Babaji

5692 Posts

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Alƙalin alƙalan Nijeriya, Ibrahim Tanko ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Alƙalin alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammad ya rasu a wani asibiti da ba a bayyana ba. A cewar wata majiya da ta gana da ShaharaReporters a safiyar yau Talata, tsohon alƙalin ya rasu ne yayin da ake masa magani a wani asibitin ƙasar waje. "Tsohon CJN Tanko Muhammad ya rasu. Ya rasu ne a safiyar nan a wani asibitin Saudiyya ", inji majiyar. Tuni ƙungiyar ɗaliban shari'ar Musulunci ta ƙasa (NAMLAS) ta miƙa saƙon ta'aziyyarta, inda ya bayyana hakan a matsayin babban rashin ga fannin shari'a da ma addini musulunci…
Read More

An samu raguwar hauhawar farashi da kaso 14.45 a Nuwamba – NBS

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta ce adadin hauhawar farashi a Nijeriya ya ragu da kaso 14.45 cikin 100 a watan Nuwamban 2025. NBS ta bayyana hakan ne a wani rahoton na 'Consumer Price Index (CPI)' da ta fitar a ranar Litinin, inda ta nuna cewa wannan shi ne karo na takwas a jere da hauhawar farashi ke raguwa a shekarar 2025. Rahoton ya nuna cewa wannan raguwa ta zarce burin Shugaba Bola Tinubu na kashi 15 cikin ɗari, abin da ke nuna alamun samun sauƙi a matsin tattalin arziƙi. A cewar hukumar, adadin…
Read More

‘Yan sanda sun kama mace mai kai wa ƴan ta’adda alburusai, ƴan bindiga da wasu a Neja

Rundunar ƴan sanda a Jihar Neja, ta sanar da kama wata mata mai suna Zuwaira Usman, mai shekaru 35, ’yar Pandogari a Karamar Hukumar Rafi, bisa zargin ƙwarewa wajen jigilar alburusai ga ’yan ta’adda a jihar. A wata sanarwa, rundunar ta ce an cafke wadda ake zargin ne a ranar 4 ga Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, bayan samun sahihan bayanan sirri. Jami’an FID–STS na rundunar ne suka aiwatar da kamen. A yayin bincike, Zuwaira ta amsa cewa ta hadu da wani mutum mai suna Lawali a Birnin Gwari, Jihar Kaduna, a watan Satumba 2025, inda suka…
Read More

Kano: Sun halaka shi bayan ya yi wa ladani yankan rago

Fusatattun matasa a Kano sun kashe wani matashi da ake zargi da kisan ladanin wani masallaci a birnin Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya. Bayan kashe matashin, sun kuma ƙona gidan iyalinsa. Al'amarin ya faru ne a unguwar Hotoro, inda bayanai suka tabbatar da cewa matashin ya yi wa ladanin, mai suna Zubairu Kasim, yankar rago ne da asubahin yau Litinin sa'ilin da yake shirin kiran sallar asubahi. Tuni ƴan'uwa da sauran al'ummar unguwar suka shiga zaman makoki bayan jana'izar ladanin. A lokacin da ya tattauna da BBC Hausa, ɗan mamacin, Isa Kasim, ya ce: “Da asuba ne mahaifina…
Read More

Ku kai ni kotu ko ku sake ni – Malami ga EFCC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana binciken da EFCC ke yi a kansa a matsayin abin da aka siyasantar, yana cewa lamarin ya samo asali ne bayan komawarsa jam'iyyar ADC. A wani saƙo daga mai taimaka masa akan harkar yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, Malami ya zargi shugaban EFCC da yin aiki bisa ɗaukar ɓangare, yana mai tunatar da jama’a cewa Mai Shari'a Ayo Salami ta taɓa fitar da bayanai masu hujjoji masu ƙarfi akansa. Saboda haka, Malami ya ce ba zai samu gaskiya da adalci ba…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu na ganawar sirri da jagororin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A halin yanzu Shugaba Bola Tinubu na tattaunawar sirri da jagororin tsaro a Aso Rock da ke Birnin Tarayya Abuja. Wannan shi ne karo na farko da shugaban ƙasar ke irin tattaunawar tun bayan rantsar da Janar Christopher Musa Gwabin a matsayin Ministan Tsaro a ranar 4 ga watan Disamba. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ɗalibai 115 na makarantar kwana ta Catholic da ke Papiri a Jihar Neja ke cigaba da kasancewa a hannun ƴan bindiga tun bayan garkuwa da su a watan Nuwamba. Idan za a tuna, a ranar 26…
Read More

Kotun Ƙoli ta jaddada ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-ɓaci da dakatar da zaɓaɓɓu

Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa shugaban ƙasa na da ikon dakatar da zaɓaɓɓen jami’in gwamnati a duk lokacin da aka ayyana dokar ta-ɓaci a wata jiha. Hukuncin ya fito ne a ranar Litinin daga kwamitin alƙalai bakwai, inda alƙalai shida suka amince da matsayar kotun, yayin da alƙali guda ɗaya ya bayar da ra’ayi na daban. Ƙarar dai ta fito ne daga gwamnatin Jihar Adamawa tare da wasu jihohi guda goma da gwamnoninsu ke ƙarƙashin jam’iyyar PDP. Sun ƙalubalanci matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Rivers a watan Maris na wannan…
Read More

Komawar Gwamna Kefas APC ta kawo ƙarshen mulkin PDP na shekara 26 a Taraba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yi rajista a APC ya kuma karɓi katin zama ɗan jam’iyya, alamar shirin sauya sheƙarsa daga PDP zuwa jam’iyar mai mulki. Shugaban APC na mazabarsa a Ƙaramar Hukumar Wukari, wanda kuma ya miƙa masa katin, shi ne ya yi wa gwamnan rajistar a ofishinsa da ke Jalingo a jiya Lahadi. Da yake jawabi bayan karɓar katin, Gwamna Kefas ya ce matakin ya yi daidai da shirin da ya kammala na sauya sheƙa zuwa APC bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyar. Ya ce, an jinkirta sauya shekar ne tun da…
Read More

MOPPAN ta taya Hamisu Iyantama murnar samun kyautar karramawa ta Bajekolin Zuma

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, ta miƙa saƙonta na taya murna ga ɗaya daga cikin mambobinta kuma daɗaɗɗen jarumin fina-finan masana'antar Kannywood, Hamisu Lamiɗo Iyantama bisa samun kyautar karramawa ta bajekolin Zuma na 2025. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta Shehu Hassan Kano, MOPPAN ta ce hakan ya nuna yadda jarumin ya kasance mai jajircewa, inda ta bada misali da nasarar da fim ɗinsa mai dogon zango na Tsintsiya da ya samu karramawa a 2018. Ta kuma ce, Iyantama ginshiƙi ne ga ci-gaban harkar fim a Nijeriya musamman…
Read More

Za a fara sayer da fetur a N739 ranar Talata, inji Ɗangote

Kamfanin mai na Ɗangote ya sanar cewa daga ranar Talata, 17 ga Disamba, 2025, za a fara sayar da man fetur (Premium Motor Spirit - PMS) a gidajan mai da ke hulɗa da kamfanin a faɗin ƙasar nan kan farashin N739 kowace lita. Wannan sauyi ne mai muhimmanci a ɓangaren man fetur na ƙasa, yayin da aka fara amfani da man da aka tace a cikin gida daga matatar Dangote, wanda zai iya rage dogaro da shigo da mai daga waje. Masana harkar suna ganin wannan ci gaba zai iya rage matsin lamba a kasuwa tare da daidaita farashin mai…
Read More