Editor

9513 Posts
NBC ta dakatar da tashar Channels saboda tattaunawa da jagoran IPOB

NBC ta dakatar da tashar Channels saboda tattaunawa da jagoran IPOB

Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta dakatar da gidan talabijin na Channels har da ƙarin tarar milyan N5 sabida take dokar aiki. A wata wasiƙa da ta aike wa Manejin Daraktan tashar wadda ta sami sa hannun Muƙaddashin Babban Daraktan Hukumar, Prof. Armstrong Idachaba, NBC ta nuna ta ɗaiki wannan mataki ne ta kafa hujja da wani shirin kai-tsaye da tashar ta gabatar a ranar Lahadi, 25, Afrilu, 2021 da misalin ƙarfe bakwai na dare, inda ta kama tashar da laifin bai wa jagoran tsegerun IPOB damar faɗin maganganun da ka iya haddasa fitina ba…
Read More
Zulum ya naɗa Indimi da wasu matsayin majalisar gudanarwa ta jami’ar Barno

Zulum ya naɗa Indimi da wasu matsayin majalisar gudanarwa ta jami’ar Barno

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnan jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya naɗa Majalisar Gudanarwa da za ta sanya ido kan gudanar da harkokin Jami'ar Jihar Barno. Zulum ya naɗa majalisar ne a ranar Litinin a fadar gwamnatin jihar, wadda za ta gudana ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mohammed Indimi. Sauran mambobin majalisar sun haɗa da Farfesa Abubakar Mustapha, Farfesa Bankole Ogumbameru, Farfesa Shettima Umara Bulakarima, Alhaji Lawan Buba, wakilin majalisar dattawa na jami'ar da dai sauransu, yayin da rajistaran jami'ar zai kasance riƙe da muƙamin sakataren majalisar. Gwamnan ya yi kira ga 'yan majalisar da su samar da tsari mai inganci wajen…
Read More
Za a yi jana’izar mahaifiyar Sarkin Kano yau

Za a yi jana’izar mahaifiyar Sarkin Kano yau

Daga BASHIR ISAH Masarautar Kano ta bada sanarwar za a yi jana'izar mahaifiyar Sarkin Kano, marigayiya Hajiya Maryam (Mai Babban Ɗakin Kano), a yau Litinin. Masarautar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun Madakin Kano, Yusuf N. Ibrahim Chigari da aka fitar a jiya Lahadi. Sanarwar ta ce, "A bisa babban rashi da muka yi na rasuwar Mai Babban Ɗakin Kano, wanda ya faru Asabar 12 ga Ramadan 1442 (24 ga Afrilu, 2021)a ƙasar Masar, Masarautar Kano da Masarautar Bichi, na sanar da shirinjana'iza kamar haka: Ana tsammanin isowar mamaciya filin jirgin saman Malam Aminu…
Read More
An kama hanyar bai wa wasu marayu ilimi mai nagarta a Gombe

An kama hanyar bai wa wasu marayu ilimi mai nagarta a Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI, Gombe Shugaban gidauniyar zaka da waƙafi na jihar Gombe, Abdullahi Abubakar Lamiɗo, ya yi alƙawarin cewa gidauniyarsu da gidan Marayu na AL-GUH (Al- gidan Umma Hajara) za su haɗa kai dan ganin an bai wa marayu ilimi mai inganci dan su samu abun dogaro a rayuwa. Abudullahi Lamiɗo, ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar gidauniyar suka ziyarci gidan marayun a ranar Lahadi dan ba su tallafin kayan abinci cikin irin tsarin su na tallafa wa gajiyayyu da marayu a watan Ramadan. Ya koka kan irin yadda Musulunci yake da tsari ya kuma bayyana falalar…
Read More
NGE ta shirya gudanar da babban taronta a Kano

NGE ta shirya gudanar da babban taronta a Kano

Daga FATUHU MUSTAPHA Kungiyar Editoci ta Nijeriya (NGE) ƙarƙashin jagorancin Comrade Mustapha Isah, ta sanar da cewa ta yanke shawarar gudanar da babban taronta na ƙasa a birnin Kanon Dabo. Comrade Mustapha Isah, ya ce ra'ayin gudanar da babban taron ƙungiyar a Kano ya zo a daidai lokacin da ya fi dacewa. Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala naɗa kwamitin tsare-tsare, shugaban ƙungiyar ya ce Kano wuri ne mai zaman lafiya wanda mambobin ƙungiyar ba za su samu wata fargaba ko tsoron zuwa ba daga ko'ina don halartar taron. Ya ce kwamitin da aka kafa mai…
Read More
Gwamnatin Kaduna ta tsawaita wa’adin tashi da ta bai wa dillalan motoci

Gwamnatin Kaduna ta tsawaita wa’adin tashi da ta bai wa dillalan motoci

Daga WAKILINMU Hukumar Tsarawa da Bunƙasa Birane ta Jihar Kaduna ta amince da roƙon Ƙungiyar Masu Sayar da Motoci ta Jihar Kaduna inda ta buƙaci a ƙara wa mambobinta lokaci game da tashi daga inda suke da aka buƙace su da yi. A wata takardar sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 21, Afrilu, 2021 wadda Stephen Baji ya sanya wa hannu a madadin Darakta Janar na hukumar, ta nuna an ƙara wa waɗanda lamarin ya shafa wa'adi zuwa mako guda bayan watan Ramadan, wato 19 ga Mayu, 2021. Da wannan, hukumar ta ce ana buƙatar mambobin ƙungiyar su bi umarni…
Read More
Har yanzu ‘yan Boko Haram na riƙe da Geidam

Har yanzu ‘yan Boko Haram na riƙe da Geidam

Daga UMAR M. GOMBE Saɓanin bayanin da aka yi ta yaɗawa cewa an kashe mayaƙan Boko Haram tare da ƙwace garin Geidam daga hannunsu, wasu mazauna garin da suka buƙaci a sakaya sunansu sun tabbatar wa jaridar Neptune Prime lamarin ba haka yake ba. Sun ce har yanzu 'yan bindigar na riƙe da garin kuma sai ƙaruwar suke ta yi. Wani mazaunin garin da Neptune Prime ta samu zantawa da shi da sanyin safiyar Lahadi ya ce, "Na gan su da idanuna, waɗanda suka shigo shekaranjiya suna nan, sannan sun ƙaru daga daren da ya gabata zuwa wannan safiya." Wani…
Read More
‘Yar shekara 50 a sakandare: ‘Ba a makara da neman ilimi’, cewar Atiku Abubakar

‘Yar shekara 50 a sakandare: ‘Ba a makara da neman ilimi’, cewar Atiku Abubakar

Daga BASHIR ISAH Shade Ajayi, 'yar shekara 50, ita ce ɗaliba mai mafi yawan shekaru a tsakanin ɗaliban makarantun jihar Kwara. A halin da ake ciki, Shade Ajayi ɗaliba ce a Ilorin Grammar School, da ke Ilorin babban birnin Jihar. Lamarin wannan gyatuma ya ɗauki hankali 'yan ƙasa da dama ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ganin yadda yawan shekaru bai hana ta zuwa makaranta neman ilimi don ingata rayuwarta ba. Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na twita game da Shade, Alhaji Atiku Anubakar ya ce, "Tana tunatar da mu cewa ba a makara da…
Read More
Hajjin 2021: NDLEA ta buƙaci a hori maniyyata su guji mu’amala da miyagun ƙwayoyi

Hajjin 2021: NDLEA ta buƙaci a hori maniyyata su guji mu’amala da miyagun ƙwayoyi

Daga AISHA ASAS Hukumar Yaƙi da Fatauci da Tu'ammali da Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta yi kira ga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da ta wayar da kan maniyyata da ke shirin tafiya ƙasa mai tsarki da su guji yin mu'amala da muggan ƙwayoyi yayin aikin Hajjin 2021. Kwamandan NDLEA na jihar Neja, Haruna Kwetishe ne ya yi wannan kira yayin ziyarar da ya kai wa hukumar kula da walwalar maniyyata ta jihar da ke Minna, babban birnin jihar. Haka nan, Kwamandan ya yi kira ga jami'an gwamnati da su tabbatar da cewa waɗanda aka amince wa zuwa ƙasa…
Read More