24
Apr
Daga WAKILINMU Sahihan bayanai daga jihar Imo sun tabbatar da wasu mutum biyu sun rasa rayukansu yayin harin da 'yan bindiga suka kai wa gidan Gwamna Uzodinma da ke Omuma a yankin karamar hukumar Oru ta Yamma a jihar. Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da gwamnan ya sanar da manema labarai cewa an yi nasarar kama wasu mutum 50 da ake zargi suna da hannu a hare-haren da aka kai a Imo lokacin bikin Easter da ya gabata, tare da cewa wasu 'yan siyasa ne suka ɗauki nauyinsu. Sai dai Manhaja ba ta samu tabbacin faruwar hakan ba…
