Babaji

5684 Posts

Jirgin yaƙin sojoji ya yi kuren halaka fararen hula da dama yayin farautar ‘yan bindiga a Neja

Wasu fararen hula da ba a tantance adadinsu ba sun rasa rayukansu sakamakon wani sabon harin bom ta sama da ake zargin sojoji suka kai a ƙauyen Guradnayi da ke kusa da Kusasu a Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Lamarin ya kara jefa al’umma cikin fargaba, yayin da ake ci gaba da samun rahotannin hare-haren jiragen yaki da suka yi sanadin mutuwar fararen hula a yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Najeriya. Majiyoyi da dama sun shaida wa manema labarai cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi. Hotunan da aka samu daga wurin sun nuna…
Read More

Gwamnatin Kaduna ta ware biliyan N50 don yaƙi da ambaliya da zaizaya

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da rattaba hannu kan kwangiloli guda uku da kudinsu ya haura naira biliyan 50 domin aiwatar da manyan ayyukan dakile ambaliya da zaizayar kasa a yankunan Rigasa da Tudun Wada, Kawo da kuma cikin garin Zaria. An gudanar da aikin ne ta hannun Hukumar Gudanar da Aikin ACReSAL ta jihar, domin magance matsalolin ambaliya da zaizayar kasa da ke barazana ga rayuka, kadarori da muhalli a sassan jihar. Rahotanni sun bayyana cewa bayan kammala tsarin tantance kamfanoni da bayar da kwangila cikin gaskiya, an bai wa kamfanonin Mothercat Nigeria Limited, da CGC Nigeria Limited da…
Read More

Sojoji sun halaka mayaƙan ISWAP 50 da ƙwato makamai a Yobe

Dakarun rundunar Atisayen HAƊIN KAI sun kashe aƙalla mayaƙan ƙungiyar ISWAP 50 tare da ƙwato makamai masu yawa bayan wani hari da aka kai a hedikwatar Birgetta 27 da ke Buni Gari a Jihar Yobe. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin-gwiwa ta Arewa maso Gabas, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce ‘yan ta’addar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 2 na dare daga wurare daban-daban domin kutsawa sansanin sojojin. Sanarwar ta ce dakarun sun yi amfani da ƙarfin wuta da dabarun yaƙi wajen dakile harin, lamarin da ya jawo mutuwar mayaƙa da dama…
Read More

EFCC ta ayyana tsohuwar ministar jin-ƙai, Sadiya Farouk wadda ake nema ruwa a jallo

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta ayyana tsohuwar Ministar Jin-ƙai da Harkokin Agaji, Sadiya Umar Farouq a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo bisa wasu zarge-zargen badaƙalar kuɗaɗen gwamnati. A cikin sanarwar da hukumar ta wallafa, EFCC ta bayyana cewa tana neman tsohuwar ministar ne dangane da zargin amfani da muƙami ba bisa ka'ida ba, haɗa baki wajen aikata laifi da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati yayin da take riƙe da muƙaminta. Hukumar ta bayyana cewa Sadiya Umar Farouq ta taɓa zama Ministar Jinƙai da Harkokin Agaji a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari,…
Read More

NDC ta ba Kudu tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027

Jam’iyyar adawa ta NDC ta cimma matsaya a hukumance na mayar da tikitin takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027 zuwa yankin Kudu na wa’adin shekara huɗu kacal, bayan haka kuma tikitin zai koma yankin Arewa. Majiyoyin jam’iyyar sun tabbatar wa wakilinmu hakan yayin da babban taron ƙasa na jam’iyyar ke gudana a Abuja yau. An cimma wannan matsaya ne a yayin taron da ake gudanarwa a Los Angeles Event Centre da ke kan titin Ahmadu Bello Way, inda wakilan jam’iyyar suka amince da shawarar bayan doguwar tattaunawa kan tsarin rabon tikitin takarar shugaban ƙasa. Bisa ga yarjejeniyar, yankin Kudu ne…
Read More

2027: Atiku, Amaechi da Hayatu-Deen sun yanki fom ɗin takarar shugaban ƙasa a ADC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi sun mallaki fom a jam’iyyar ADC domin neman tsaya wa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027. Haka ma Mohammed Hayatu-Deen, wanda shi ma ya mallaki fom ɗin, inda ya ci alwashin fifita harkar tsaro, samar da ayyuka da kuma nuna damuwa akan matsin tattalin arziƙi da al’ummar Nijeriya ke fuskanta. Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya tabbatar da haka ga manema labarai a ranar Juma’a, inda ya ce ‘yan takarar uku tuni suka sayi fom ɗin. Ana sayar da fom…
Read More

Sufeto Janar ya umarci a binciki zargin kisan Dadiyata kan wasu manyan ‘yan sanda

Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu ya umarci sashen sa ido na rundunar da su gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa wasu manyan jami’an ’yan sanda biyu, CSP Hussaini Gimba da CSP Hassan Gimba. Za a yi binciken dangane da ɓacewar da kuma zargin kisan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata. Wannan umarni ya biyo bayan jerin ƙorafe-ƙorafe da wani mai fafutuka kuma lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam mazaunin Kano, Abba Hikima ya gabatar a ranar Juma’a. Takardun ƙorafe-ƙorafen, waɗanda wakilinmu ya gani kuma aka aika wa Sufeto-Janar, sun jawo hankali ne kan…
Read More

2027: Jonathan ya ƙalubalanci ƙarar neman hana shi tsaya wa takarar shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya ƙalubalanci ƙarar da wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ya shigar domin hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Ta bakin lauyansa, Chris Uche, Jonathan ya roƙi Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ya yi watsi da ƙarar. Lauyan ya bayyana cewa, sun shigar da takardun ƙalubalantar ƙarar tun ranar 5 ga Mayu, 2026, yana mai cewa an taɓa yanke hukunci kan irin wannan batu tun daga Babbar Kotun Tarayya har zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara. A nasa ɓangaren, lauyan…
Read More

Rikicin Masarautar Kano: Ni ban ce na amince da Sarki Sanusi ba, inji Ganduje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya musanta amincewa da Muhammadu Sanusi na II a matsayin Sarkin Kano, yana mai cewa Kotun Ƙoli ce kaɗai ke da ikon yanke hukunci akan rikicin masarautar. Ganduje ya ce duk hukuncin da kotun koli ta yanke, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai mutunta shi tare da aiwatar da shi bisa doka da oda. Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ya amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano kuma shugaban majalisar sarakunan jihar…
Read More

Hatsarin mota ya yi ajalin mutane 16 a Jihar Kogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin mutane 16 ne suka rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a babban titin Lokoja zuwa Okene da ke jihar Kogi. Rahotanni sun bayyana cewa wata motar haya kirar Toyota Hiace, wadda ke ɗauke da fasinjoji 22 daga jihar Plateau zuwa Lagos, ta gamu da hatsarin ne bayan da direban ya rasa iko da motar, sakamakon gudun wuce ƙa’ida da kuma gajiya. Motar ta faɗa ƙarƙashin wata gada, lamarin da ya janyo asarar rayuka masu yawa a wurin. Jami’in Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) a jihar Kogi, Lawal Fagge, ya…
Read More