Bayan shekara 25, Nijeriya ta samu ƙarin rumfunan zaɓe 56,872

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta ce kawo yanzu adadin rumfunan zaɓe da Nijeriya ke da su ya kai 176,846.

Tun 1996 da aka ƙirƙiri ƙarin rumfunan zaɓe, hakan bai sake aukuwa ba sai bayan shekara 25, inda INEC ta sauya wasu cibiyoyin zaɓe guda 56,872 a faɗin ƙasa zuwa cikakkun rumfunan zaɓe.

Kafin wannan lokaci, rumfunan zaɓen da INEC ta san da su a faɗin ƙasa guda 119,974 ne.

Da yake jawabi a wajen wani taro tare da kwamishinonin hukumar a ranar Laraba, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce sun yi nasarar ɗauke rumfunan zaɓe 749 daga inda ba su dace ba zuwa inda suka dace don masu kaɗa ƙuri’a su samu sauƙin sha’ani.

Yakubu ya ce, “Daga wannan adadi, an ɗauke rumfuna 232 daga wuraren da ba na gwamnati ba da suka haɗa da fadar sarakuna 145, masallatai 6, majami’u 21, sai kuma wuraren butar gargajiya guda 9.

“Rumfuna 336 da suka rage an sauya musu wuri ne saboda dalilai daban-daban, kamar nisan wuri da wahala kafin isa rumfar, da cinkoso da rikicin ƙabilanci, matsalar tsaro da sauya wurin zama.

“Bayan tuntuɓa da neman shawarwari wajen masu ruwa da tsaki da ma’aikatanmu, an sauya cibiyoyin zaɓe 56,872 zuwa cikakkun rumfunan zaɓe sannan aka ƙara a kan rumfuna 119,974 da ake da su.”

Shugaban na INEC ya ce an sha yunƙurin ƙirƙiro da sabbin rumfunan zaɓe a tsakanin shekaru 25 da suka gabata amma ba a cimma nasara ba sai a wannan karon.

Da wannan cigaban da aka samu, Yakubu ya ce yanzu ya tabbata Nijeriya na da rumfunan zaɓe har guda 176,846 kenan.