Shirye-shiryen Zuwan Ramadan

Daga IMAM YAHYA ALYOLAWI

Kalmar Ramaḍan an tsago ta ne daga Kalmar “Ramad”, wadda ke nufin abin da ya duku da zafin rana. Larabawa kan kira tumakin da suka sha zafin rana a wajen kiwo da suna ‘ramidah’, zafin ranar da har kan yi sanadin lalacewar hantar dabbobin saboda tsananin zafi.

Watan Ramadan ya samu sunansa ‘Ramadan’ ne saboda ƙona zunuban bayin Allah na gaskiya da yakan yi. Imām Qurtubi ya ce: ”Ramadan ya samu sunansa ne saboda ƙona kurakuran bayin Allah nagartattu da yake yi.” Abu Huraira (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) na cewa: “Duk wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da neman yardar Allah, za a gafarta masa laifukansa da suka gabata.” (Al-Bukhari)

Muhimmancin Ramadan

Ramadan shi ne wata na 9 a kalandar Musulunci, wata ne na rahma, shi ne watan da aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shi ne wata mafifici a cikin watannin shekara kuma watan da akan nunka sakamakon ayyukan bayi, wata mai cike da gafara.

Azumin Ramadan ɗaya ne daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar. Magabata sun kasance masu maida hankali sosai game da raya watan Ramdan da ibada. Bayan an fita Ramadan, sukan kasance masu fatan da burin Allah Ya tsawaita rayuwarsu domin su shaida Ramadan na gaba saboda sake samun damar gabatar da ibadar azumi a watan.

Ga wasu ayoyi da hadisai da suka yi magana game da Ramadan:

  • Ramadan tamkar makaranta ce ta nuna tausayi. Allah Maɗaukaki Ya ce, “Ya ku wadanda kuka yi imani, an sanya muku yin azumi kamar yadda aka sanya ma waɗanda suka gabace ku don ku zama mutanen kirki” (Q 2:183). Haka nan Ya ce: “Wanda ya fi girma a cikinku a gaban Allah shi ne wanda ya fi tsoron Allah. “(Q 49:13)
  • Azumi kariya ne daga barin aikata zunubi da munanan ayyuka. An ruwaito Annabi (SAW) na cewa: “Azumi garkuwa ne.” (Bukhari da Muslim)
  • Azumin Ramadan shi ne na huɗu daga jerin shika-shikan Musulunci: An karɓo daga Ibn Umar ɗan Umar bin Al-Khattab (R.A) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) na cewa, “An gina Musulunci ne a kan abubuwa guda biyar; shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah kuma Muhammad Manzon Allah, tsayar da sallah, bayar da zakka, zuwa aikin Hajji da kuma azumin Ramadan.” (Bukhari da Muslim)
  • Ramadan wata ne na Alƙur’ani: A cewar Allah (SWT), “A cikin watan Ramadan aka saukar da Alƙur’ani domin shiriya ga mutane…” Q2:186. Don haka a lizimci karatun Alƙur’ani a cikin wannan wata mai alfarma gwargwadon iko.
  • A watan Ramadan ake samun Daren Lailatul-Kadr, daren da ya fi alheri bisa ga watanni dubu, (wato shekaru 83 da wata 6). Haƙiƙa Mun saukar da Alƙur’ani ne a cikin Lailatul-Ƙadr? Daren Lailatul-Kadr ya fi alheri fiye da watanni dubu. Mala’iku da Ruhi na sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu. Aminci ne a cikinsa har zuwa fitowar alfijir.” (Q97.1-5)
  • Raya dararen Ramdan da ibada hanya ce ta samun tarin lada da kuma shafewar zunubai.
  • Yawaita bada sadaka a cikin watan Ramadan abin so ne: Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Annabi (S.A.W) shi ne kan gaba wajen kyautatawa, yakan ƙarfafa kyautatawarsa musamman ma cikin Ramadan…” [Bukhari]
  • Allah kan buɗe ƙofofin Aljanna a watan Ramadan sannan Ya kulle ƙofofin wuta tare da ɗaure duka shaiɗanu. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ana ɗaure duka shaiɗanu a ranar farko na Ramadan. Ana kulle ƙofofin wuta, ko ƙofa guda ba za a bari a bude ba, sannan mai kira zai yi kira da cewa: ‘Ya ku masu neman alheri ku yiwo gaba, masu neman sharri kuwa su yi baya, Allah na ‘yanta bayinSa da dama daga barin shiga wuta a cikin kowane dare (na Ramadan)’ [at-Tirmithi].
  • Azumi kariya ne ga barin shiga wuta: Abu Said al-Khudri ya ruwaito Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Babu wata rana da bawa zai yi azumi saboda Allah face sai Allah ya nesanta tsakaninsa da wuta na tsawon shekara saba’in.” [Bukhari da Muslim]. Haka ma Abu Sa`eed al-Khudri ya ruwaito Manzon Allah (SAW) ya ce: “Azumi garkuwa ne wanda bawa kan kare kansa da ita daga wuta.” [Ahmad]
  • Yin azumin Ramadan daidai yake da azumtar watanni goma: Abu Ayyub (R.A) ya ruwaito Manzon Allah (SAW) na cewa: “Duk wanda ya azumci Ramadan sannan ya bi shi da azumi guda shida a watan Shawwal, tamkar ya yi azumin shekara ne baki ɗayanta.” [Muslim da Abu Dawud]. Annabi ( SAW) ya bayyana haka ne a lokacin da ya ce: “Duk wanda ya yi azumi na kwana shida bayan Idil Fitr (karamar sallah), ya cika shekara: (duk wanda ya aikata aiki mai kyau zai samu lada goma kwatankwacinsa).” Malamai sun yi ƙarin haske da cewa: “Allah na bada lada goma ga kowne kyakkyawan aiki, don haka azumin wata tamkar azumin watanni goma ne, sannan azumin kwana shida ya cikasa shekara kenan.” Allah Shi ne masani.
  • Azumin Ramadan hanya ce ta samun shafewar laifuffuka muddin mutum ya guji aikata manyan laifuka.
  • Duk wanda ya tsaya sallah a cikin Ramadan da daddare, yana mai imani da neman yardar Allah, za a rubuta masa tamkar wanda ya raya dare da ibada baki dayansa.
  • Yin Umura a watan Ramadan daidai yake da aikin Hajji.

Shirin Tarbar Ramadan

  1. Tuba ta gaskiya: Ana buƙatar mutum ya zama mai tuba a kowane lokaci ta yadda da zuwan Ramadan za a samu yin ibada da zuciya mai tsarki. Allah Madaukaki Ya ce a cikin Alƙur’ani: “Ya ku wadanda kuka yi imani ku tuba zuwa gare Shi baki ɗayanku, ko kun samu nasara.” An ruwaito daga Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Ya jama’a! Ku tuba zuwa ga Allah ku nemi gafararSa. Ni ina neman gafarSa sau ɗari a yini.” A zamo masu kyautata niya da kuma koyi da Annabi (SAW).
  2. Yawaitar addu’ar neman Allah Ya karbi dukkan ibadun da aka gabatar da ma wadanda za a gabatar a gaba.
  3. Hanzarta rama azumin baya da ake bin mutum. An samo daga Abu Salama (RA) cewa, “Na ji Aisha (RA) na cewa: “Wasu lokuta nakan sha azumin Ramadan amma ba zan samu rama su ba sai a watan Sha’aban.”
  4. Neman sani game da abin da ya shafi alfarmar watan Ramadan da kuma azumin da ake yi a cikinsa.
  5. Yi ƙoƙari ka kammala duka ayyukan da za su ɗauke maka hankali wajen hana ka yin ibada yadda ya kamata kafin shigowar Ramadan.
  6. Mutum ya zauna ya tsara lokacinsa da kuma yadda zai gabatar da ayyukansa a cikin Ramadan. Kamar karance Alƙur’ani baki ɗayansa, tabbatar da sallatar sallar tarawihi kowane dare, ko gayyatar mutane zuwa wajen buɗe-baki, tsara abubuwan da ake burin cim ma a watan da dai sauransu. Ka tabbatar da ka tsara abin da kake so ka cim ma kowane dare kafin ka kwanta a Ramadan, sannan ka yi kokarin dabaka wannan dabi’a ko da bayan wucewar Ramadan.
  7. Duba lafiyarka da kuma ƙarfin aljihunka, wannan abu ne mai muhimmanci.
  8. Yin azumin watan Sha’aban: An ruwaito a cikin wani hadisi mai inganci daga Aisha (RA) cewa: “Wasu lokuta Manzon Allah (SAW) yana yin azumi sosai kamar ma ba ya hutawa, haka nan wasu lokautan yakan huta da yin azumi kamar ma ba ya yin azumi. Ban taba ganin inda Manzon Allah (SAW) ya yi azumin wata cikakke ba in banda Ramadan. Sannan ban taba ganin inda yake ƙoƙarin yin azumi ba fiye da na watan Sha’aban.”
  9. Zuwa ga ‘yan kasuwarmu: ‘Yan kasuwa (maza da mata) a ji tsoron Allah a daina tsawwala ma kayayyakin masurufi kuɗi a watan Ramadan don neman yardar Allah da albarkarSa a cikin kasuwancinku. Kamata ya yi ma a ce kuna yin garaɓasar kayayyaki da Ramadan.

Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya ci gaba da shiryar da mu da kuma kare mana imaninmu, Ya ƙaddare mu da ganin watan Ramadan mai zuwa, kana Ya amsa mana duka ibadunmu, amin.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talika.

Wannan huɗuba ce da aka gabatar a masallacin Juma’a na Nurul Yaqeen da ke Life Camp, Abuja – Daga bakin Imam Yahya Alyolawi – 26, Maris, 2021 / 12, Sha’aban,1442