22
Jun
Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe kuɗi Naira biliyan 18 domin gina jami'o'in ƙwararru guda huɗu a faɗin ƙasa. Gwamnati ta bayyana haka ne a Litinin da ta gabata, inda ta ce jami'o'in da za a gida sun haɗa da ta fasaha da za a gina Jigawa da Akwa Ibom, sai kuma ta kiwon lafiya da nazarin ingancin abinci da magunguna da za a gina a Azare, jihar Bauchi da Ila Orangun, jihar Osun. Da yake yi wa manema labarai bayani a Abuja, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce…
