26
May
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Borno ta sanar da sanya takunkumin zirga-zirgar ababen hawa da mutane na wucin-gadi domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da sallar Idi a gobe Laraba. Rahotanni sun bayyana cewa, takunkumin, wanda Gwamna Babagana Zulum ya amince da shi, zai fara aiki ne daga ƙarfe 6 na safe zuwa 11 na safe a ranar Laraba. Haka kuma, zai shafi motoci, adaidaita sahu da babura. Matakin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Rundunar Sojin Nijeriya ta yi gargaɗin yiwuwar hare-haren ta’addanci a wuraren taruwar jama’a a faɗin jihar. A sanarwar da Kwamishinan Yaɗa…
