…
Read More
ACF ga Ohanaeze da Afenifere: Ku bai wa ‘yan Arewa mazauna cikinku kariya

ACF ga Ohanaeze da Afenifere: Ku bai wa ‘yan Arewa mazauna cikinku kariya

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar 'Yan Arewa (ACF) ta yi kira ga takwarorinta na ƙabilar Ibo da Yarabawa, wato Ohanaeze Ndigbo da Afenifere, da su kauce wa abubuwan da ka iya cutar da rayuka da dukiyoyin 'yan Arewa da sauran 'yan ƙasa mazauna yankunansu, tare da cewa a nata ɓangaren za ta tabbatar da kariyar 'yan ƙasa mazauna Arewa. Cikin sanarwar bayan taron shugabannin ƙungiyar na ƙasa, shugaban ACF na ƙasa, Audu Ogbeh ya yaba wa ƙungiyar Ohanaeze dangane da nesata kanta da ta yi da harkokin IPOB da kuma shirin Eastern Security Network (ESN). Ya ce nan ba da daɗewa…
Read More
Yadda maganin gargajiya ya yi sanadin mutuwar mutum 10 ‘yan gida ɗaya a Kwara

Yadda maganin gargajiya ya yi sanadin mutuwar mutum 10 ‘yan gida ɗaya a Kwara

Daga WAKILINMU Al'ummar ƙauyen Biogberu da ke yankin ƙaramar hukumar Baruten a jihar Kwara, sun faɗa wani hali na tashin hankali biyo bayan wasu 'yan gida ɗaya su goma da suka kwanta dama ɗaya bayan ɗaya a ƙauyen sakamakon wani maganin gargajiya da suka kwankwaɗa. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna wannan al'amari mai gigitarwa ya faru ne ran Juma'a ta makon jiya. Wata majiya mai tushe ta bayyana yadda lamarin ya faru, inda ta ce wasu 'yan ƙauyen su biyu, Okosi Musa da Worugura Julin, su ne suka bai wa wata mata mai suna Pennia Bonnie maganin gargajiya…
Read More
Babu mai raba mana Nijeriya, cewar Ganduje

Babu mai raba mana Nijeriya, cewar Ganduje

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce duk da irin matsalolin da Nijeriya ke fuskanta, za ta ci gaba da kasancewa ƙasa dunƙulalliya. Ganduje ya bayyana haka ne a Kano a matsayin martani kan ce-ce-ku-cen da ake yi a ƙasa inda wasu 'yan ƙasa ke rajin ɓallewa daga Nijeriya don kafa tasu ƙasar. Gwamnan ya ce yana da yaƙinin Nijeriya ba za ta rabe ba komai ƙalubalen da take fuskanta. Ya ci gaba da cewa ba ya son yin magana game da masu neman a raba ƙasa, saboda a cewarsa masu wannan buƙata…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da kwamitin shirin raba ‘yan Nijeriya miliyan 100 da fatara

Buhari ya ƙaddamar da kwamitin shirin raba ‘yan Nijeriya miliyan 100 da fatara

Daga UMAR M. GOMBE A Talatar da ta gabata ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da kwamitin da aka ɗora wa alhakin sanya ido kan shirin rage talauci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ana sa ran ya raba 'yan Nijeriya miliyan 100 da fatara. Buhari ya sha alwashin gwamnatinsa za ta fito da dabarun da za su taimaka mata wajen kuɓutar da 'yan Nijeriya milyan 100 daga ƙangin talauci a tsakanin shekaru goma masu zuwa. A jawabinsa yayin ƙaddamar da kwamitin, Buhari ya bayyana dabarar da kwamitin NPRGS za ta…
Read More
Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya kan ƙarin kasafin biliyan N895

Buhari ya nemi amincewar Majalisar Tarayya kan ƙarin kasafin biliyan N895

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Ahmad Lawan, ya karanta wa majalisa wasiƙar da Shugaba Ƙasa Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar yana neman amincewarta kan ƙarin kasafin kuɗi na biliyan N895. Lawan ya karanta wasiƙar Shugaban Ƙasar ne yayin zaman da majalisar ta yi a Talatar da ta gabata. Da ma dai kafin wannan lokaci, Majalisar Zartarwa ta yi na'am da ƙarin kasafin da Buhari ya nema. Bayanai sun nuna za a yi amfani da wani kaso mai tsoka daga kasafin wajen sayo wa sojoji ƙarin kayan aiki domin ƙara musu ƙarfi wajen yaƙi da ta'addanci da 'yan…
Read More
Kotu ta ɗaure Lawan shekara bakwai saboda cin-hancin $500,000

Kotu ta ɗaure Lawan shekara bakwai saboda cin-hancin $500,000

Daga UMAR M. GOMBE Wata Babbar Kotun Abuja, ta yanke wa tosohon ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Hon Farouk Lawan, hukuncin zaman gidan yari bisa laifin karɓar cin-hanci na $500,000 daga hannun hamshaƙin ɗan kasuwar nan, wato Femi Otedola.      Alƙaliyar kotun, Justice Angella Otaluka, ta bayyana cewa kotu ta yanke wa Hon Lawan daga Kano, hukuncin zaman gidan kaso na shekara bakwai a bisa aikata laifuka uku wanda hukumar ICP ta tuhume shi da aikatawa. ...cikakken bayani na nan tafe.
Read More