14
Jun
Daga AMINA YUSUF ALI Firayiminista Benjamin Netanyahu, kuma firayiminista mafi daɗewa a Ƙasar Isra'ila ya yi adabo da kujerarsa. Hakan ta faru ne bayan majalisa ta sutale shi tare kuma da maye gurbinsa da wani sabon Firayiministan wanda aka zaɓo shi ta hanyar haɗin gwiwa da jam'iyyun siyasar da suke a ƙasar. A halin yanzu tuni sabon Firayiminista Mista Bennet ya ɗare kujerar Netanyahu wanda ya shafe tsawon shekaru goma sha biyu a matsayin firayiminista a ƙasar. Mr. Bennet dai ɗan ɓangaren mulkin ra'ayin riƙau ne na 'yan ƙasa. Kuma ana sa ran zai shafe shekaru biyu yana riƙe da…
