18
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ƙarshen makon jiya ne kansilan Kano, Honorabul Muslihu Yusuf Ali ya ƙaddamar da raba tallafi ga marayu 10 da aka samar wa gurbin karatu da ɗaukar nauyin su a 'Ihya'us Sunna Science and Commercial College' tare da bada tallafin N20,000 don ɗinka masu kayan makaranta. Shirin wanda ke ƙarkashin kwamitin Hajiya Bilkisu Yusuf Ali da ake wa laƙabi da 'Guringawa Education Promotion Committee' a turance zai duba makarantun kuɗi da ke cikin mazaɓar don samun gurbi na malamai da ɗalibai, sai kuma gidauniyar kansila ta bayar da tallafi. Haka kuma Muslihu Yusuf Ali,…
