Babaji

5684 Posts

Abdul Samad Rabi’u ya kere Johann Rupert a matsayin mutum na biyu da ya fi arziƙi a Afirka

Sanannen attajirin ɗan kasuwa a Nijeriya, Abdul Samad Rabiu, ya zama mutum na biyu mafi arziƙi a Afirka bayan dukiyarsa ta haura dala biliyan 18.6, kamar yadda jerin masu kuɗi na Bloomberg Billionaires Index ya nuna. Rahoton ya ce Rabiu ya zarce attajirin Afirka ta Kudu, Johann Rupert, wanda dukiyarsa ta ragu zuwa dala biliyan 17.9 a shekarar 2026. Bloomberg ta bayyana cewa Rabiu ya samu ƙarin arziki mafi yawa a Afirka bana, sakamakon bunƙasar kamfanoninsa na siminti, abinci da masana’antu. Sabon matsayinsa ya sanya shi a bayan Aliko Dangote kaɗai, wanda har yanzu yake matsayin mutum mafi arziki a…
Read More

Filato: ‘Yan bindiga sun halaka mutum 13 da raunata da dama a sabon hari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a Jihar Filato, sun halaka kimanin mutane 13 a ƙauyen Ngbra Zongo da ke Gundumar Kwall a Ƙaramar Hukumar Bassa. Al'amarin ya auku ne a safiyar ranar Juma'a, wanda ya jefa al'umma cikin firgici kuma ya yi sanadiyyar raunata mutane da dama. Wani mazaunin yankin mai suna Philip Alanga ya shaida wa 'yan jarida a Jos cewa maharan sun farmaki ƙauyen ne da tsakar dare, inda suka yi ta harbe-harbe na kan-mai-uwa-da-wabi kana suka riƙa saran su da adduna da wasu makamai masu haɗari. A cewarsa, 'yan…
Read More

Jami’an tsaro sun kama Bello Baɗejo a Jalingo bayan bayyana muradin tsaya wa takarar sanata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, sun kama Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Baɗejo jim-kaɗan bayan ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar sanata a mazaɓar Taraba ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kamar yadda rahotanni suka bayyana. An kama Baɗejo ne a birnin Jalingo, Babban Birnin Jihar Taraba. Bayanan sun nuna cewa Baɗejo ya isa filin jirgin sama na Ɗanbaba Suntai da ke garin Jalingo cikin jirgi mai zaman kansa, inda dubban magoya baya suka tarbe shi daga ƙananan hukumomin mazaɓar. An ruwaito cewa, an kama shi ne da dare…
Read More

Kotu ta ɗage shari’ar jagorancin ADC akan David Mark har illa masha Allah

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Juma'a Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta sake ɗage sauraron ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark. Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ɗage sauraron shari’ar ba tare da sanya wata sabuwar ranar cigaba da sauraro ba, bayan da lauyan mai ƙara ya sanar da kotun cewa sun rubuta wa Babban Alƙalin Kotun Tarayya wasiƙa domin neman a mayar da shari’ar gaban wani alƙali daban. Mai ƙarar, Nafiu Bala Gombe, na ƙalubalantar wasu matakai da suka shafi…
Read More

2027: Kotu za ta yi shari’ar hana Jonathan shiga takarar shugaban ƙasa a yau

Babbar Kotun Tarayya a Abuja za ta saurari wata ƙara a yau wadda ke neman hana tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan sake tsaya wa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen shekarar 2027, a cikin sabon muhawarar doka kan iyakacin wa’adin mulki a kundin tsarin mulki. Wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ne ya shigar da ƙarar, inday a nemi kotun da ta ayyana Jonathan a matsayin wanda bai cancanci sake tsaya wa takara ba bisa tanadin kundin tsarin mulkin Nijeriya. Mai shari’a Peter Lifu ya umarci a aike da sanarwar zaman kotu ga dukkan bangarorin da ke cikin shari’ar, bayan…
Read More

Sakataren gwamnati ya gyara salon gabatar da Tinubu bisa kurakuran ‘yan jarida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya OSGF, ya yi gyara akan salon gabatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu biyo bayan kurakurai da ake samu daga ɓangaren 'yan jarida dangane da al'amarin. Mai ba wa sakataren gwamnatin shawara akan harkokin yaɗa labarai, Yomi Odunuga ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a yau Juma'a. Ya ce, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ne ya yi gyaran musamman domin ankarar da fannin jarida da ɗaukacin al'umma akan batun. A cewarsa, Akume ya roƙi al'umma da gidajen jarida da su riƙa tantance laƙabi a hukumance gabanin wallafawa…
Read More

2027: Shettima ya miƙa wa APC fom ɗin takarar Tinubu na zaɓen shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya miƙa fom ɗin nuna sha’awa da na tsaya wa takarar Shugaba Bola Tinubu ga jagororin ƙasa na jam’iyyar APC. Shettima, wanda ya miƙa fom ɗin a Cibiyar Taro ta Ƙasa-da'Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja, ya yi kira ga gwamnonin APC da ‘yan Majalisar Tarayya da su mara wa takarar Shugaban Ƙasar baya. Ya ce, gwamnatin Tinubu ta fara kawo sauye-sauye masu anfani ta hanyar ajandar “Renewed Hope”, duk da ƙalubalen tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta. Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe…
Read More

Legas, Kano da Ribas na cikin jihohin da ke fuskantar barazanar ambaliya, inji NiMet

Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa NiMet, ta yi gargadin cewa aƙalla jihohi 19 a fadin Nijeriya ka iya fuskantar ambaliyar ruwa acikin kwanaki masu zuwa sakamakon dakon mamakon ruwan sama da ake sa ran samu. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, NiMet ta bayyana cewa, haɗarin ambaliya ya ƙaru saboda bushewar kasa da zai hana ruwa ya ratsata yadda ya kamata, wanda hakan zai haifar da ka iya haifar da ambaliyar. Hukumar ta ce Jihohin da abin zai shafa sun hada da Zamfara, Nasarawa, Kwara, Oyo, Legas, Ogun, Ekiti, Delta, Imo, Anambra, Enugu, Ebonyi, Akwa Ibom,…
Read More

Masu yin kabbara yayin yi wa wasu kisan gilla za su je wuta, inji Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya ce duk wanda ya kashe mutumin da ba shi da laifi yana kabbara (Allahu Akbar), to wuta ce makomarsa. Ya jaddada cewa addinin Musulunci bai koyar da hakan ba, kuma babu dalilin karkashe mutane da sunan addini. Sarkin ya faɗi haka ne a ranar Laraba yayin taron Majalisar Tattaunawa Tsakanin Addinai ta Ƙasa (NIREC) da aka gudanar a Abuja. Ya buƙaci al'umma da su daina danganta ta’addanci da addini, inda ya ce "Bari mu kira su da sunansu na asali—masu laifi. Kada a ce masu laifi Musulmai ko ’yan ta’adda Musulmai." Muhammadu…
Read More

Hajjin 2026: Sama da maniyyata 9,000 sun tafi Madinah daga Nijeriya, inji NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ce kimanin sama da maniyyata aikin hajjin 2026 guda 9,000 ne suka isa birnin Madinah zuwa yanzu. A cewar bayanai daga jami'an NAHCON a Saudiyya, adadin ya kai haka ne tun daga fara jigilar su a ranar Lahadin da ta gabata. Hukumomin Saudiyya sun amince da karɓar maniyyata daga Nijeriya guda 50,000 na shekarar 2026. Waɗancan maniyyata da suka riga suka isa ƙasar, za su yi aƙalla kwana huɗu kafin garzayawa zuwa Makkah domin cigaba da gudanar da ibadar. Wani bayani da NAHCON ta fitar ya nuna cewa,…
Read More