Editor

9513 Posts
Za a raba wa ‘yan Nijeriya miliyan ɗaya N5,000 kowanen su a tsawon wata 6

Za a raba wa ‘yan Nijeriya miliyan ɗaya N5,000 kowanen su a tsawon wata 6

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa 'yan Nijeriya miliyan ɗaya da matsalar cutar korona ta shafa za su riƙa karɓar N5,000 a kowane wata har tsawon watanni shida. Ta ce wannan ya na cikin wani sabon shiri ne da ya fara aiki a farkon wannan shekarar da mutum 3,115 a Legas da Abuja, wanda yanzu za a faɗaɗa shi zuwa sauran dukkan jihohi inda mutane za su fara amfana da shi su ma. Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ta bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da aka yi…
Read More
Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen kwamishinonin INEC da zai naɗa

Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen kwamishinonin INEC da zai naɗa

Shugaba Muhammadu Buhari ya tura sunayen mutane shida da ya ke so ya naɗa a matsayin kwamishinonin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ga Majalisar Dattawa domin ta amince da zaɓen su da ya yi. Sun haɗa da Lauretta Onochie, wadda ita ce mai ba shi shawara ta musamman kan soshiyal midiya. A da dai majalisar ta yi fatali da zaɓin da ya yi wa Onochie a zaman ta na ranar 12 ga Oktoba, 2020 domin wasu sanatoci sun ce ba su amince da naɗin nata ba. A zaman majalisar na ranar Laraba ta wannan makon, Sanata Yahaya Abdullahi (ɗan APC daga mazaɓar…
Read More
ASUP ta janye yajin aikin kwanaki 65

ASUP ta janye yajin aikin kwanaki 65

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Fasaha (ASUP), ta janye yajin aikin da ta shafe kwanaki 65 tana yi don bai wa gwamnati damar yin abin da ya kamata. Sanarwar da ASUP ɗin ta fitar a Laraba ta hannun sakatarenta na ƙasa, Comrade Abdullahi Yalwa, ta nuna cewa, "Bayan samun rahoton gwamnati ta soma aiwatar da buƙatun da ke ƙunshe cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyar da gwamnatin tarayya, ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 65 tana yi daga ranar 10 ga Yunin 2021." ASUP ta ce “Dakatarwar ta watanni uku ne kawai domin…
Read More
Dambo ya zama shugaban Hukumar Alhazai ta Zamfara

Dambo ya zama shugaban Hukumar Alhazai ta Zamfara

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya naɗa Abubakar Sarkin-Pawa Dambo a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai na Jihar. Naɗin Alhaji Dambo na daga cikin sabbin naɗe-naɗen da gwamnan ya yi a makon jiya. Sanarwar naɗin ta bayyana ne a Talatar da ta gabata cikin wata sanarwar da ta samu sa hannun muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Kabiru Balarabe. Alhaji Sarkin-Pawa Dambo shi ne shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Alhazai Musulmi na Jihohi. Kazalika, sanarwar ta sake nuna naɗin da aka yi wa Sheikh Abubakar Muhammad Sodangi Gusaua a matsayin Sugaban Hukumar Zakka da Taimako na Jihar.
Read More
Ba za mu bari a sake samun aukuwar yaƙi a ƙasa ba – Dattawan Arewa

Ba za mu bari a sake samun aukuwar yaƙi a ƙasa ba – Dattawan Arewa

Daga BASHIR ISAH Sakamakon tashin-tashinar da ke aukuwa a yankin Kudu-maso-gabas, Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta yi kira ga shugabannin ƙabilar Igbo da su ja kunnen masu tada zaune tsaya a yankin da su maida wuƙaƙensu cikin kube domin hana sake aukuwar yaƙi a ƙasa. Ƙungiyar ta yi wannan furuci ne sa'ilin da take yi wa manema labarai bayani a Litinin da ta gabata a Abuja jim kaɗan bayan kammala wani taronta. NEF ta ce biris da shugabannin Igbon suka yi ba su ce komai ba hakan ya nuna ba su damu da kisan da ake yi wa 'yan Arewa…
Read More
Masu neman a kafa ƙasar Yarabawa wawaye ne, cewar Aregbesola

Masu neman a kafa ƙasar Yarabawa wawaye ne, cewar Aregbesola

Daga UMAR M. GOMBE Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana masu rajin kafa ƙasar Yarabawa da magoya bayansu a matsayin wawaye. Aregbesola ya bayyana haka ne a wajen  taron bikin cikarsa shekara 64 da haihuwa wanda aka gudanar a Zenabab Hotel da ke Ilesha, jihar Osun a Asabar da ta gabata. Ministan ya gargaɗi masu wannan ƙudiri da su yi la'akari da yara ƙanana da mata da tsofoffi da masu fama da nakasa da ake da su a yankin. Ya ce Nijeriya ita ce ƙasar da za ta cire wa yankin Afirka kitse a wuta daga kowane irin…
Read More
Gwamna Bala ya sauke kwamishinoninsa da masu riƙe da muƙaman siyasa

Gwamna Bala ya sauke kwamishinoninsa da masu riƙe da muƙaman siyasa

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala A.Mohammed CON (Ƙauran Bauchi), ya rushe majalisarsa tare da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar. Sanarwar manema labarai da ta fito ta hannun mai bai wa gwamnan shawara kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Mukhtar Gidado, ta nuna Bala ya sauke duka kwamishinoninsa haɗa da wasu masu riƙe da muƙaman siyasa da suka haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar da Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jihar da dukkanin Masu Bai wa Gwamna Shawara (SA) amma ban da wasu mutum huɗu daga ckinsu. Mutum huɗu da suka tsira da muƙamansu su…
Read More
Matawalle ya dawo da wasu tuɓaɓɓun kwamishinonisa, ya dakatar da sarakuna biyu

Matawalle ya dawo da wasu tuɓaɓɓun kwamishinonisa, ya dakatar da sarakuna biyu

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake naɗa wasu daga cikin kwamishinonin da ya sauke a baya da kuma naɗa wasu shugabannin hukumomin gwamnati. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 1 ga watan Yuni, 2021, Gwamna Matawalle ya sauke Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Bala Bello tare da kwamishinoni 23. Bayanin dawo da Kwamishinonin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun Shugaban Ma'aikatan Jihar kuma Muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Kabiru Balarabe, a ran Talata a Gusau, babban birnin jihar. Kwamishinonin da aka sake dawo da su, su ne Alhaji Ibrahim Dosara a matsayin…
Read More