Babaji

5684 Posts

2027: Tambuwal ya janye tsaya wa takarar sanata yayin da jita-jitar zama mataimakin shugaban ƙasa ta ɗauki ɗumi

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya janye daga batun tsaya wa takarar kujerar sanatn Sakkwato ta Kudu yayin tunkarar zaɓen 2027. Rahotanni sun bayyana cewa Tambuwal, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC kuma na kusa da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya ɗauki matakin ne sakamakon sauye-sauyen siyasa da ke gudana a bangaren adawa. Janyewar tasa na zuwa ne yayin da jam’iyyar ADC a jihar Sokoto ta bayyana sunayen wadanda za su tsaya takara a mukamai daban-daban na zaben shekarar 2027. Jam’iyyar ta bayyana Alhaji Manir Dan Iya a matsayin dan takarar gwamna, yayin da Ambasa Faruk…
Read More

Yadda Tinubu ya kusa tsige ni saboda Desmond Elliot – Femi Gbajabiamila

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa ya kusa rasa muƙaminsa na Gwamnatin Tarayya saboda goyon bayan da yake ba wa ɗan Majalisar Dokokin Lagos, Desmond Elliot. Gbajabiamila ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya kira shi yana tambayarsa ko Desmond Elliot mutuminsa ne, bayan zargin cewa yana cikin ‘yan majalisar da suka jagoranci tsige tsohon Kakakin Majalisar Legas, wato Mudashiru Obasa. Ya bayyana cewa, ya shawarci Elliot da ya fito ya nesanta kansa daga batun tsige Obasa, amma bai yi hakan ba saboda waɗansu dalilai. Desmond Elliot na wakiltar mazaɓar Surulere,…
Read More

Kaduna: Uba Sani ya kafa kwamitin sasanci don ƙarfafa haɗin kan ‘yan APC gabanin zaɓen 2027

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da kafa wani kwamitin sasanci domin ƙarfafa haɗin kai da daidaito a cikin jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen da ke tafe. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ya fitar, inda ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin bunƙasa dimokiraɗiyya ta cikin gida, ƙarfafa haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki, da kuma samar da fahimtar juna tsakanin masu neman takara a faɗin jihar. Sanarwar ta bayyana cewa kwamitin zai riƙa tattaunawa da masu neman takara, shugabannin jam’iyya da sauran masu…
Read More

Sojoji sun halaka mayaƙan Lakurawa biyu da ƙwato makamai a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro sun yi nasarar halaka mayaƙan Lakurawa guda biyu yayin da suka farmaki wata daba ta 'yan ta'addar a Ƙaramar Hukumar Tangaza da ke Jihar Sakkwato. Haka kuma sun ƙwato wasu muggan makamai da dabbobi da aka sace a wasu atisayen a jihohin Sakkwato da Katsina. A cewar wata sanrwa da Mataimakin Daraktan hulɗa da jama'a na riƙo na rundunar da ke sashe na 8 kuma ɓangare na 2 na atisayen FANSAN YAMMA, Laftanal Kanal Olaniyi Osoba ya fitar a yau Juma'a, atisayen, wani ɓangare ne na yaƙi da ayyukan 'yan ta'adda da…
Read More

Ɗangote ya ki amince wa kamfanin NNPC ya ƙara hannun jari a matatarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya ce kamfaninsa ya yi watsi da buƙatar da Babban Kamfanin Fetur a Ƙasa NNPC ya gabatar ta neman ƙara adadin hannun jarinsa a Matatar Ɗangote da kaso 7.25 cikin 100. Ɗangote ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da shugaban asusun zuba jari na Norway, Nicolai Tangen, kamar yadda ra rahotanni suka bayyana. An ruwaito cewa an samu ƙaruwar man da ake tacewa a matatar mai ta Lekki a Jihar Legas zuwa lita biliyan 3.18 a watanni uku na farkon 2026 yayin da man…
Read More

Sheikh Nuru Khalid ya nemi maniyyata su ƙara haƙuri da jigilar NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban malamin addinin Islama a Abuja, Sheikh Nura Khalid, ya yi kira ga maniyyatan Nijeriya na hajjin bana da su kasance masu haƙuri da lamuran hukumomin Hajji yayin da suke ƙoƙarin samar musu da yanayi mai kyau a zamansu na Makkah. Shehin ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis yayin gabatar wa maniyyatan jihohin Abuja da Oyo jawabi a lokacin da suka isa Makkah daga Madinah. A cewarsa, aikin hajjin musamman a lokacin da maniyyata ke sanye da iharami na buƙatar haƙuri da juriya domin yi wa kai da Nijeriya addu'a. Ya kuma…
Read More

Ma’aikatan WAEC za su yi zanga-zanga kan matsalolin walwala

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ma'aikatan Hukumar Shirya Jarrabawa ta Makarantun Yammacin Afirka (WAEC), sun shirya gudanar da gangamin gama-gari na kwana uku bisa zargin ayyukan ƙwadago na rashin adalci, matsalolin hanyoyin ɗaukar aiki da wasu lamuran da suka shafi walwala acikin hukumar. Ƙungiyar Ma'aikatan da ba Malamai ba da wasu Cibiyoyi (NASU) ce ta shirya zanga-zangar, wanda tuni aka tsara farawa a ranar 13 ga watan Mayu, 2026 a Hedikwatar WAEC da ke Yaba a Jihar Legas da kuma ofisoshinta na rassan jihohi a Nijeriya. Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana biyu da WAEC ta sanar da…
Read More

EFCC ta kama Daraktan Hukumar Makamashi, Mustapha Abdullahi kan badaƙalar biliyan N500

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, sun yi ram da Darakta Janar na Hukumar Kula da Harkokin Makamashi ta Ƙasa (ECN), Dakta Mustapha Abdullahi bisa zargin sa da hannu a almundahanar wasu maƙudan kuɗaɗe da jimillar adadinsu ya kai Naira biliyan 500. A ranar Laraba wata majiya daga EFCC da ta nemi a sakaye sunanta, ta ce an kama Dakta Abdullahi ne a Abuja, wanda a yanzu yana hannun hukumar. A cewarta, masu bincike suna bincike ne akan zargin hada-hadar kuɗaɗe da suka kai kusan biliyan N500 da aka danganta…
Read More

Hajjin 2026: Ma’aikatar Lafiya a Saudiyya ta ba cibiyoyin lafiyar NAHCON lasisin aiki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta samu amincewa da lasisi a hukumance daga Ma'aikatar Lafiyar Saudiyya ga cibiyoyin lafiyarta da aka samar don kula da lafiyar maniyyata 'yan Nijeriya yayin aikin hajjin 2026. Wannan ya nuna cewa tawagar lafiya ta NAHCON ta samun damar fara ayyukan kula da maniyyatan a ƙasa mai tsarki. An samar da waɗannan cibiyoyi ne musamman don samar da magani ga maniyyatan Nijeriya a matakin farko ciki har da neman shawarwari, kulawar matakin farko da magani ga ƙananan cutuka. Akan haka ne NAHCON ta sanar da maniyyatan…
Read More

Surukar Sarki Aminu Ado Bayero ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iyalan gidan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun shiga alhini bisa rashin surukarsa, Hajiya Karima Lawal, wadda aka fi sani da Yayar Gandu. Marigayiyar ta rasu ne a wani asibiti da ke Kano bayan fama da wani gajeren rashin lafiya, kamar yadda majiyoyi daga gidansu suka shaida. Hajiya Karima ita ce mahaifiyar Hadiza Aminu Ado Bayero, wato matar Sarki Aminu Ado. Akan haka ne aka yi ta miƙa gaisuwar ta'aziyya daga iyalai, dangi, makusantansa da sauran al'umma daga ciki da wajen Kano. Marigayiyar ta rayuwa da 'ya'ya tara da jikoki da dama…
Read More