20
Apr
Daga UMAR M. GOMBE Rahotanni daga ƙasar Chadi sun tabbatar da rasuwar Shugaban Ƙasar, Idris Deby Itno, mai shekaru 68. Bayanan sojojin ƙasar sun nuna marigayin ya kwanta dama ne sakamakon raunukan da ya samu a karawar da ya jagoranci dakarunsu wajen fatattakar ‘yan tawayen FACT na ƙasar. Bayanan sosjojin sun sake nuna cewa, marigayi Deby ya rasu ne jim kaɗan bayan sanar da nasarar da ya samu a babban zaɓen ƙasar da aka gudanar a ranar 11, Afrilu, 2021. A cewar Hukumar Zaɓen Chadi, marigayin ya lashe zaɓen ne da kashi 79.32 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa. Sanarwa…
