Babaji

5692 Posts

Zargin badaƙala: EFCC ta rufe gidan Timipre Sylva na Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Julius Bokoru, wanda shi ne Mai taimaka wa tsohon Ƙaramin Ministan Albarkatun Fetur kuma tsohon gwamnan Bayelsa, Cif Timipre Sylva, akan harkokin yaɗa labarai, ya yi alla-wadai da rufe gidan maigidansa da ke Maitama a Abuja da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati, EFCC ta yi a jiya Litinin. Bokoru ya nuna rashin amincewa da matakin na EFCC wanda ya kira da "taka masa ƴancin mutunci" a matsayin na ɗaya daga cikin jagororin al'umma. Tun a watan Nuwamba EFCC ta ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin sa da…
Read More

Hukumomin Burkina Faso sun tsare sojojin Nijeriya 11 bayan taka dokar sararin samaniya

Gwamnatin soji ta ƙasar Burkina Faso ta bayyana cewa ta tsare jami’an sojin Nijeriya guda 11 tare da ƙwace wani jirgin rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) bayan jirgin ya yi saukar gaggawa a cikin kasar. Al'amarin ya faru ne bayan jirgin ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da samun izinin hukumomin ƙasar ba a jiya Litinin. Rahotanni sun bayyana cewa jirgin, wanda ke ɗauke da kayan aiki, an tilasta masa yin saukar gaggawa bayan tasowarsa daga Nijeriya. Haka kuma hukumomin Burkina Faso sun ce wannan karya dokar sararin samaniya ce, wadda ta tilasta su ɗaukar matakin tsaro akan…
Read More

MOPPAN ta koka wa NFC bisa nuna mata wariya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar masu Shirya fina-finai ta ƙasa (MOPPAN) da haɗin-gwiwar Ƙungiyar ƴan fim ta ƙasa (AFMAN), sun nuna damuwa kan yadda ake ƙoƙarin mayar da su saniyar ware a harkokin Hukumar Kula da Fina-finai ta ƙasa NFC. A wata wasiƙa zuwa ga Darakta Manaja na NFC reshen Jihar Filato, da Shugaban MOPPAN da AFMAN (Shehu Hassan Kano da Salisu Mohammed Officer) suka fitar, ƙungiyoyin sun bayyana damuwarsu bisa yadda ake nuna musu wariya da sakaci da al'amuransu waɗanda ke cigaba da yawaita daga ɓangaren wakilan NFC na Arewa. Sun ce, gabanin daraktan ya kama aiki,…
Read More

Zamfara: Gwamna Lawal ya ƙaddamar da shirin ciyar da jihar gaba na shekara 10

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya bayyana Shirin Ci-gaban jihar a matsayin dogon tsari na shekaru goma da aka gina bisa shaidu da bincike, wanda ke bayyana burin jama’a da muradun haɗin kai wajen sauya jihar zuwa mataki na ci-gaba. Gwamnan ya ƙaddamar da shirin ne a ɗakin Sakatariyar JB Yakubu da ke Gusau a ranar Juma’a. Wata sanarwa daga Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki kamfanin KPMG Advisory a matsayin babban mai kula da tsara shirin. Sanarwar ta kuma da ce KPMG yayi aiki kafaɗa da kafaɗa da mambobin Majalisar Zartarwa ta…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya gana da gwamnonin APC shida a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Litinin ne Shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da gwamnoni guda shida na jam'iyyar APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Gwamnonin sun isa fadar ne da misalin ƙarfe 4 na yamma domin halartar zaman, wanda ya ɗauki tsawon ƙasa da sa'a guda ana yin sa. Saidai babu wani ƙarin bayani akan musabbabin abinda aka tattauna a yayin haka duba da cewa ba a sanar da maƙasudin zaman ba. Blueprint.ng ta ruwaito cewa waɗanda suka halarci zaman sune gwamnonin jihohin Jigawa, Umar Namadi; Edo, Monday Okpebholo; Ekiti, Biodun Oyebanji;…
Read More

Sakkwato: Jami’an Sabon Birni sun musanta kashe-kashen masallaci yayin da sojoji suka daƙile hari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Birnin Jihar Sakkwato, Alhaji Ayuba Hashimu, ya ƙaryata rahoton cewa an kai farmaki a wani masallaci wanda aka yi zargin ya halaka limami da wasu masallata a yankin. Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ce wani gidan jarida ne ya ruwaito cewa ƴan bindiga sun farmaki al'umma a wani masallaci da ke cikin garin Sabon Birni, inda suka halaka limami da wasu mamu tare da yin awon-gaba da wasu. A wata hira da manema labarai, Shugaban ƙaramar hukumar ya musanta batun kai harin, inda ya ce kwatakwata hakan bai faru ba.…
Read More

Shugaba Macron ya yi alƙawarin tallafa wa Nijeriya kan harkar tsaro

Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa za ta taimaka wa Nijeriya shawo kan matsalar tsaro a arewacin ƙasar da ke fuskantar taɓarɓarewa. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X, Macron ya ce ya nemi sauran ƙasashe ƙawayensu da su "ƙara ƙaimi a hulɗarsu" da Nijeriya. "Na yi magana da Shugaban Najeriya Bola Tinubu, na shaida masa goyon bayan Faransa game da matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya," a cewar Macron. "Kamar yadda ya [Tinubu] buƙata, za mu ƙarfafa hulɗarmu da hukumomi da kuma taimaka wa al'ummomin da lamarin ya shafa. Bai kamata mu zama…
Read More

Yadda Tinubu ya umarci a gaggauta ceto dimukraɗiyyar Jamhuriyar Benin

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana irin rawar da Shugaba Bola Tinubu ya taka wajen daƙile yunƙurin juyin mulkin da aka yi ranar Lahadi a Jamhuriyar Benin da ke maƙotaka da Nijeriya. Wata sanarwa daga Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, fadar ta ce shugaba Tinubu ya tura sojojin sama da na ƙasa zuwa Benin bisa buƙatar da gwamnatin ƙasar ta gabatar. Da safiyar lahadi ne tawagar wasu sojoji ƙarƙashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ta sanar da kifar da gwamnatin shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ta ƙasar. Saidai da rana, ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin Alassane Seidou ya bayyana…
Read More

‘Ka daina ɓata lokaci’: Remi Tinubu ta yi yunƙurin dakatar da Gwamna Adeleke yayin jawabi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu aukuwar wani al'amari mai kama da wasan kwaikwayo yayin taron bikin Ooni na Masarautar Ife karo na 10 a Jihar Osun yayin da matar Shugaban Ƙasa Sanata Remi Tinubu ta ari numfashin Gwamna Ademola Adeleke a lokacin da yake tsaka da jawabi. Taron, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, ya yi daidai da cikar Oba Adeyeye Ogunwusi shekaru 10 akan kujerar sarautar. A yayin haka ne kuma Sarkin ya ba wa matar shugaban ƙasar sarautar 'Yeye Asiwaju Oodua' na masarautar. Haka kuma taron ya samu halartar manyan baƙi daga sassa Nijeriya ciki…
Read More

2026: JAMB ta fitar da sabon tsarin rajista ga masu neman rubuta jarrabawar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Haɗaka ta kula da Lamuran Bada Gurbin Karatu a Manyan Makarantu JAMB, ta fitar da cikakken bayanai game da tsarin rajistar jarrabawar UTME ta shekarar 2026. JAMB ta yi sanarwar ne ta shafinta na kafar X a jiya Lahadi inda ta ce an samu sauye-sauye akan tsarin da aka saba bi a baya domin tabbatar da kammala shiri cikin tsari ga ɗaliban. Ta ce, wajibi ne ɗalibai su tabbatar bayanansu na lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN), Imel da takardun kammala karatunsu na baya suna nan daidai gabanin fara yin rajistar. Don haka ta…
Read More