Babaji

5684 Posts

Hajjin 2026: Adadin maniyyata ya kai miliyan 1.5 duk da yaƙin Gabas ta Tsakiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin sama da maniyyata miliyan 1.5 ne suka je Saudiyya daga wajen ƙasar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026, lamarin da ke nuna adadin ya haura na bara duk da yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya. Rikicin wanda aka fara a ƙarshen watan Fabarairu tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran, ya shafi wani sashi na Saudiyya da wasu sassan yankin Gulf, wanda ya janyo tsaiko ga sufurin jiragen sama da tsadar tafiye-tafiye. Manyan tashoshin jiragen sama a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Ƙatar da Bahrain sun yi aikin gyara harkokinsu cikin hanzari makonni bayan rufe su.…
Read More

Dala 600,000 nake karɓa a kowace gayyata, kuma ina amsar aƙalla huɗu a wata, inji mawaƙi Davido

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen mawaƙin nan na Nijeriya, Davido ya sake tayar da hazo a kafafen sada zumunta, inda ya bayyana adadin kuɗaɗen da yake karɓa a kowace gayyata. A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ƙwararren mawaƙin na 'Afrobeats', ya ce ba ya karɓar ƙasa da Dala 600,000 a kowane aikin gayyata, wato kimanin Naira miliyan 825 gwargwadon matakin sauyin kuɗi. Davido ya bayyana cewa, aƙalla yana amsar gayyata guda huɗu a kowane wata, wanda ya kai jimillar kuɗaɗen da yake samu a wata zuwa Dala miliyan 2.4, wato biliyan N3.4. Wannan batu…
Read More

Bindow ya janye shiga takarar gwamnan Adamawa a ADC, ya jaddada biyayya ga jam’iyya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Muhammed Umaru Jibrilla Bindow, ya sanar da janyewa daga shiga takarar gwamna a ƙarƙashin Jam’iyyar ADC. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Bindow ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan zurfin tunani da kuma yin la’akari sosai, inda ya ce janyewar ta samo asali ne daga dalilai na ƙashin kai. Duk da janyewar, tsohon gwamnan ya sake tabbatar da cikakken biyayya da goyon bayansa ga jam’iyyar, tare da alƙawarin cigaba da mara mata baya da shugabancinta a Jihar Adamawa. Haka kuma ya yi godiya magoya…
Read More

Michael Carrick ya amince da zama kocin Manchester United na shekara biyu

Ƙungiyar Manchester United ta sanar da naɗin Michael Carrick a matsayin kocinta 'yan wasanta na dindindin, inda zai cigaba da jagorantar ta har zuwa shekarar 2028. Carrick, wanda tsohon ɗan wasan United ne, ya samu wannan muƙamin ne bayan rawar gani da ya taka a matsayin kocin wucin gadi tun daga watan Janairun 2026. A ƙarƙashin jagorancinsa, United ta samu sauye-sauye masu kyau, ciki har da samun gurbin shiga Gasar Zakarun Turai (Champions League) da kuma kammala kakar Premier League a matsayi na uku. Rahotanni sun bayyana cewa, shugabannin ƙungiyar sun gamsu da irin tasirin da Carrick ya yi akan…
Read More

Sharafadeen Alli ya doke tsohon Ministan Lantarki a zaɓen fidda gwanin gwamnan APC a Oyo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanata mai wakiltar mazaɓar Oyo ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sharafadeen Alli, ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo, bayan da ya doke manyan abokan hamayyarsa a zaɓen da aka gudanar. Rahotanni sun bayyana cewa Alli ya samu ƙuri’u 578,143, wanda hakan ya ba shi nasarar zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar. Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya zo na biyu da ƙuri’u 19,193, yayin da wani ɗan takara guda ɗaya ma ya shiga takarar. Nasarar ta Sharafadeen Alli na zuwa ne yayin…
Read More

Pep Guardiola ya tabbatar da barin Man City cikin juyayi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Manchester City ta tabbatar da cewa kocin 'yan wasanta, wato Pep Guardiola zai bar kulob ɗin a ƙarshen kakar wasan bana. Ɗan Sifaniyar mai shekaru 55 ya sanar da haka a ranar Juma'a ta wani faifan bidiyo, inda aka gan shi cikin halin takaici yana wa magoya bayan ƙungiyar jawabi, lamarin da yak kawo ƙarshen zamansa a kulob ɗin na tsawon kusan shekara goma. A cewar BBC Sport, Man City ta fara shirye-shiryen ɗauko wani koci tun tsawon shekara guda gabanin ƙarewar kwantaragin Guardiola. A gobe Lahadi ne Guardiola zai jagoranci wasansa na…
Read More

Kakakin majalisar Kwara ya kada na hannun daman gwamnan Kwara a zaɓen fidda gwanin APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Hon. Yakubu Danladi Salihu ya lashe zaɓen fidda gwanin takarar gwamna na jam'iyyar APC da aka gudanar a ranar Juma'a. Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwanin gwamna na jihar a jam'iyyar, Sanata Musliu Obanikoro yayin sanar da sakamakon, ya ce Hon. Danladi-Salihu ya samu ƙuri’u 94,000, lamarin da ya ba shi damar doke 'yan takara takwas a zaɓen. Shugaban kwamitin zaɓen ya kuma yaba wa mambobin jam'iyyar bisa fitowa ƙwansu da ƙwarƙwata duk da cewa an ɗage zaɓen daga Alhamis zuwa Juma'a. Ya ƙara da cewa, yin zaɓen cikin lumana…
Read More

Wadada ya zama ɗan takarar gwamnan Nasarawa a APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanata Aliyu Ahmed Wadada ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamna a ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC a Jihar Nasarawa. Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na APC a Jihar, Farfesa Theodore Maiyaki (SAN) ya sanar da haka a gidan gwamnatin jihar da ke Lafiya a yammacin ranar Juma'a. Ya ce, Wadada ya yi nasara ne bayan samun ƙuri’a 195,285, lamarin da ya ba shi damar doke abokin hamayyarsa na kuma tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, wanda ya samu ƙuri’u 39,675. Da fari, Gwamna Abdullahi Sule ya ayyana Sanata Wadada a matsayin…
Read More

Ɗan kasuwa ya rasu yayin rikici da ɗansa a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan Sanda a Abuja ta fara bincike akan mutuwar wani ɗan kasuwa mazaunin Abuja mai suna Mista Adimike Godwin, wanda aka yi zargin an halaka shi ne a yayin wani rikici a gidansa da ke yankin Guzape a babban birnin tarayyar. Wasu rahotanni da ake yaɗawa ta kafafen sada zumunta sun nuna cewa marigayin ya rasu ne bayan sa'insa da ɗansa mai shekaru 19 da aka ce mai yi wa ƙasa hidima (NYSC) ne ya soka masa wuƙa. Saidai, jami'an hukumar 'yan sandan ba su tabbatar da asalin sunan makashin ba ko ainihin…
Read More

‘Yan sanda sun gargaɗi matafiya bayan kama ‘yan fashin manyan titina a Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan Sanda a Jihar Kebbi ta ce ta kama mutane biyar bisa zargin su da hannu a ayyukan fashi da makami da garkuwa da mutane, inda ake danganta su da 'yan "one chance" akan manyan hanyoyin sassan jihar. Kakakin rundunar, Bashir Usman ne ya sanar da haka a wata takarda, inda ya ce an kama waɗanda ake zargin ne yayin wasu shiryayyun atisaye da aka yi ƙananan hukumomin Birnin Kebbi, Kalgo, Jega, Maiyama da Aliero. Mutanen da aka kaman sune Abubakar Muhammad na ƙauyen Bancho a Tambuwal, Shehu Ango, Shamsu Daudu, Shuaibu Umar…
Read More