Babaji

5684 Posts

2027: PRP ta tantance Donald Duke da wasu biyu don zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar PRP ta tantance tsohon gwamnan Jihar Kuros Riba, Donald Duke da wasu mutum biyu don shiga zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027. Za a gudanar da zaɓen ne a ranar 25 ga watan Mayu, 2026. Jam'iyyar ta ce, tantancewar wani ɓangarene na shirye-shiryenta domin tunkarar babban zaɓen 2027. Sakataren yaɗa labaran PRP na Ƙasa, Muhammad Ishaq ne ya sanar da haka a wata takarda. Waɗanda aka tantance sun haɗa da Donald Duke, masanin tattali Dakta Nnaoke Ufere da Jihar Abia da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a…
Read More

Shettima ya tafi Jamhuriyar Benin halartar taron rantsar da shugaban ƙasar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bar Abuja ya tafi Cotonou a Jamhuriyar Benin, inda zai halarci taron ƙaddamar da Shugaba Romuald Wadagni na ƙasar. Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya bayyana haka a wata takarda, ranar Asabar. Shettima zai haɗu da shugabannin ƙasashen Afirka a babban taron rantsar da shugaban, wanda za a yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Cotonou a ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu, 2026. Nkwocha ya bayyana cewa, Nijeriya da Jamhuriyar Benin sun jima da alaƙar…
Read More

Abin da ya hana jagororin ADC ganin El-Rufa’i yayin da yake tsare – ICPC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Yaƙi da Rashawa ICPC, ta ce ta hana shugabannin jam’iyyar ADC ziyartar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne saboda biyayya ga umarnin kotu da ya taƙaita damar ganin sa yayin da yake tsare a hannun hukumar. A cewar Jaridar punch, kakakin hukumar John Odey ya bayyana cewa kotu ta amince ne kaɗai wa iyalansa na kusa, lauyoyinsa da likitocinsa su riƙa ganinsa a halin. Ya kuma musanta zargin cewa jami’an tsaro sun tsorata shugabannin ADC a hedikwatar ICPC da ke Abuja, yana mai cewa abin da aka gani tsari ne na tsaro…
Read More

2027: ADC tsagin su Bala ya tantance ‘yan takara 1,657, ya soke 212

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam’iyyar ADC tsagin su Nafiu Bala Gombe, ya kammala tantance masu neman takara gabanin zaɓen fidda gwani da za ta gudanar a faɗin Nijeriya. Jam’iyyar ta bayyana cewa, an amince da mutane 1,657 su shiga zaɓen fidda gwani, yayin da aka kori mutum 212 saboda rashin cika sharuddan da aka gindaya. Ta ce, an gudanar da tantancewar ne cikin tsari da gaskiya a jihohi 36 da Abuja, inda aka kafa kwamitocin tantancewa bisa kundin tsarin jam’iyyar da dokokin zaɓe. Jam'iyyar ta ƙara da cewa, 'yan takara 980 ne aka tantance a matakin majalisun dokokin…
Read More

Sheikh Ahmad Gumi ya musanta goyon bayan ayyukan ‘yan bindiga

Shahararren malamin addinin Musuluncin nan da ke zama a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya fitar da gargaɗi mai ƙarfi ga mutanen da ke cigaba da alaƙanta shi da ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a ƙasar nan. Rahotanni sun bayyana cewa, shehin ya nuna ɓacin ransa akan yadda wasu ke amfani da kalaman ɓatanci wajen shafawa da'awarsa kashin kaza, inda ya buƙaci masu sukarsa da su gaggauta dakatawa. Sheikh Gumi ya bayyana cewa, ɗaukacin ƙoƙarin da ya yi a baya na shiga daji domin tattaunawa da ƴan bindigar ba don yana goyon bayan ayyukansu ba ne, illa dai…
Read More

Tinubu zai karɓi shaida bayan lashe zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa a APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Lahadi Shugaba Bola Tinubu zai karɓi takardar shaidar zama ɗan takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar APC, bayan kammala zaɓen fidda gwani na jam’iyyar domin zaɓen 2027. Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga a wata sanarwa ta ranar Asabar, ya ce Kwamitin Zaɓen Fidda Gwanin Shugaban Ƙasa na APC ne zai miƙa takarda da tutar a Cibiyar Taro ta Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre da ke Abuja. Ya ce, hakan zai gudana ne bayan tattara sakamakon zaɓen daga sassan ƙasar da aka gudanar a ranar Asabar. Sanarwar ta kuma ce, gwamnonin APC, mambobin…
Read More

Ni na yi silar zaman Buhari shugaba ba Tinubu ba, inji Amaechi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu akan iƙirarinsa na cewa da ba dan shi ba marigayi Muhammadu Buhari ba zai ci zaben 2015 ba. Amaechi ya ce, Tinubu, wanda tsohon gwamna ne kima jagora a jam'iyyar APC, bai yi abin a zo a gani ba a zaman Buhari shugaban ƙasa. Amaechi ya ce bai kamata Tinubu ya ce shi ne ya yi silar zaman Buhari shugaban kasa a 2015 ba, har ma ya riƙa iƙirari da cewa tallafin siyasarsa ne ya sa…
Read More

Alƙalin Kotun Tarayya, Mohammed Nasir Yunusa ya rasu a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Shari'a Mohammed Nasir Yunusa na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ya rasu. An ruwaito cewa, alƙalin ya rasu ne a ɗakinsa na kwana bayan ya yanki jiki ya faɗi a daren ranar Alhamis wayewar Juma'a, lamarin da ya sa aka gaggauta garzayawa da shi asibiti inda a nan aka tabbatar da rasuwarsa. Rahotanni daga Babbar Kotun Tarayya a Abuja sun tabbatar da faruwar al'amarin a yau Asabar. Sun ce tuni aka masa jana’iza a ranar Juma'a. Ita ma Daraktar yaɗa labaran Babbar Kotun, Catherine Oby Christopher, ta tabbatar da faruwar al'amarin, inda…
Read More

Ɗan Ganduje ya koma NDC, ya yanki tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin Kwankwasiyya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya yankin tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin tutar jam’iyyar NDC. Rahotanni sun bayyana cewa, Abdulaziz ya yanki fom ɗin ne a yau Asabar domin shiga takarar ta mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a zaɓen 2027 da ke tafe. Wannan mataki ya janyo cece-kuce a fagen siyasa da alaƙar Abdulaziz da tafiyar Kwankwasiyya na tsawon lokaci duk da tasirin mahaifinsa a APC a ‘yan shekarun baya-bayan nan. Ana ganin Abdulaziz a matsayin mai biyayya ga Rabi’u Musa Kwankwaso kuma ya jima yana…
Read More

Ɗan Ganduje ya koma NDC, ya yanki tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin Kwankwaso

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya yankin tikitin takarar kujerar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin tutar jam'iyyar NDC. Rahotanni sun bayyana cewa, Abdulaziz ya yanki fom ɗin ne a yau Asabar domin shiga takarar ta mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a zaɓen 2027 da ke tafe. Wannan mataki ya janyo cece-kuce a fagen siyasa da alaƙar Abdulaziz da tafiyar Kwankwasiyya na tsawon lokaci duk da tasirin mahaifinsa a APC a 'yan shekarun baya-bayan nan. Ana ganin Abdulaziz a matsayin mai biyayya ga Rabi'u Musa Kwankwaso kuma ya jima yana…
Read More