Babaji

5684 Posts

Atiku ya lashe zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa a ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar adawa ADC, ta ayyana tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar a matsayin wanda ya ci zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa yayin babban zaɓen 2027. Atiku ya samu jimillar ƙuri'u 1,846,370, wanda hakan ya ba shi damar doke abokin karawarsa kuma tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, wanda ya samu ƙuri'a 504,117. Haka ma ɗan kasuwa Mohammed Hayatu-Deen, wanda ya zo na uku da ƙuri'a 177,120. Wannan sakamako ya nuna cewa Atiku shuni ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, a wani yanayi da masu sharhi ke bayyanawa…
Read More

Gwamnan Zamfara ya buƙaci a ƙara addu’o’in zaman lafiya yayin bikin Babbar Sallah

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga al’ummar jihar da ma ɗaukacin Nijeriya da su ƙara dagewa wajen yin addu’o’in zaman lafiya da tsaro a yayin bikin Babbar Sallah na shekarar 2026. Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon taya murnar Babbar Sallah da ya aikewa al’ummar jihar a ranar Laraba, inda ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan babban biki na addinin Musulunci. Babbar Sallah, wadda Musulmi ke gudanarwa duk shekara a ranar 10 ga watan Zul-Hijja, biki ne da ke nuna sadaukarwa da biyayya ga Allah, kamar yadda Annabi Ibrahim (A.S.) ya nuna cikakkiyar biyayya…
Read More

Babbar Sallah: Dakarun tsaro sun tabbatar da yin sallar idi cikin aminci a Arewa maso Gabas

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaron Atisayen Haɗin Kai (OPHK) da ke aiki a ƙarƙashin atisayen DESERT SANITY V/SIEGE a arewa maso gabashin Nijeriya, sun cimma gagarumar nasara a sassan shiyyar sakamakon tabbatar da gudanar da sallar Idi cikin aminci yayin fuskantar matsin ayyukan 'yan ta'adda. A wata sanarwa da jami'in yaɗa labaran jami'an haɗaka na OPHK, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar a yau Laraba, ya ce dakarun da aka tura ƙauyen Ngoshe a Jihar Borno, sun tabbatar da bada wadataccen tsaro wajen yin aiki tare da 'yan bijilante da wasu 'yan sa kai daga mazauna yankin,…
Read More

Ranar Arafa: NAHCON ta tabbatar wa mahajjatan Nijeriya dawowa gida cikin ƙoshin lafiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta yi kira ga mahajjatan Nijeriya da su kasance masu haƙuri, sadaukarwa da haɗin kai yayin da suka shiga sahun miliyoyin Musulumi wajen yin Ibadar ranar Arafa. NAHCON ta bayyana ranar Arafa a matsayin lokaci na musamman yayin aikin hajji wajen neman gafara, rahama da miƙa wuya ga Allah Maɗaukakin Sarki akan dukkan buƙatun rayuwa. A cewarta, darussa da aka samu a aikin hajjin shekarun bayan suna taimakawa wajen aiwatar da sababbin gyare-gyaren da nufin inganta walwala da zama cikin ƙoshin lafiya ga mahajjatan Nijeriya a Saudiyya. Haka kuma,…
Read More

Katsina: Raɗɗa ya tsige mai taimaka masa na musamman kan hannu a kitsa garkuwa da ƙaramin yaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya dakatar da babban mai taimaka masa na musamman akan ci-gaban al'umma, Alhaji Nura Aliyu Garwa bisa zargin sa da hannu a garkuwa da wani ɗan shekara 8 mai suna Imam Abubakar. Kwamishinan yaɗa labarai da al'adu na jihar, Dakta Bala Salisu Zango ne ya sanar da haka a ranar Litinin. Ya ce, ana zargin Nura Aliyu Garwa ne da hannu a sace yaron a yankin rukunin gidajen Sardauna da ke cikin garin Katsina, lamarin da ya sanya gwamnan ya dakatar da shi daga muƙamin. Ya ƙara…
Read More

EFCC ta mayar da tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman kurkukun Kuje bayan hukunci

Hukumar Yaƙi da Rashawa EFCC, ta tura tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, zuwa gidan yarin Kuje bayan kotu ta same shi da laifin cin hanci da rashawa. Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya bayar da umarnin a ranar Talata. Tun a ranar 7 ga watan Mayu kotun ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume goma sha biyu da EFCC ta shigar, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru saba’in da biyar a gidan yari saboda rashin halartar zaman yanke hukunci. Kotun ta kuma bayar da umarnin kamo shi bayan ya ɓace, kafin…
Read More

Amaechi ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, yana mai cewa babu adalci da gaskiya a ciki. Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X bayan zaɓen da aka gudanar ranar Talata, Amaechi ya zargi masu shirya zaɓen da hana wasu masu kaɗa ƙuri'a damar yin zaɓe tare da aikata maguɗin zaɓe. Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Rivers ya bayyana sakamakon da jam'iyyar ta sanar a matsayin wanda aka ƙirƙira, yana mai cewa ba zai amince da duk wani sakamako da ba a yi cikin…
Read More

ADC ta kare zargin maguɗi a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa

Yayin da cece-kuce ke cigaba da mamaye zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, shugabannin jam’iyyar sun buƙaci Rotimi Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen da su nemi hakkinsu ta hanyoyin doka maimakon fito-na-fito a kafafen yaɗa labarai. Kakakin ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa har yanzu babu wata hujja da ke tabbatar da cewa an tafka maguɗi ko murɗe sakamakon zaɓen domin fifita tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen daga jihohin ƙasar nan, don…
Read More

Kotu ta umarci a mayar da tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman kurkukun Kuje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotu ta bayar da umarnin a mayar da tsohon Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Saleh Mamman, zuwa gidan gyaran hali na Kuje domin fara zaman hukuncin da aka yanke masa na shekaru 75 a gidan yari. Kotun ta yanke hukuncin ne bayan samun sa da laifukan almundahana da karkatar da kuɗaɗen gwamnati yayin da yake riƙe da muƙaminsa a gwamnatin tarayya. Hukuncin ya biyo bayan shari’a mai ɗaukar lokaci inda aka gabatar da hujjoji da dama kan yadda aka zarge shi da hannu wajen karkatar da biliyoyin naira. Rahotanni sun bayyana cewa…
Read More

Gombe: Fusataccen mai neman takarar gwamna a PDP ya ƙi amincewa da Pantami

Ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamnan a Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya yi watsi da sanarwar da ta bayyana tsohon Ministan Sadarwa Isa Ali Ibrahim Pantami, a matsayin ɗan takarar gwamna a PDP a zaɓen 2027. Saleh ya bayyana wannan mataki a matsayin wanda bai dace ba, yana mai cewa ba a bi ka’idojin jam’iyya yadda ya kamata ba wajen gudanar da zaben fidda gwani da ya haifar da nasarar Pantami. Ya ce, shigar Pantami cikin takarar PDP ya keta dokokin cikin gida na jam’iyya tare da tauye haƙƙin sauran ‘yan takara da…
Read More