16
Jun
Daga AMINA YUSUF ALI Ana sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a jihar Barno ran Alhamis idan Allah ya kai mu. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, shi ne ya bayyana haka yayin jawabin da ya yi wa 'yan jihar kai tsaye a kafar yaɗa labarai a Maiduguri. Tare da kira ga talakawansa da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata domin tarbar babban baƙon nasu. A cewar Zulum Buhari da tawagarsa za su ziryaci Barno ne domin la'akari da sha'anin tsaro na yankin Arewa-maso-gabas, kana ya ƙaddamar da tarin ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar a tsakanin shekaru…
