22
May
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimamin fatake 'yan Nijeriya sama da 1,100 ne suka isa Kano daga Agadez a Jamhuriyar Nijar ta hanyar tattaki, kamar yadda Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa ta bayyana. Hukumar ta ce, an zuba jami'an hukumomin tsaro a matakin ƙasa da jiha domin kula da su da sadar da su ga iyalansu. Kwamandan na Makarantar Horar da Jami'an Shige da Fice, Anthony Akuneme, ya bayyana cewa tuni aka ɗauki dukkan bayanan da suak dace akansu domin tabbatar bin dukkan ƙa'idojin da ake buƙata gabanin damƙa su ga makusantansu. Cibiyar tantance ƙasashen ɗaiɗaikun mutane ta…
