Babaji

5692 Posts

NFC ta karrama Hamisu Iyantama a bajekolin Zuma International Film Festival

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen jarumin fina-finan masana'antar Kannywood kuma daɗaɗɗen furodusa, Hamisu Lamiɗo Iyantama, ya samu lambar girmamawa a taron baje kolin fina-finai na ƙasa-da-ƙasa, wato Zuma International Film Festival, wanda Hukumar Kula da Fina-finai ta ƙasa (NFC) ta shirya. Taron, wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja a yau Laraba, ya jinjina wa gudumawar da Iyantama ya bayar a harkar fim musamman duba da yadda ya shafe tsawon shekaru da dama aciki, lamarin da ya taimaka wa ci-gaban fannin da ma masana'antar fim ta Arewa a keɓance. Da yake jawabi a taron, Iyantama ya miƙa godiyarsa…
Read More

Shugaban Hukumar Raya Kogunan Haɗejia ya jinjina wa Tinubu kan ceto ɗaliban da aka yi garkuwa da su

Shugaban Hukumar Raya Kogunan Haɗejia da Jama'are, Alhaji Rabi'u Sulaiman Bichi, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan ceto ƴan makarantun nan da ƴan Bindiga suka sace a Jihohin Kebbi da Neja, inda shi shugaban ne kansa ya jagoranci ceto waɗannan ɗalibai cikin aminci. A sanarwar daga ofishin hukumar, ta ce Alhaji Sulaiman Bichi ya kuma jinjina wa salon jagorancin Shugaba Tinubu saboda nuna damuwa kan abinda ya shafi tsaro da jin daɗi da walwalar al'ummarsa. "Yana da matuƙar muhimmanci mu jinjina wa Shugaban Kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu saboda daukan matakan gaggawa dan ceto wadannan ya'ya namu. Yayin da…
Read More

Gwamnan Osun, Adeleke ya koma AP bayan fita a PDP

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana komawarsa Jam'iyyar "Accord Party', inda ya ce a cikinta ne zai yi takarar neman wa'adin mulkinsa na biyu a zaɓen da za a yi a 2026. Adeleke ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudana a fadar gidan gwamnatin jihar, inda ya yi maraba da jagororin jam'iyyar na jiha da na ƙasa. "Tun a ranar 6 ga watan Nuwamba na yanke shawarar komawa Jam'iyyar Accord domin in yi takarar tazarce bayan tattaunawa da na yi da masu ruwa da tsaki da mazauna jiharmu ta Osun", inji shi. Ya bayyana cewa, ya…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnan Ribas ya koma APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas ya sanar da komawarsa zuwa jam'iyyar APC. Fubara ya bayyana haka ne yayin wani zama na masu ruwa tsaki a gidan Gwamnatin jihar. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan ya fice daga babbar jam'iyyar adawa PDP. Idan ba a manta ba a jiya Litinin ne gwamnan ya yi wata ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Read More

Kakakin KAFIGAN, Al-Amin Ciroma ya yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Daraktan yaɗa labarai kuma mamban kwamitin amintattu (BOT) na ƙungiyar masu shirya fina-finai ta KAFIGAN, Al-Amin Ciroma ya yi murabus daga muƙaminsa. A wata takarda da ya aike wa Darakta Janar na ƙungiyar, Ciroma ya ce ɗauki matakin ne duk da cewa yana da muhimmiyar rawa da yake takawa wajen tafiyar da harkokin ƙungiyar. Ya ce, lokaci ya yi da ya dace ya ajiye aikin sakamakon wasu dalilai na raɗin kansa. Ya kuma yi godiya ga hukumar gudanarwar ƙungiyar bisa damar da ta ba shi na gagarumim matsayin wanda ya yi amfani da ƙwarewa…
Read More

Ribaɗu ya miƙa ɗalibai 100 da aka ceto ga gwamnatin Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, ya miƙa ɗalibai 100 na makarantar St. Mary Catholic School da ke Papirin Ƙaramar hukumar Agwara a jihar Neja, ga gwamnatin jihar bayan ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane. An gudanar da mika su a Minna a ranar Litinin, inda Wing Cdr. Abdullahi Idi Hong ya wakilci NSA wajen gabatar da su ga gwamnatin jihar. Hong ya ce ceton ya biyo bayan makonni na tsauraran hare-haren hadin gwiwa tsakanin Ofishin NSA, Hukumar DSS, Rundunar Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro.…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: ECOWAS ta ayyana dokar ta-ɓaci a Yammacin Afirka

Ƙungiyar Ci-gaban Tattalin Arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS), ta ayyana dokar ta-baci a faɗin yankin yammacin Afirka sakamakon ƙalubalen tsaro da juyin mulki da ke ƙaruwa a wasu ƙasashen mambobinta. Wannan mataki na zuwa ne a matsayin martani ga hauhawar barazanar tsaro, musamman juyin mulki a wasu ƙasashe, da kuma yunƙurin dawo da tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiya a yankin. A cewar shugabannin ECOWAS, wannan dokar ta-baci za ta bai wa ƙungiyar damar ɗaukar matakan gaggawa don kare dimokuraɗiyya, samar da zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama'a. Za a ci gaba da bibiyar wannan mataki don ganin…
Read More

Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu ta tura dakaru Jamhuriyar Benin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta tura jami'an sojoji zuwa Jamhuriyar Benin domin taimaka wa ƙoƙarin ƙasar na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda da aka yi yunƙurin kifar da gwamnatin dimukraɗiyyar ƙasar. Da fari, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya sanar da batun yayin zamansu na yau Talata, wanda daga bisani suka cimma matsayar amince wa buƙatar bayan nazari a kai. Lamarin da ya nuna goyon bayansu ga yunƙurin tallafin na lamuran tsaro a shiyyar. Akpabio ya bayyana matakin a…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da tura dakarun Nijeriya zuwa Jamhuriyar Benin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa wasiƙar neman ta amince wa buƙatar tura dakarun tsaron Nijeriya zuwa Jamhuriyar Benin. Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya karanta takardar yayin zaman majalisar na yau Talata. Tinubu ya ce, matakin abu ne mai muhimmanci bisa la'akari da yunƙurin juyin mulki da aka yi a ƙasar kwanan nan. Ya bayyana cewa, hakan tallafi ne ga ƙasar sakamakon neman agaji da Shugaba Patrice Talon ya yi jim-kaɗan bayan yunƙurin juyin mulkin ga shugaban Nijeriyar. Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa, gwamnatin Benin tana fuskantar barazanar karɓe mulkinta na…
Read More

Lalacewar na’ura ce ta haifar da saukar jirgin sojojin Nijeriya a Burkina Faso ba shiri, inji NAF

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin aka shiga fargaba a shiyyar ƙasashen Sahel (AES) yayin da Mali, Nijar da Burkina Faso suka yi alla-wadai ta saukar gaggawa da jirgin C-130 na rundunar sojin Nijeriya ya yi a Burkina Faso, lamarin da ƙasar ta kira da saɓa wa dokokin sararin samaniyarta. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya auku ne a lokacin da jirgin ya yi jigilar dakarun Nijeriya 11 yayin da suak nufi ƙasar Portugal, inda babu shiri suka sauka a Bobo-Dioulasso, abinda hukumomin Nijeriya suka ce ya faru ne sakamakon gazawar na'ura ana tsaka da tafiya. A…
Read More