Editor

9513 Posts
Zaɓen 2023: Atiku ya nesanta kansa da wani shirin kamfe

Zaɓen 2023: Atiku ya nesanta kansa da wani shirin kamfe

Daga WAKILINMU Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nesanta kansa da wani shirin yaƙin meman zaɓe inda aka haɗa hotonsa da na tsohon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mr Charles Soludo. A Litinin da ta gabata aka ga fostoci ɗauke da hoton Atiku da Soludo na ta karkaina a birnin Abuja a matsayin 'yan takarar shugaban ƙasa ya zuwa babban zaɓen 2023. Cikin sanarwar da hadiminsa kan sha'anin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar, Atiku ya ce ba shi da masaniya a kan waɗannan hotuna da ake yaɗawa kuma ya nesata kansa da hakan. A cewar sanarwa, "Hankalinmu ya…
Read More
Labari da zafi-zafinsa: Buhari ya kira taron gaggawa kan sha’anin tsaron ƙasa

Labari da zafi-zafinsa: Buhari ya kira taron gaggawa kan sha’anin tsaron ƙasa

Yanzu haka Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na kan ganawa da shugabannin tsaro a wani taron gaggawa da ya kira kan sha'anin tsaron ƙasa. Taron na gudana ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Mahalarta taron sun haɗa da Shugaban Ƙasa MuhammaduMBuhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, Shugaban Tsaro, General Lucky Irabor; Shugaban Sojijin Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu, Shugaban Sojojin Sama, Air Marshal Isiaka Amoo da kuma sabon Shugaban Sojoji, Major General Farouk Yahaya. Sauran su ne, Babban Sufeton 'Yan Sanda, Usman Alkali Baba; Shugaban Cibiyar Tattara Bayanan Sirri (NIA), Ahmed Rufa’i; Darakta Janar na DSS, Yusuf Bichi, da sauran…
Read More
NBC ta buƙaci gidajen rediyo da talabijin su dai amfani da Tiwita

NBC ta buƙaci gidajen rediyo da talabijin su dai amfani da Tiwita

Daga WAKILINMU Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta bai wa tashoshin rediyo da talabijin na faɗin Nijeriya umarnin dakatar da yin amfani da Tiwita. NBC ta ce ɗaukar wannan mataki ya biyo bayan dakatar da Tiwita a Nijeriya da Gwamnantin Taray ta yi kan yadda ta ce kafar ba ta mutunta Nijeriya. Hukumar ta buƙaci tashoshin da su hanzarta katse shafukansu a manhajar Tiwita a matsayin hanyar tattara bayanai da yaɗa harkokinsu. Muƙaddashin Babban Daraktan hukumar, Farfesa Armstrong Idachaba, shi ne ya ba da wannan umarni a Abuja a Litinin da ta gabata.
Read More
Cutar Korona: Ƙarin mutum 49 sun harbu a Nijeriya

Cutar Korona: Ƙarin mutum 49 sun harbu a Nijeriya

Daga UMAR M. GOMBE Cibiyar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta ce a halin yanzu adadin mutane da suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasa ya kai 166,816 bayan da aka samu ƙarin mutum 49 da suka harbu da cutar a tsakanin sa'o'i 24 da suka gabata. NCDC ta ba da wannan bayani ne a shafinta na intanet. Inda ta ce ƙarin da aka samu ya shafi wasu jihohi ne da suka haɗa da Ondo mai mutum 30, Legas na da 15, Kaduna na da 2, sannan Gombe da Adamawa kowacce na da ɗai-ɗai. A cewar NCDC,…
Read More
Sufeto Janar ya haramta wa abubuwan hawa amfani da gilashi mai duhu, shingayen bincike

Sufeto Janar ya haramta wa abubuwan hawa amfani da gilashi mai duhu, shingayen bincike

Daga AISHA ASAS Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Usman Alƙali Baba, ya bada umarnin dakatar da amfani da gilashi mai duhu a motoci a faɗin Nijeriya. A Litinin da ta gabata Baba ya ba da wannan umarni yayin wata ganawa da ya yi da manyan jami'an 'yan sanda daga jihohin ƙasa. Da alama dai ɗaukar matakin haramta wa motoci amfani da gilashi mai duhu na da nasaba da batun yaƙi da matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya. Baya ga haka, Baba ya jaddada cewa haramun ne kafa shingayen bincike a kan hanyoyi a faɗin ƙasa, tare da gargaɗin cewa wajibi…
Read More
Badaƙalar haramta Tiwita: Nijeriya ta gayyaci wakilan Amurka, Birtaniya da Kanada

Badaƙalar haramta Tiwita: Nijeriya ta gayyaci wakilan Amurka, Birtaniya da Kanada

Kimanin sa'o'i 48 da sukar matakin haramta Tiwita da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ɗauka, gwamnatin ta gayyaci wakilan ƙasashen Amurka da Birtaniya da Kanada a Nijeriya da su bayyana a gabanta. Sanarwar gayyatar ta fito ne ta hannun Kimiebi Ebienfa na sashen Sanya Ido Kan Suka da Sadarwa na Ma'aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya. A cewar jami'in, "Biyo bayan haramta Tiwita da Gwamnatin Tarayya ta yi da kuma bayanan da wasu jakadu a Nijeriya suka yi a kan batun dakatarwar, an buƙaci in sanar cewa Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya gayyaci jakadun da lamarin ya shafa zuwa wajen taro…
Read More
Yadda wasu matasan Kano 17 suka rasu a haɗarin mota, Ganduje ya miƙa ta’aziyyarsa

Yadda wasu matasan Kano 17 suka rasu a haɗarin mota, Ganduje ya miƙa ta’aziyyarsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wasu matasa su 17 daga jihar Kano sun rasu sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da su a babbar hanyar Zariya zuwa Kano yayin da suke komawa Kano daga Kaduna bayan halartar ɗaurin auren abokinsu. Wannan mummunan al'amari ya auku ne da yammacin Asabar da ta gabata. Bayanai sun tabbatar cewa wasu daga cikin matasan a nan take suka cika, yayin da wasunsu sai da aka dangana da asibiti kafin rai ya yi halinsa. Majiyar Manhaja ta ce takwas daga cikin marigayan sun fito ne daga yankin Sani Mainagge a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar.…
Read More
Kudancin Nijeriya zai daina ganin albasa daga wannan Litinin har sai an biya mana buƙatunmu – Ƙungiya

Kudancin Nijeriya zai daina ganin albasa daga wannan Litinin har sai an biya mana buƙatunmu – Ƙungiya

Daga UMAR M. GOMBE Ƙungiyar Manoman da 'Yan Kasuwar Albasa ta Nijeriya (OPMAN), ta ce za ta dakatar da kai albasa ya zuwa Kudancin ƙasa daga wannan Litinin har sai gwamnatin trayya da na jihohi sun biya mata buƙatunta. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Malam Aliyu Isa ne ya bayyana haka a Sakkwato a Asabar da ta gabata sa'ilin da yake yi wa manema labarai bayanin matsayinsu. Daga cikin jerin buƙatun da ƙungiyar ke neman a biya mata su har da biyan cikakken diyya ga mamabobinta waɗanda rikicin addini da na ƙabilanci ya shafa a yankin Kudu. Haka nan, ta buƙaci…
Read More
Badaƙalar haramta Tiwita a Nijeriya: Sulhu shi ne mafita – Ƙasashen Turai

Badaƙalar haramta Tiwita a Nijeriya: Sulhu shi ne mafita – Ƙasashen Turai

Daga BASHIR ISAH Gwamnatocin Birtaniya (UK), Kanada, Jamhuriyar Ireland, Norway da na Tarayyar Turai (EU) sun yi kira da a tattauna don warware matsalar da ke tsakanin Nijeriya da Tiwita A wani bayanin haɗin gwiwa da suka fitar a Asabar da ta gabata a Abuja aka kuma raba wa manema labarai, ƙasashen sun ce suna goyon bayan 'yancin faɗin albarkacin baki da kuma damar samun bayanai a matsayin ginshiƙin dimukuraɗiyyar Nijeriya kamar dai yadda lamarin yake a sauran ƙasashen duniya, wannan 'yancin kuwa ya shafi amfani da intanet da kishiyar haka. A cewarsu, "Ɗaukar matakin dakatar da wani al'amari ba…
Read More