Babaji

5684 Posts

Abba Anas Laushi: ‘Yan bindiga sun sako gawar jigon ADC bayan biyan fansar miliyan N50

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan garkuwa da mutane sun sako gawar tsohon ɗan Majalisar Wakilai kuma jigo a jam'iyyar ADC, Abba Anas Laushi bayan iyalansa sun biya kuɗin fansa. An sace marigayin ne tare da wani ɗan siyasa mai suna Ali Tukur Gantsa daga Jihar Jigawa a yayin da suke kan hanyar tafiya Abuja domin halartar babban taron ADC. A cewar jaridar Daily Post, majiyoyi masu kusanci da iyalansa sun shaida cewa da fari 'yan bindigar sun nemi a biya su Naira miliyan 100 kana daga bisani aka cimma yarjejeniyar biyan miliyan N50, lamarin da ya yi sanadin…
Read More

Yanzu-yanzu: INEC za ta tura ‘yan hidimar ƙasa sama da miliyan 1.4 aikin zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ce za ta ɗauki sama da mutum miliyan 1.4 aikin wucin-gadi domin gudanar da zaɓukan 2027 daga cikin 'yan hidimar ƙasa na NYSC. Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar NYSC a Abuja a yau Litinin. Ya yaba wa rawar da ‘yan hidimar ƙasar ke takawa wajen gudanar da zaɓukan tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu a Nijeriya. INEC ta bayyana cewa, za a tura dubban matasa domin gudanar da zaɓukan shugaban kasa, gwamnoni da na ‘yan majalisu, tare da…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta soke jarrabawar shiga kwalejin ilimi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sanar da cire sharadin rubuta jarabawar UTME ga ɗaliban da ke neman shiga makarantun kwalejin ilimi. Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron tsara manufofin shiga jami’o’i da sauran manyan makarantu na shekarar 2026. Ya ce daga shekara mai zuwa, ɗaliban da suka samu aƙalla kredit huɗu a darussan da suka dace za su iya neman shiga shirin NCE ba tare da sun rubuta UTME ba. Sai dai ya bayyana cewa dole ne irin waɗannan ɗalibai su yi rajista da hukumar JAMB, domin tantance takardunsu kafin…
Read More

An yi walimar goyon bayan ɗan takarar gwamnan Kano na ADC, Sheikh Ibrahim Khalil

An gudanar da wani gagarumin biki da Kungiyoyin Khalil suka shirya domin nuna goyon baya ga dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Malam Ibrahim Khalil, inda jama’a da dama daga sassa daban-daban suka halarta. Taron ya samu halartar farfesoshi, malamai addinin Musulunci, wakilan Kiristoci, mata, matasa da sauran magoya baya da suka taru domin nuna goyon baya ga takarar Malam Ibrahim Khalil gabanin zaben da ke tafe. A yayin taron, masu jawabi da dama sun bayyana damuwa kan halin da jihar Kano da Najeriya baki daya ke ciki. Yawancinsu sun bayyana cewa jam’iyyar ADC ita…
Read More

Osimhen ya taimaka wa Galatasaray lashe kofin Turkiyya na huɗu a jere

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan wasan gaba na Super Eagles ta Nijeriya, Victor Osimhen, ya sake nuna bajinta bayan da ya zura ƙwallo biyu a wasan da ƙungiyarsa Galatasaray ta doke Antalyaspor da ci 4-2, lamarin da ya tabbatar wa ƙungiyar lashe kofin gasar Turkish Super Lig karo na huɗu a jere. Nasarar ta sa Galatasaray ta lashe kofin gasar Turkiyya karo na 26 a tarihinta, wanda ya ƙara tabbatar da ita a matsayin ƙungiyar da ta fi kowacce nasara a Turkiyya. Osimhen ya kasance cikin fitattun ’yan wasan ƙungiyar tun bayan komawarsa daga Napoli ta ƙasar Italiya,…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: APC ta soke ‘yan takarar ɓangaren Fubara, ta tantance 33 a zaɓen majalisa na fidda gwani

Kwamitin tantance 'yan takara na jam’iyyar APC ya hana tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Ribas na tsagi Hon. Victor Oko Jumbo da wasu 'yan takara 64 shiga zaɓen fidda gwani na majalisar dokokin jihar gabanin zaɓen 2027. Rahotanni sun nuna cewa, galibin waɗanda aka hana tsayawa takarar na daga cikin magoya bayan gwamnan jihar Siminalayi Fubara ne. Rahoton kwamitin tantancewar, wanda shugaban kwamitin Rt. Hon. Muraina Ajibola da wasu mambobi uku suka sanya wa hannu, ya bayyana cewa an cire 'yan takarar ne saboda rashin cika wasu sharuddan jam’iyya. Sai dai kwamitin ya amince da ƴan takara 33 da ake…
Read More

Barcelona ta lashe kofin Laliga na 29 bayan doke Real Madrid

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta tabbatar da lashe kofin LaLiga karo na 29 bayan doke Real Madrid da ci 2 da 0 a wasan El Clasico na ranar Lahadi. Tuni dai yaran Hansi Flick suka shiga wasan da tazarar maki 11 tsakaninsu da abokan hamayyarsu, Real Madrid da ke matsayi na biyu. Barcelona ta mamaye wasan ne tun a farkon lokaci a Camp Nou, inda Marcus Rashford ya fara zura kwallo ta bugun daga kai sai mai tsaron gida, kafin Ferran Torres ya ƙara ta biyu. Duk da ƙoƙarin da Madrid ta yi…
Read More

‘Yan bindiga 70 harin sojoji ya halaka a Neja, ba fararen hula ba, inji Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar Tsaro DHQ, ta musanta rahotannin da ke cewa an halaka fararen hula a yayin hare-haren sama da rundunar soji ta kai a Karamar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, inda ta ce, an kai su ne akan maboyar ’yan bindiga. Daraktan Yaɗa Labaran Harkokin Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. Sanarwar ta ce, rundunar soji ta kai hare haren ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ’yan bindiga sun taru a ƙauyen Lukupe a ranar 9 ga Mayun 2026. Ta ce, rundunar jiragen yaƙi marasa matuƙa ta soji sun…
Read More

An tsinci gawar ɗan jami’ar tarayya bayan zargin halaka kansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An gano wata gawar wani ɗalibin aji ɗaya na Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure mai suna Favour Olaniyi a bayan gari ta yankin ƙofar arewa ta jami'ar. Mamacin, wanda ɗan tsangayar nazarin taswira ne a jami'ar, ganin gawar tasa ya sa aka fara zargin yiwuwar ya halaka kansa ne. Haka kuma, an ga wata kwalbar maganin kashe ƙwari a gona a kusa da inda aka samu gawar. Da yake tabbatar da faruwar al'amarin jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar ta FUTA, Adegbenro Adebanjo ya koka game da rashin ɗalibin, inda ya ce…
Read More

Masu muradin tsaya wa takarar sanata sun janye wa Shekarau a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Masu muradin tsaya wa takarar sanata guda shida daga Kano ne suka janye muradunsu domin goya wa tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau baya yayin zaɓen 2027. An ɗauki wannan mataki ne yayin wani babban zama da ya ƙunshi jiga-jigan 'yan siyasar jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Da suke ganawa da manema labarai bayan zaman, 'yan takarar — Usman Bala, Sha’aban Sharada, Muhammad Zango, Ɗan Yaro Yakasai, Abbas Sani Abbas, da Shehu Isa Direba, sun ce sun janye ne don haɗin kai da zaman lafiya a jihar. A cewarsu, amince wa Shekarau wani…
Read More