Editor

9513 Posts
Rikicin ƙungiyar asiri ya ci mutum shida a Ekiti

Rikicin ƙungiyar asiri ya ci mutum shida a Ekiti

Daga BASHIR ISAH Bayanai daga jihar Ekiti sun tabbatar da mutuwar wasu mutum shida sakamakon rikicin da ya ɓarke a tsakanin ƙungiyoyin asiri a yankin Ikere na jihar. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar wa manema labarai da faruwar haka. Jami'in ya ce sun gano gawarwakin mutum shida da aka kashe sakamakon rikicin wanda ya auku da sanyin safiyar Lahadi. Wata majiya daga yankin da abin ya faru ta ce an ji ƙarar harbe-harben bindigogi yayin rikicin lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin gudun neman mafaka don tsira da rayuwarsu. Abutu ya ce waɗanda…
Read More
Boko Haram: Ministan Tsaro ya yi wa Jihar Borno tsinke

Boko Haram: Ministan Tsaro ya yi wa Jihar Borno tsinke

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Borno A ci gaba da kai ziyarar ƙarfafa gwiwa ga sojojin da ke aikin samar da tsaro a jihar Borno, Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (ritaya), tare da Shugabanin Rundunonin Sojojin Nijeriya, sun yi wa birnin Maiduguri tsinke domin duba halin da ake ciki a yankin, a ranar Lahadi. Kwamandan shalkwatar Rundunar Lafiya Dole da ke Maiduguri, Manjo Janar Farouq Yahaya, shi ne ya yi wa tawagar ministan marhabin, tare da yaba wa ƙoƙarin ministan da shugabanin sojojin dangane da ingantattun matakan da ministan tsaro tare da takwarorinsa ke ɗauka wajen ƙarfafa gwiwar rundunonin da ke…
Read More
Katsina: Za a tura karnuka don su bada tsaro a makarantu

Katsina: Za a tura karnuka don su bada tsaro a makarantu

Daga FATUHU MUSTAPHA A matsayin wani mataki na ƙokarin daƙile matsalar tsaro musamman ma a makarantun kwana, gwamnatin Jihar Katina ta amince da batun tura karnuka na musamman ya zuwa makarantun kwana domin su yi aiki tare da jami'an tsaro wajen bai wa makarantun kariya. Tun farko, sai da gwamnatin jihar ta ɗauki matakin tura jami'an tsaro biyar-biyar zuwa makarantun kwana tare da ɗaga katangar kariya domin samar da tsaro a makarantun da lamarin ya shafa a jihar. Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnati ta ɗauki matakin yin amfani da karnukan ne…
Read More
Ba mu yarda da ci gaban shugabanci mara kan gado ba – PDP

Ba mu yarda da ci gaban shugabanci mara kan gado ba – PDP

Daga AISHA ASAS Babbar jam'iyyar bamayya a Nijeriya, PDP, ta ce duk da dai tana yi wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari barka da dawowa daga jinyar da ya je a Turai, amma ba ta yi na'am da zancen shugaban ba na cewa 'yan Nijeriya su sa ran ganin "Ci gaba." A bayanin da ta fitar, PDP ta ce tana ra'ayin ko ma dai da wata manufa shugaban ya furta kalmar 'Ci gaba' ɗin, kada hakan ya yi nasaba da barin mulkinsa ya zuwa 29, Mayu, 2023. Ta ci gaba da cewa hasali ma 'yan Nijeriya ba su yarda da duk…
Read More
Taraba: Shugaban ƙaramar hukuma ya tsallake rijiya da baya

Taraba: Shugaban ƙaramar hukuma ya tsallake rijiya da baya

Daga UMAR M. GOMBE 'Yan bindiga sun kai wa Shugaban Karamar Hukumar Takum, Shiba Tikari, a jihar Taraba hari inda ya samu ya tsallake rijiya da baya. Harin wanda ya auku Asabar da ta gabata a ƙauyen Dogo-Gawa, ya yi sanadiyar rasa ran ɗan sandan da ke bai wa shugaban tsaro sakamakon wuta da tsegerun suka buɗe wa motocinsu. Manhaja ta gano cewa ɗan sandan da ya rasa ransa a harin na ɗaya daga cikin 'yan sandan kwantar da tarzoma su 67 da aka girke a yankin ƙaramar hukumar. A wata sabuwa, bayanai sun nuna 'yan sandan Ƙaramar Hukumar Wukari…
Read More
Adamawa: Buhari ya jajanta wa al’ummar Kwapre bisa harin ta’addanci

Adamawa: Buhari ya jajanta wa al’ummar Kwapre bisa harin ta’addanci

Daga WAKILINMU Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa tare miƙa ta'aziyyarsa ga al'ummar Kwapre da ke yankin ƙaramar hukumar Hong, jihar Adamawa, dangane da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai musu kwanan nan. Buhari a bisa wakilicin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya miƙa ta'aziyyarsa ne yayin ziyarar da sakataren ya kai a yankin da lamarin ya shafa. A cewar Boss Mustapha, "Na zo Kwapre ne a bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari domin ganin abin da ya auku. Shugaban ya jajanta muku kan abin da ya faru." Ya ce, "Na gani da idona irin ɓarnar da aka tafka…
Read More
Duk macen da ta dogara da miji, za ta kwashi haushi – Fatima Kaita

Duk macen da ta dogara da miji, za ta kwashi haushi – Fatima Kaita

*Yawancin abinda ke jawo wa 'ya'ya mata shiga harkar lalacewa na da alaƙa da rashin sana'a - Fatima Daga AISHA ASAS Fatima Kaita cikakkiyar 'yar boko kuma 'yar kasuwa sannan 'yar gwagwarmayar siyasa, a hirar ta da jaridar Manhaja ta taɓo abubuwa da dama da su ka shafi muhimmancin sana'a ga 'ya mace ta yadda ba sai ta rage murya a wajen maigida ko 'yan'uwa ba. An dai ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi, don haka ga yadda hirar ta kasance: Ko za ki faxa wa masu karatu sunan ki da kuma ɗan taƙaitaccen tarihin ki?Assalamu alaikum,…
Read More
Na yi da-na-sanin rera waƙar Abubakar Ladan, Cewar Aminu ALA

Na yi da-na-sanin rera waƙar Abubakar Ladan, Cewar Aminu ALA

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Ɗaukar waƙar wani mawaƙi rubutacciya a rera ta ba wani sabon abu ba ne a fagen waƙa a duniya. Don haka ne ma ake samun wasu mawaƙan ko dai su saya ko su nemi izinin rera wata rubutacciyar waƙa da wani mawaƙi ya zauna ya tsara. Irin wannan salo ne fitaccen Mawaƙi Alhaji (Dakta) Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya yi amfani da waƙar 'Afrika' ta Marigayi Malam Abubakar Ladan Zariya, inda ya rera ta a salo na zamani tare da kayan kiɗa na zamani da nufin zamanantar da waƙar. To, sai dai bayan fitar waƙar…
Read More
Game da rikicin ganin jinjirin wata a Nijeriya

Game da rikicin ganin jinjirin wata a Nijeriya

Daga ALIYU SAMBA A kusan kowacce shekara ana samun taƙaddama tsakanin Musulmi kan bayyanar jinjirin watan Ramadana da kuma watan Shawwal. Musulmai a duniya suna saɓawa wajen ƙirgen azumi. A sanda wasu su ke ɗaya, wasu su na biyu, wasu kuma su na uku ga watan Ramadan. Akwai buƙatar mu san cewa, dukkanmu na rayuwa ne a duniya guda (Earth), wacca take da wata guda ɗaya a sama, rashin rungumar ilimin kimiyya ya taimaka wajen faɗaɗar saɓanin nan a tsakanin mutane, domin ita ce hanya mai sauƙi da za a gane bayyanar hasken wata a sarari ko fakuwarsa. Wasu na…
Read More