Editor

9513 Posts
Buhari ya naɗa Ilelah shugaban NBC

Buhari ya naɗa Ilelah shugaban NBC

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauke Farfesa Armstrong Idachaba a matsayin shugaban Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC) sannan ya maiye gurbinsa da Balarabe Shehu Ilelah. Kafin sauke shi, an bai wa Idachaba riƙon wannan muƙami tun Fabrairun 2020. Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana naɗin da aka yi wa Ilelah a wata sanarwar manema labarai da ya fitar ran Juma'a. Tare da cewa, Ilelah zai riƙe NBC ne na tsawon shekara biyar. Tun farko, gwamnati ta dakatar da Moddibo Kawu a matsayin shugaban NBC inda ta bai wa…
Read More
Yadda magidanci ke ƙara rura wutar kishi a gidansa

Yadda magidanci ke ƙara rura wutar kishi a gidansa

Daga AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Sannunku da jimirin bibiyar filinku na 'Zamantakewa', wanda yake zuwar muku kowanne mako daga jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata mun yi magana a kan yadda rashin tausayi ya yawaita a tsakanin kishiyoyi, haka a makon da ya gabace shi, shi ma mun yi magana a kan yadda namiji zai ɗauki matakan samar da zaman lafiya a lokacin da zai ƙara aure. A wannan makon kuma, mun zo mu ku da bayani a kan yadda magidanta ke ƙara assasa kishi a tsakanin matansu.…
Read More
Mutum da gaɓɓansa (2)

Mutum da gaɓɓansa (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI 'Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin  ɗan-Adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda ƙirar jikinku ta ke da kuma yadda take aiki.  Mu je kogon ƙugu:Akwai abubuwa masu matuƙar muhimmanci a ciki irinsu mahaifa, bututun wucewar maniyyi, hanyoyin jini, da sauransu. Idan muka ɗauki mahaifa misali, za mu shafe tsawon lokaci muna bayani akanta. Abubuwan da suka shafi mahaifa sun haɗa da yadda take ɗaukar ciki, yadda take samar da jinin haila da na biqi,…
Read More
Masu garkuwa sun canja salo a Sakwkwato

Masu garkuwa sun canja salo a Sakwkwato

*Sun fara yin shigar burtu*Yanzu haka wani attajiri na hannunsu – Hon. Salihi*Ku ci gaba da ba mu muhimman bayanai – ’yan sanda Daga JAMIL GULMA a Sakkwato Masu garkuwa da mutane sun ɓullo da sabon salon ɗaukar mutane a waɗansu sassan Jihar Sakwkwato, inda yanzu suka ɓullo da sabon salon ɗaukar mutane ɗaya-bayan-ɗaya a gidajensu, maimakon kai farmaki a cikin babbar tawaga. Wakilin Manhaja mai kula jihohin Sakwkwato da Kebbi ya ziyarci waɗansu yankuna da suka haɗa da ƙananan hukumomin Illela, Gada da kuma Gwadabawa, inda abin ya fi ƙamari. Shugaban Ƙaramar Hukumar Illela, Hon. Injiniya Aliyu Salihu, ya…
Read More
Rikicin Tiwita: An bar jaki, ana dukan taiki

Rikicin Tiwita: An bar jaki, ana dukan taiki

A makon jiya ne, Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya aike da wanikakkausan saƙo ga waɗanda suka addabi ƙasarsa da fitinar tsaro ta hanyar kashe rayuka, ɓarnata dukiya da kai wa ofisoshin gwamnati hare-hare. Shugaban yana mayar da martani ni kai-tsaye kan ƙungiyar ’yan ta’addar nan ta IPOB mai fafutukar kafa Ƙasar Biyafra, wacce a kwanakin nan ta ke kai hare-haren ta’addanci kan ofisoshin hukumar INEC da na ’yan sanda a yankin Kudu maso Gabas. Shugaba Buhari ya kuma yi furucin ne a Fadar Shugaban Ƙasa lokacin da Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya kai masa…
Read More
Wasu malamai da ɗaliban Nuhu Bamalli Polytechnic sun faɗa hannun miyagu a Kaduna

Wasu malamai da ɗaliban Nuhu Bamalli Polytechnic sun faɗa hannun miyagu a Kaduna

Daga UMAR M. GOMBE 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu malamai da ɗaliban makarantar Nuhu Bamalli da ke Zariya a jihar Kaduna. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna lamarin ya faru ne da daddare a Alhamis da gabata, inda aka yi garkuwa da mutane a ƙalla su takwas. Binciken Manhaja ya gano cewa daga cikin waɗanda aka sace akwai malamai da ɗalibai da iyalin wani malamin makarantar. Bayanai sun ce wani ɗalibi guda ya rasa ransa yayin harin sakamakon harbin bindiga yayin da wani ya samu rauni. Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan,…
Read More
Ranar Dimukuraɗiyya: Gwamnati ta bayyana 14 ga Yuni hutun gama-gari

Ranar Dimukuraɗiyya: Gwamnati ta bayyana 14 ga Yuni hutun gama-gari

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar Litinin, 14 ga Yuni, 2021 a matsayin ranar hutun ma'aikata na gama-gari albarkacin bikin 'Ranar Dimukuraɗiyya' na bana. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a madadin Gwamnatin Tarayya. Tare da yin amfani da wannan dama wajen taya 'yan Nijeriya murnar wannan biki, kana ya yi kira ga 'yan ƙasa da a ci gaba da mara wa gwamnati mai ci baya domin tabbatar da haɗin kai da cigaban ƙasa. Aregbesola ya ce al'umma su yi fatali da duk wani nau'i na barazana ga ƙasa…
Read More
<strong>Matar El-Rufai ga ‘yan Nijeriya: Ku shirya sadaukar da ranku don kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane

Matar El-Rufai ga ‘yan Nijeriya: Ku shirya sadaukar da ranku don kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane

Daga AISHA ASASMatar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia el-Rufai, ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su shirya sadaukar da rayuwarsu domin kawo ƙarshen harkokin ‘yan fashin daji da garkuwa da mutane. Asia ta bada misalin cewa idan ya zamana an yi garkuwa da ita, a shirye take ta rasa ranta muddin hakan shi zai kawo ƙarshen bala’in. Matar gwamnan ta yi waɗannan bayanan ne sa’ilin da take jawabi a wajen wani taron horar da ‘yan’uwanta mata kan sha’anin zaman lafiya da tsaro wanda cibiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Larabar da ta gabata a Kaduna. Daraktan EAI…
Read More
IPOB, Boko Haram da ISWAP dangin juna ne – Soyinka

IPOB, Boko Haram da ISWAP dangin juna ne – Soyinka

Daga AISHA ASAS Fitaccen marubucin nan Farfesa Wole Soyinka, ya bayya IPOB a matsayin ƙani ga Boko Haram. Soyinka ya bayyana haka ne duba da irin ɓarnar da 'yan IPOB ke yi ƙasa musamman ma a yankin Kudu-maso-gabas inda suke karkashe mutane da jami'an tsaro da lalata ofisoshin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da sauransu. Da yake tsokaci kan batun haramta Tiwita a Nijeriya, Farfesan ya ce gwagwarmayar tsagerun IPOB ba halastacciya ba ce. Ya ce, "Ba na goyon bayan waɗanda suka ɓuge da ƙona ofisoshin 'yan sanda tare halaka jami'ansu, lalata ofisoshin zaɓe, yi wa 'yan siyasa kisan gilla…
Read More