Babaji

5692 Posts

DSS ta sako mutane uku da biyan su diyyar miliyan N3 bayan tsare su kan zargin hannu a garkuwa bisa kure

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta farin kaya DSS, ta sako mutane uku da aka kama su bisa kuskure kuma aka tsare su bisa zargin su da hannun a ayyukan garkuwa da mutane da fashi, bayan bincike ya nuna ba su da hannu a wani mugun aiki. Mutanen sune; Umar Ibrahim, Alhaji Bello Rabiu, da Jaja Sarki Bamo, waɗanda suka kasance a hannun hukumar tun watan Yunin 2025 a lokacin da jami'an DSS suka kama su a Filin jiragen sama na Tunde Idiagbon jim-kaɗan bayan dawowarsu daga aikin hajji. An zarge su ne da hannun a alaƙa…
Read More

Zargin rashawa: An tsare tsohon Ministan Ƙwadago, Chris Ngige a Kurkukun Kuje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Shari'a Mariam Hassan ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a tsare tsohon Ministan Ƙwadago da Ɗaukar Aiki, Chris Ngige a gidan gyaran hali na Kuje. An ruwaito cewa, an tsare Ngige ne bisa tuhumar sa da hannu a rashawa, wanda zai cigaba da zama a gidan hat zuwa ranar Litinin inda za a saurari ƙorafin neman belinsa. Musamman ana tuhumar tsohon ministan ne da laifin bada kwangilolin ayyuka da dama ba bisa ƙa'ida ba a lokacin da yake minista tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023. Haka kuma, an zarge shi da…
Read More

PDP ta tabbatar da rasuwar Mataimakin Gwamnan Bayelsa, Sanata Ewhrudjakpo

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar jam'iyyar adawa (PDP) ta tabbatar da rasuwar Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa, Lawrence Oboraw-Harievwo Ewhrudjakpo a jiya Alhamis. An shiga damuwa da fari a ranar yayin da aka samu rahotannin da ke cewa ya yanki jiki ya faɗi a ofishinsa kuma an garzaya da shi asibiti. Da take tabbatar da rasuwarsa a daren Alhamis wayewar Juma'a, PDP tsagin jagorancin su Turaki ta bakin Sakataren yaɗa labarai, Ini Emembong, ta bayyana rashin a matsayin abin da ya girgiza jama'a. Sannan, ta bayyana marigayin a matsayin mamba mai biyayya, wanda rashinsa ya haifar da babba giɓi…
Read More

DA ƊUMI-ƊUMi: Majalisar Dattawa ta tantance Omokri da Fani-Kayode a matsayin jakadu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin Majalisar Dattawa akan al'amuran ƙasashen waje ya tantance Reno Omokri a matsayin jakada bayan miƙa sunansa da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa majalisar. A yau Alhamis aka tantance Omokri, wanda tsohon mataimaki ne na musamman ga shugaban ƙasa. Idan za a iya tunawa, sanya Omokri a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za a naɗa jakadu a gwamnatin Shugaba Tinubu ya janyo cece-kuce acikin sanatoci da wasu ƴan Nijeriya bisa zargin sa da kiran Shugaba Tinubu da "dillalin ƙwaya". Amma duk da haka a yau ya je gaban majalisar bisa umarnin Tinubu na…
Read More

DA ƊUMI-ƊUMI: Rahoto ya nuna Maitaimakin Gwamnan Bayelsa ya rasu sa’o’i bayan ya yanki jiki ya faɗi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo ya rasu a yau Alhamis. Da misalin ƙarfe 1:30 na rana aka ruwaito cewa ya yanki jiki ya faɗi a ofishinsa, inda aka gaggauta garzayawa da shi zuwa Babban Asibitin Tarayya da ke Birnin Yenagoa, sannan aka tabbatar da rasuwarsa jim-kaɗan bayan haka. A ranar 5 ga watan Satumban shekarar 1965 aka haifi marigayin, kamar yadda majiyoyi suka shaida. Majiyoyi daga gidan gwamnatin jihar sun bayyana shi a matsayin mai ƙoƙarin kiyaye aikinsa bisa sadaukarwa da jajircewa. A cewar ShaharaReporters, Mataimakin gwamnan ya shiga mawuyacin hali ne…
Read More

Tirela ta murƙushe ɗaliban Jami’ar Jos takwas har lahira

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jama'a a Jami'ar Jos da ke Jihar Filato sun shiga jimami a yayin da ɗalibai guda takwas suka rasu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su da asubahin ranar Alhamis. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na dare a lokacin da ɗaliban su 11 suke kan hanyar wata tafiya, inda suka yi taho mu gama da wata tirela a daura da Bankin Unity da ke kan hanyar Zariya a Jos, Babban Birnin Jihar Filato. A cewar Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) reshen jihar ta bakin Kakakinta, Peter Longsan,…
Read More

Jami’an EFCC sun kama tsohon gwamnan Anambara, Chris Ngige a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Anambara kuma tsohon Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Dakta Chris Ngige, ya shiga hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) bisa zargin sa da ayyukan da ke da alaƙa da cin hanci da rashawa. Tsohon hadimin Ngige mai suna Fred Chukwulobe ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce jami’an EFCC sun kama tsohon ministan ne domin amsa wasu tambayoyi kan waɗansu kuɗaɗe da ake zargin an karkatar da su lokacin da yake kan muƙami. Kodayake hukumar EFCC ba ta fitar da cikakken…
Read More

Remi Tinubu ta magantu kan cece-kucen taƙaddamarta da gwamnan Osun

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Matar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta warware batun taƙaddamar da ta faru tsakanin ta da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke a taron cikar Ooni na Masarautar Ife, Adeyeye Ogunwusi shekaru 10 a kujerar sarauta. A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen watsa labarai a ranar Litinin, an ga yadda Adeleke ya je kan mimbari da nufin yin jawabin taya murna ga matar shugaban ƙasar bisa karrama ta da sarautar 'Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua'. A madadin haka ne sai gwamnan ya soma abin da ya saba na ƙoƙarin nishaɗantar da jama'a gabanin jawabinsa…
Read More

EFCC ta ci gaba da riƙe Malami kan binciken alaƙanta shi da asusun bankuna 46

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN), ya shafe kwana na biyu a tsare a hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) bayan kasa cika sharuɗɗan belinsa. Majiyoyi sun ce ana bincikensa ne akan zarge-zargen laifuka 18, ciki har da hada-hadar kuɗi da saɓa ka'idar aikin ofis, da kuma zargin taimaka wa ayyukan ta’addanci ta hanyar kuɗi. Haka kuma, ana tuhumar sa kan yadda aka yi asarar Dala miliyan 346.2 na kuɗin Abacha da aka dawo da su daga Switzerland da Jersey, da kuma rabon kuɗaɗen shirin…
Read More

Sojoji sun halaka na hannun daman Turji, Kachalla Kallamu da wasu 14 a Sakkwato

Dakarun Rundunar 8 ta Division ta Nijeriya a Sakkwato, sun samu gagarumar nasarar kawar da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Kachalla Kallamu, a yankin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni. An kashe Kallamu ne a wani samame na musamman da sojoji suka gudanar tare da haɗin-gwiwar ƴan sa-kai a yankin Kurawa da safiyar ranar Litinin. Kallamu, wanda babban na hannun daman shugaban ƴan bindiga Bello Turji ne, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka addabi al’ummar Sabon Birni da hare-hare, garkuwa da mutane da kuma tada tarzoma a yankin. Rahotonni sun bayyana cewa an kashe shi ne tare da ɗaya daga cikin manyan…
Read More