25
May
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba da Alhamis, wato 27 da 28 ga watan Mayu, 2026 a matsayin lokacin hutun Babbar Sallah. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da haka ta ofishin Babbar Sakatariyar ma'aikatar, Magdalene Ajani a wata sanarwa. A cewar sanarwar, gwamnatin ta yi haka don girmama addinai da abin da miliyoyin al'ummar Nijeriya suka gada wajen yin biki da kuma al'ummar Musulmi a sassan duniya. Tunji-Ojo ya kuma yaba wa al'ummar musulmi a Nijeriya da ma sauran ƙasashen duniya bisa zagayowar lokacin yana mai bayyana Eid-el-Adha a matsayin biki…
