Babaji

5692 Posts

Bello Turji ya tabbatar da yin tattaunawar sulhu da gwamnatin Matawalle

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji, ya tabbatar da cewa an yi zaman sulhu tsakaninsa da gwamnatin Zamfara ta lokacin Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne Ƙaramin Ministan Tsaro. Saidai ya musanta batun karɓar Naira Miliyan 30 da kuma baburan hawa daga gare ta. Turji ya faɗi haka ne cikin wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Asabar. Gabannin wannan dai, Musa Kamarawa wanda gwamnatocin Sakkwato da Zamfara suka wakilta don sasantawa da ƴan bindiga a Arewa maso yammacin Nijeriya, shi ne ya bayyana cewa gwamnatin Matawalle ta bai wa Turji Naira…
Read More

Fasinjoji sun tsira bayan jirgi ya karci ƙasa a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar Lahadi ne wani jirgin gida mai tashin angulu na kamfanonin Flybird Airlines ya karci ƙasa a Filin jiragen sama na Malam Aminu Kano, lamarin da ya girgiza al'umma. Wani shaida ya bayyana wa manema labarai cewa fasinjoji 11 ne ke cikin jirgin a lokacin da abin ya faru ciki har da jami'an jirgin su uku, waɗanda suka taso daga Abuja. An samu tsaikon ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe yayin da jirgin ke ƙoƙarin sauka. Sannan, an samu sauƙin al'amarin ne a lokacin da aka ciro mutanen da ke cikin jirgin…
Read More

Dogarin Tinubu, Nurudeen Alowonle Yusuf ya zama birgediya janar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA), ya tabbatar da ƙarin matsayi ga jami'i Kanal Nurudeen Alowonle Yusuf zuwa Birgediya Janar. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannu Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu zuwa ga Shugaban Rundunar Sojoji, ONSA ya kuma tabbatar da cigaba da riƙe jami'in a matsayin mataimaki na musamman, wato ADC ga Shugaba Bola Tinubu. Hakan na nufin babban jami'in zai cigaba da kasancewa ADC ga Shugaba Tinubu a wani karo tun daga ranar 12 ga watan Disamba, 2025. NSA, ya…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi min tayin shiga APC, inji Sanata Natasha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ikirarin Fadar Shugaban Ƙasa ta nemi da ta sauya sheƙa zuwa cikin jam'iyyar APC. Natasha ta bayyana haka ne a wata hira ta Mic On Podcast Seun Okinbaloye a ranar Asabar. Ta ce, ba za ta bar PDP da nufin komawa APC ba domin tana jin daɗin kwanciyar hankalin da ke cikin jam'iyyar tata. Sanatar ta kuma ce, ko lokacin da yi aure an yi ta mata tayin tsayawa takara daga Jihar Delta domin mijin da ta aura ɗan can ne. Ta bayyana cewa, a baya…
Read More

MOPPAN da AFMAN sun yi ƙarin bayani kan wasiƙarsu ga jagorancin NFC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyoyin masu shirya fina-finai na MOPPAN da AFMAN sun yi ƙarin haske game da buɗaɗɗiyar saƙon da suka aike wa Hukumar kula da fina-finai ta ƙasa (NFC) sakamakon abin da suka kira da rashin fahimtar saƙonsu daga wasu mambobin masana'antar Kannywood da ɗaiɗaikun al'umma. A wata takarda da ƙungiyoyin suka fitar mai ɗauke da sanya hannun Shugabannin MOPPAN da AFMAN, wato Shehu Hassan Kano da Salisu Mohammed Officer, sun ce kwatakwata ba su da nufin kushe ko kai farmaki ga jagorancin Darakta Manaja na NFC, wato Dakta Ali Nuhu. A cewarsu, ƙorafi suka yi…
Read More

Zamfara: ‘Yan bindiga sun halaka mataimakin ciyaman da awon-gaba da masu shayarwa biyar bayan karɓar miliyan N15

Al'umma a Jihar Zamfara sun tsinci kansu cikin yanayi na alhini da jimami bayan samun labarin kisan gilla da 'yan bindiga suka yi wa Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Bukuyum, Honarabul Mu’azu Muhammad Gwashi. Rahotanni sun bayyana cewa, marigayin ya shafe tsawon watanni shida a tsare a hannun maharan kafin su halaka shi. Bayanai masu ratsa zuciya sun nuna cewa 'yan bindigar sun riga sun karɓi kuɗin fansa har Naira miliyan 15 daga hannun iyalansa da nufin za su sake shi, amma suka yi ƙememe suka kashe shi duk da biyan kudin. Wannan ɗanyen aiki ya kara jefa fargaba a zukatan…
Read More

Har yanzu ba a sako sojojin Nijeriya da aka tsare a Burkina Faso ba, inji Ministan Harkokin Waje

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce har yanzu sojojin Najeriya 11 na maƙale a ƙasar Burkina Faso bayan saukar gaggawa da wani jirgi da suke ciki ya yi a ƙasar. Rahoton ya ce, lamarin ya faru ne tun a ranar 8 ga Disamba, lokacin da jirgin ya yi saukar gaggawa a ƙasar inda ƙungiyar ƙasashen Sahel (AES) ta zargi jirgin sojin Najeriya da keta sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba. A cewar rahoton, shugaban gwamnatin soji ta Mali, Assimi Goïta, ya bayyana saukar jirgin a matsayin matakin da ya saɓa wa ƙa'idojin ƙasashen duniya Rundunar Sojin…
Read More

Kotu ta ayyana ranar shari’ar NDLEA akan Abba Kyari

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana ranar 26 ga Fabarairun 2026 domin yanke hukunci a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Sha Raya Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta shigar akan tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DCP Abba Kyari. Mai Shari'a James Omotosho ya bayyana haka ne a jiya Juma’a bayan lauyoyin NDLEA da na Kyari da ‘yan uwansa sun gabatar da takardun kare kansu da muhawarar karshe a gaban kotu. Kyari tare da ‘yan uwansa guda biyu, Mohammed Kyari da Ali Kyari, na fuskantar tuhume-tuhume guda 23 da NDLEA ta shigar na zargin su da ƙin bayyana dukiya, ɓoye mallaka,…
Read More

Ɗangote ya rage farashin fetur zuwa N699

Masana'antar Man Fetur ta Dangote ta sake rage farashin fetur a matakin gangar haya, inda ta saukar da shi daga N828 zuwa N699 ga kowace lita. Bayanan kasuwa na ainihi da Petroleumprice.ng ta wallafa a ranar Juma’a sun nuna cewa masana'antar ta sake yin babban rangwame, inda ta rage farashin da N129 kowace lita — raguwar kimanin kashi 15.58% kenan. Wani jami'in masana'antar, wanda ya gana da manema labarai a kan sharaɗin a boye sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a bainar jama’a, ya kuma tabbatar da wannan sauyi. Wata majiya da ke cikin masana’antar ta tabbatar da…
Read More

Kotun Ƙoli ta soke afuwar Tinubu akan Maryam Sanda da tabbatar mata da hukuncin kisa

Kotun Ƙoli ta rusa afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, da aka samu da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello a shekarun baya. A shekarar 2020, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya, hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar daga baya. Bisa dalilan jinƙai, Shugaba Tinubu ya rage mata hukuncin zuwa shekaru 12 kacal a gidan yari makonni kaɗan da suka gabata. Saidai a yau, 12 ga Disamba, 2025, Kotun Ƙolin ta yi hukunci da rinjayen alƙalai huɗu, inda ta dawo da hukuncin kisa na farko da aka…
Read More