Babaji

5684 Posts

Tinubu ya yi tsokaci akan nasarori a tattali, titina, ilimi da lantarki yayin cikarsa shekera uku a mulki

Shugaba Bola Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar shimfiɗa tubalin farfaɗo da tattalin arziƙi da sake daidaita al’amuran ƙasa bayan shekaru uku da hawansa mulki. Tinubu ya bayyana haka ne a jawabinsa na cika shekara uku cif a mulkin gwamnatinsa a yau Juma'a, 29 ga Mayu, 2026. Shugaban kasar ya ce lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2023, Najeriya na cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki, karancin kudaden shiga, matsalar tsaro da kuma tabarbarewar harkokin gwamnati. Ya ce, gwamnati ta ɗauki matakai masu wahala amma masu muhimmanci domin ceto kasar daga durkushewar tattalin arziki, ciki har da…
Read More

5 ga Yuni za a fara jigilar dawowar mahajjatan Nijeriya, inji NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta sanar da lokacin fara jigilar dawo da mahajjatan Nijeriya daga ƙasa mai tsarki, Saudiyya, wanda za a fara a ranar 5 ga watan Yuni, 2026. Daraktanta na horarwa da bincike, Farfesa Abubakar Abubakar ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai wa Amirul Hajji na Jihar Kano, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulƙadir a Makkah. Ya ce, an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace wajen ganin an dawo da mahajjatan Nijeriya gida cikin ƙoshin lafiya bayan kammala aikin hajjin na 2026. A cewarsa, hukumar da haɗin-gwiwar hukumomin kula…
Read More

MOPPAN ta yi jimamin rasuwar daɗaɗɗiyar jaruma, Wasila Isma’il

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar masu Shirya Finafinai ta Ƙasa MOPPAN, ta miƙa ta'aziyyarta ga 'yan uwa da abokan arziƙi bisa rasuwar abokiyar aiki, Hajiya Wasila Isma'il, wadda ta rasu a ranar Lahadin ta gabata. Daɗaɗɗiyar jarumar na ɗaya daga cikin taurarin Kannywood da suka yi tashe musamman a shekarun baya a lokacin da ta fito a wani fim mai suna "Wasila". A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran MOPPAN na ƙasa, Ibrahim Amarawa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce marigayiyar ta nuna ƙwarewa wajen ilimantarwa da nishaɗantar da masu kallo musamman a ƙasar Hausa. Haka kuma,…
Read More

Aminu Gwarzo ya zama ɗan takarar gwamnan Kano a NDC yayin da Gawuna ya karɓi tikitin na sanata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An zaɓi tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin tutar jam'iyyar NDC bayan da abokin hamayyarsa, Nasiru Yusuf Gawuna ya karɓi tayin jam'iyyar na tsaya wa takarar kujerar sanata a zaɓen 2027 da ke tafe. Mai taimaka wa Gawuna na musamman, Tahir Ahmad ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa tsohon mataimakin gwamnan ya amince da tsaya wa takarar sanatan mazaɓar Kano ta Tsakiya a NDC. Hakan na nufin kawo ƙarshen makonni ana tattaunawa acikin tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Injiniya Rabi'u Musa…
Read More

2027: APM ta tabbatar da Yakubu a matsayin ɗan takarar gwamna a Bauchi, Bala a na kujerar sanatan kudu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar APM a Jihar Bauchi, ta tabbatar da Dakta Yakubu Adamu da Hon. Mahmood Babamaji Abubakar a matsayin ‘yan takarar gwamna da mataimaki a zaɓen 2027 da ke tafe. An bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin babban taron jam’iyyar da aka gudanar bayan kammala zaɓukan fidda gwani na APM a faɗin jihar. Haka kuma, Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed na jihar ya fito a matsayin ɗan takarar sanatan Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar. Da yake jawabi bayan kammala taron, Dakta Yakubu Adamu ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta ɗora akan…
Read More

Hajjin 2026: NAHCON ta tabbatar da kiyaye dokokin tsaron abinci da ƙaddamar da binciken jigilar mahajjata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta jaddada ƙoƙarinta na tabbatar da kiyaye walwala a harkokin aikin hajji, inda ta sanar da tsauraran matakai akan tsaron abinci da ƙaddamar da bincike akan masu aikin jigila da aka zarge su da wulaƙanta mahajjata. A wata sanarwa da NAHCON ta fitar a ranar Alhamis, hukumar ta ce abincin dare da dama a ranar 27 ga watan Mayu, 2027, an ƙi karɓar su saboda rashin cika sharuɗɗan kula da killacewa. An ruwaito cewa, an ƙi amincewa a karɓe su ne da haɗin-gwiwar hukumomin lafiya na Saudiyya bisa nazari…
Read More

Ashiru Kudan ya zama ɗan takarar gwamnan Kaduna a ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar ADC ta zaɓi Isa Ashiru Kudan a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna a babban zaɓen 2027 da ke tafe. Hon. Ashiru tsohon ɗan takarar gwamna ne a Kaduna har sau biyu a ƙarƙashin tutar jam'iyyar PDP. Ashiru Kudan, wanda tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Maƙarfi/Kudan ne, ya yi nasara ne bayan samun ƙuri'a 86,113. Sai tsohon Kwamishinan Ilimi a gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, wato Jafaru Sani, wanda ya zo na biyu da ƙuri'a 29,580. Sauran 'yan takarar sun haɗa da tsohon Kwamishinan Ilimi a gwamnatin yanzu ƙarƙashin Uba…
Read More

Mateta ya taimaka wa Crystal Palace lashe kofin Turai a karon farko

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Crystal Palace da ke ƙasar Ingila ta lashe kofinta na farko na Nahiyar Turai a birnin Leipzig bayan doke Rayo Vallecano ta Sifaniya da ci 1 da 0 a wasan ƙarshe na gasar UEFA Conference League. Palace ta zama ƙungiya ta farko da ta lashe irin kofin a yunƙurin farko cikin shekaru 38. Ɗan wasa Philip Mateta ne ya samu damar zura ƙwallon ne a minti na 51a lokacin da mai tsaron gidan Vallecano, Augusto Batalla ya buge ƙwallon da Adam Wharton ya farmake shi da ita. Wannan nasara ta…
Read More

2027: Shettima ya kirayi jagororin siyasa su kauce wa kalaman tunzuri

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya yi kira ga jagororin siyasa da 'yan ƙasa da su tunkari zaɓen 2027 cikin hikima da ƙaurace wa dukkan abin da zai janyo fitina, yana mai gargaɗin tunzura ka iya haddasa tashin-tashina a Nijeriya. Shettima ya kuma tabbatar wa al'umma cewa gwamnatocin tarayya da na jihohi na aiki tuƙuru wajen magance matsalolin tattali ta gyare-gyare da wasu shirye-shirye da ke gudana. Ya bayyana haka ne a jiya Laraba bayan kammala sallar Idi a filin Ramat Square da ke Maiduguri, Babban birnin Jihar Borno. A wata sanarwa da Kakakinsa,…
Read More

Wadada ya roƙi tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Adamu ya dawo APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC a Jihar Nasarawa, Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya yi kira ga babban abokin karawarsa a zaɓen fidda gwani da aka yi jla jihar kwanan nan, wato tsohon Sufeto Janar na 'Yan sanda, Mohammed Adam Abubakar da ya cigaba da zama a jam'iyyar domin taimaka wa kai ta ga nasara a zaɓen 2027. Tsohon sufeton ya sanar da ficewarsa daga APC zuwa jam'iyyar SDP bayan ya yi rashin nasara a zaɓen fidda gwani a karawarsu da Wadada. Mohammed Abubakar ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su tafi…
Read More