06
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗaruruwan 'yan jam'iyar APC da magoya bayan xan majalisar tarayya mai wakiltar al'ummar ƙananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da 'Yankwashi, Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ne suka gudanar da zanga-zangar ƙin amincewa da dakatar da wakilin nasu da jam'iyyar APC ta yi. Masu zanga-zangar sun zargi gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar da ɗaukar matakin ɗauki ɗora da ya yi wa mafi yawancin al'ummar ƙananan hukumomin jihar, inda ya zaɓi mutanen da za su yi wa jam'iyar APC takarar shugabancin ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomin ba. Matasan wanda suke…
