Editor

9513 Posts
Kwastam ta kama haramtattun kayayyaki na bilyan N3.1 a Legas

Kwastam ta kama haramtattun kayayyaki na bilyan N3.1 a Legas

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri na shiyyar Zone A a birnin Legas, ta kama durom 42 maƙare da tokar bindiga (calcium carbide) wanda aka shigo da su cikin ƙasa a sace daga ƙasar Benin. Masana sun yi gargaɗin cewa lamarin fa ba zai yi daɗi ba idan irin wannan makamashi ya faɗa a hannu ɓata-gari. Hukumar Kwastam ta ce makamashin abu ne da za a iya amfani da shi wajen haɗa abubuwa masu fashewa masu ƙarfin tarwatsa gine-gine. Shugaban riƙo na hukumar a Zone A, Compt. Usman Yahaya, ya shaida wa manema labarai cewa baya ga tokar bindigar…
Read More
Mutum 164,488 aka tabbatar sun kamu da korona a Nijeriya -NCDC

Mutum 164,488 aka tabbatar sun kamu da korona a Nijeriya -NCDC

Daga AISHA ASAS Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta bada sanarwar samun ƙarin mutum 65 da suka harbu da cutar korona cikin sa'o'i 24 a faɗin ƙasa. NCDC ta ce ƙarin da aka samu ya shafi wasu jihohi su 11 ne ciki har da jihar Lagos-41, Kaduna-6, Kano-3, Rivers-3, Plateau-3 da kuma Akwa Ibom-2. Sauran su ne; Imo-2 da Oyo-2 da Edo-1 da Bauchi-1 sai kuma jihar Osun mai mutum 1. A cewar NCDC, jimillar mutanen da aka tabbatar sun harbu da annobar a faɗin ƙasa ya kama 164,488, yayin da mutum154,441 sun warke, sannan mutum2,061 sun…
Read More
Majalisa ta amince wa gwamnati kinkimo bashin bilyan $1.5 da milyan €995

Majalisa ta amince wa gwamnati kinkimo bashin bilyan $1.5 da milyan €995

Daga FATUHU MUSTAPHA Bayanan da Manhaja ta samu ba da jimawa ba sun nuna Majalisar Dattawa ta amince wa Gwamnatin Tarayya da jihohi su kinkimo bashin Dala bilyan $1.5 da Yiro milyan €995 daga ƙetare. Majalisar ta yi na'am da batun ciyo bashin ne bayan da ta yi nazarin rahoton da kwamitinta kan sha'anin rance ya gabatar mata. Shugaban Kwamitin, Clifford Ordia, ya sanar da majalisar kwamitinsa ya gamsu da batun neman rancen kuma yana bada shawarar ita ma ta amince da batun. Bashin Yiro milyan €995 da gwamnatin ta nema za ta yi amfani da kuɗaɗen ne wajen bunƙasa…
Read More
Jerin sunayen ɗalibai 17 da aka sace a jami’ar Greenfield

Jerin sunayen ɗalibai 17 da aka sace a jami’ar Greenfield

Daga AISHA ASAS An saki sunayen ɗalibai su 17 da aka yi garkuwa da su a Jami'ar Greenfield mai nisan kilomaita 34 da ke babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja. Wani ma'akacin jami'ar da ya buƙaci a sakaya sunansa, shi ne ya bayyana sunayen ɗaliban da lamarin ya shafa. Ma'akacin ya faɗa cewa ɗaya daga cikin masu gadin makarantar ya rasa ransa yayin harin wanda ya auku ranar Talata, 20 ga Afrilun 2021. Ga dai jerin sunayen ɗaliban da 'yan bindigar suka sace wanda baki ɗayansu maza ne babu mace ko guda: 1 Abraham Akinje 2 Fortune Alhassan 3 Miracle John…
Read More
Naɗa ɗan marigayi Deby matsayin shugaban Chadi ya bar baya da ƙura

Naɗa ɗan marigayi Deby matsayin shugaban Chadi ya bar baya da ƙura

Daga UMAR M. GOMBE 'Yan hamayya a siyasar ƙasar Chadi sun ƙi amincewa da naɗin da sojojin ƙasar suka yi wa ɗan tsohon shugaban ƙasar, marigayi Idriss Deby a matsayin sabon shugaban riƙo na ƙasar. Sojoji sun naɗa Muhammat Kaka Idriss Deby a matsayin shugaban riƙo na ƙasar ne biyo bayan rasuwar mahaifinsa a Talatar da ta gabata. Sai dai da alama naɗin bai yi wa wasu 'yan ƙasar daɗi ba inda wasu 'yan siyasa masu hamayya suka fito suka nuna rashin amincewarsu game da naɗin tare da cewa ƙasar ba ta mulkin kama-karya ba ce. Kafin wannan lokaci, General…
Read More
Saudiyya ta tallafa wa ‘yan gudun hijira da abinci a Nijeriya

Saudiyya ta tallafa wa ‘yan gudun hijira da abinci a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Ƙasar Saudiyya ta bada tallafin kayan abinci na kuɗi Dalal bilyan $1.1 domin raba wa 'yan gudun hijira a jihar Barno da Yobe da Zamfara. Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da rabon kayayyakin a Talatar da ta gabata a birnin Maiduguri, Mataimakin Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Ibraheem Alghamedi, ya ce Sarki Salman ya ɗauki wannan matakin ne domin ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu. Jakadan ya ce, “Ina mai amfani da wannan dama wajen jaddada kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Masarautar Saudiyya da Tarayyar Nijeriya. “Haƙika Saudiyya ta ƙuduri aniyar bunƙasawa da kuma…
Read More
Babu wata aniyar ƙara kuɗin fetur, cewar NNPC

Babu wata aniyar ƙara kuɗin fetur, cewar NNPC

Daga FATUHU MUSTAPHA Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya jaddada cewa ba shi da wata aniya ta ƙara kuɗin mai nan kusa. Shugaban kamfanin, Mele Kyari, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya bayar. Kyari ya bada sanarwar haka ne yayin ganawar da ya yi da manema labarai jim kaɗan bayan tattaunawar sirri da suka yi tare da Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Ƙasa (NARTO) da takwararta ta direbobi masu dakon mai (PTD), Litinin da ta gabata a Anuja. NNPC ya nemi ganawa da ƙungiyoyin ne bayan da mambobin PTD suka bai wa NARTO wa'adin mako…
Read More
Tsohon gwamnan Zamfara, Yari ya faɗa komar EFCC

Tsohon gwamnan Zamfara, Yari ya faɗa komar EFCC

Daga WAKILINMU A Talatar da ta gabata Hukumar Yaƙi da Zambar Kuɗaɗe da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa ((EFCC) ta gayyaci tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, don ya amsa mata tambayoyi kan wasu tarin zarge-zargen rashawa da aka yi masa. Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa a ofishin hukumar da ke Sakkwato aka tsare tsohon gwamnan na tsawon sa'o'i takwas. Tun farko sai da EFCC ta aika wa Yari wasiƙar gayyata mai ɗauke da kwanan wata 6, Afrilu, 2021 a kan tana da buƙatar ganinsa a ofishinta na Sakkwato a ranar 8 ga Afrilu domin ya amsa mata…
Read More
Zaɓen Ondo: Kotu ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar

Zaɓen Ondo: Kotu ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Ondo, ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar PDP ta jihar da ɗan takararta Eyitayo Jegede, suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu SAN na APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gudana ranar 10 ga Oktoban 2020. Kotu ta kori ƙarar ne saboda rashin ƙarfin iko da cancanta. Da yake gabatar da shari'ar ta bidiyo, shugaban kotun, Alƙali Umar Abubakar, ya ce batun da aka shigar da ƙara a kansa abu ne da jam'iyyar za ta sasanta ta cikin gida ba tare an kai kotu ba, wanda a…
Read More